← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 96

Sashe 82

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kin kulashi tayi duk da taji shi,taci gaba da takunta,
Sai dai ko step uku bata karaba cikin rashin sani ta taka doguwar rigar dake jikinta ai kuwa nan take tayi baya gaba ɗaya tana shirin faɗuwa,duk yanda taso ta kama kasa ta tsaya abin ya gagara,ta tabbatar da idan har bisa tsautsayi keyarta ta kai kasa to babu lallai na zata kara tashi a wannan rayuwar,domin ta san dinkin dake kanta ya gama kwancewa bama shi kadai ba kan gaba ɗaya ya gama tashi aiki,saboda step din nada yawa,

Ta dai jita ta faɗa jikin abu mai laushi idanunta a lumshe,sai dai ko kusa bata gwada bude ido ba,dan ta sadakar mala'ika yayi sama da ita ko,
Ai kuma jin anyi saman da ita ne yasa ta kara sake jiki gabadaya kamar mawa sumammiya,koda yake zamu iya kiranta da haka tunda da gasken suman wucen gadi tayi,

A hankali yake tafiya da ita a hannun shi yana kuma kallon yanda take sauke numfashin a hankali wanda hakan ke nuna masa da bugun zuciyarta yayi ƙasa,

A maimakon shiga da ita dakin ta,sai tura kofar dakin shi da ƙafa yayi ya shiga,ya maida,kan gado ya shimfidar da ita a hankali kamar wata karamar yarinya,ya dauki filo ya daura kanta,

Zame doguwar rigar jallabiyar jikinta yayi,wanda yayi sanadiyar bai yanar yar karamar rigar baccin dake jikinta iya cinya,
Kallo daya ya mata ya dauke idanun shi a jikinta ya maida a fuskarta,
Shafa fuskar yake a hankali tare da kiran sunan ta"Bebin bude idon ki"

"Um Umm"

Dukawa yayi saitin kunnenta "buɗe ido ki gani"

"Na mutu ne?

Bai bata amsa ba sai tafin ƙafar ta daya kama ya shiga murzawa da dan ƙarfi yanda zafin ke ratsata a hankali hakan ya tilasta mata buɗe idanunta,kallon shi take na ɗan wani lokaci kafin kuma ta kalli dakin sai zame ƙafarta tayi tana sauka,ba tare data ɗauki rigar ta ba tace" Thank"ta yi fatar ta,

Girgiza kai yayi yana mikewa canja kaya yayi ya fita,

Ita kuma tana shiga daki fadawa tayi kan gado tana sauke numfashi daga nan bacci ne ya dauke ta,
Ba ita ta tashi ba sai da Ammi ta aiko daya daga cikin masu aiki a tayar da ita ta shirya,
Da kyar ta buɗe ido ganin ƙarfe tara da rabi ne yasa babu shiri ta tashi zaune,sai kuma ta mike tana nufar banɗaki da gudu,
Cikin kankanin lokaci ta yi wanka ta shirya cikin doguwar riga na jallabiya,sai rigar sanyi mai nauyi da Ammi ta aika mata dashi,
Koda ta sauko duk suna falo harda Grandma,

Kallon Agogo Ammi tayi"yi sauri ki karya,kin san nan basu daukar African time "

"To Ammi" Cikin sauri ta dauki ruwan shayin da aka haɗa mata wanda ya dan sha iska,tana kurba tana tura soyayyen ƙwai,

"Ammi muje na gama" Ta faɗa ta karɓar keken da Grandma ke zaune tana turata a hankali,

Su suka taimaka mata ta shiga mota sannan Driba ya ja su,

A bakin wani tangamemen Kotu wanda ya amsa sunan sa suka parkar a wurin parking,

Koda suka shiga a wani babban ofishi suka zauna,ko minti goma ba su yi ba aka ce su shigo za'a fara kowa ya halarta,

A wasu manyan kujeru Alkalaine dattawa guda biyar,
Sai kuma wadanda bata sansu ba,amma abinda ya bata mamaki shine ganin Pa,Nadiya,da sauran yannin ta,sai Abbu,Shamsuddeen,Dady,Abba,Nurudeen,kai ikon Allah,
Dan can ba kaman nan bame da a cika koto,wannan shari'ar irin na Family ne kawai,

Kallon Ammi tayi"kalli su Abbu yaushe suka zo?

"Ki natsu" Ta faɗa ba tare data kalli in da suke ba,

Kallon mamaki take mata,sai dai bata ce komai ba,

Wani ne ya tashi da takarda a hannu ya fara magana kamar haka"wannan shari'a ce da aka fara shekara goma sha ɗaya da suka wuce,amma saboda rashin hujja da kuma rashin lafiyar ɗayan daga cikin hujjoji yasa yasa aka daga shari'ar har ta samu sauƙi,to yanzun gashi Allah yayi ta tashi cikin aminci,kamar yanda aka fara to yanzun za'a daura daga in da aka tsaya,sai kuma wasu daga cikin nan waɗanda aka gaiyato su a bisa yardar gwamnatin garin su,tare da wakilan gwamnatin,suma sun iso ne a safiyar yau"

Daya daga cikin Alkalan ne yace "Dr Aisha ko zaki iya fitowa ki kara fada mana abinda ya faru shekaru goma sha ɗaya baya"

Ammi ce ta tashi ta tura Grandma zuwa stage,ita sai dube dube take ko zata hango Suraj,sai dai sam ta kasa ganin shi,
Dole ta mai da hankali kan Grandma da zata fara magana.

Da farko Ahalin mu sun kasance daya daga cikin sanannun mutane a garin Mardesh,saboda Arzikin da Allah ya basu,sai dai kuma Allah bai yi su da haihuwa ba,shi yasa idan har aka samu haihuwa a zuri'ar akanyi sati ana shagali,
Ahalinmu basu yarda da auren bare,sai dai auren haɗi,
Mahaifina ya auri mahaifiyata mai suna Mariya,a lokacin baya auren haɗi ne kuma ba sonta yake yi ba,sai da suka shekara goma da aure sannan Allah ya basu haihuwa na,ina da shekaru bawai a duniya,wani aiki na buɗe sabon Company su ya kaishi South Africa,anan ya haɗu da wata yarinya mai suna Linda,sunyi soyayya sosai da ita,ba tare da aure ba ƙaddara ciki ya shiga,sai da ta haihu sannan ne dangi suka samu labari,a lokacin an yi tsiya sosai domin cewa sukayi zasu kore shi acikin dangin mu,Mariya da Hassan,dan uwan mahaifina su suka tsaya mashi,sannan dangi suka hakura,da Sharadin zai musuluntar da ita ya aure ta,kasancewar yana sonta shi yasa ya amince,mahaifiyata tayi zaman hakura dasu sosai saboda mahaifina kiri kiri yake nuna yafi son Pa a kaina,sai dai mahaifiyata bata nuna komai ba,a lokacin dana cika shekara goma ta tara mahaifiyata ta rasu,mutuwar da ta girgiza mahaifina domin zazzaɓin sati ɗaya tayi,sai dai ko sannu bai ce mata ba,saboda a tunanin shi zata tashi,ya manta cewa mutuwa bata sanarwa,yayi daya sanin rashin kyautata mata,ko sau daya bai taba furta mata kalmar so ba,
Ba na son zama tare da Linda,dan haka na koma digan dan uwan Baba na Hassan na zauna tare da matarshi da kuma yar shi mai shekaru goma,
Ana cikin haka mahaifina ya fitar min da miji mai suna Usman,babu gardama na amince kasancewar sa mutum mai nagarta kuma ya san abinda yake yi,
Inada shakara biyu a gidan miji na kammala master's dina na fara aiki,
Bayan shekaru shida da aure na mahaifina ya kamu da ciyo mai tsanani a lokacin Pa yana da kusan shekara goma sha takwas a duniya,
Mahaifina yayi kira na nida mijina,
Dana same shi ne ya nuna min wani akwati ƙarami dake gefen shi yace na ɗauka na buɗe,ina buɗe sai ganin dutsen Diamond na yi tare da wani takarda,a kalla ko a wanan lokacin kuɗin Diamond din ya haura biliyoyin kuɗi,
Tambayar shi nayi Baba wannan na menene,
Sai cewa yayi tunda ya auri mahaifiyata bai taba mata komai ba,nima haka,wannan Diamond din dukiyar daya mallaka tare da gadon da mahaifiyata ta barmin ne ya haɗa ya siya wannan dashi,dan haka ya mallaka min shi har duniya ta nade,
Nati kuka sosai na kuma gode masa,a lokacin Linda dake labe da ɗanta ta fito ta nuna Babana akan wannan abinda yayi cin amana ne,to su mai ya bar masu,girgiza kai kawai yayi ya ce ya bar mata Company shi na garinsu,sai kuma wannan gidan da yake ciki ta je ta rayu ita da ɗanta,sai kuma kuɗaɗen da bansan adadin su ba daya basu,

Ni dai mun wuce tare da mijin na,ba'a dau kwana biyu ba Allah ya mai rasuwa,
Bayan kwana biyu da rasuwar shi ta tattara ita ɗanta suka koma Sauth Africa,
Ko wata hudu ba ayi da rasuwar mahaifina ba Allah ya bani ciki,nayi farin ciki sosai na kuma yi kukan murna,
Yan wata tara na haifi dana mai suna Abdul basir,
Yaro ne wanda ya taso da natsuwa da hankali,ga tausayi,
Ta gefe ɗaya kuma yarinyar Kanin Baba na Hassan tayi auren Shamsiya,

Abdul basir nada shekaru biyar Shamsiya ta haihu,in da a wurin haihuwa Allah ya mata rasuwa,mutuwarta ta girgiza dangi sosai,nayi kuka kamar me,domin mun shaku sosai da Shansiya,hakan yasa na roƙi mijinta wanda yake matsayin Ɗan'uwa a gari saboda auren dangi ne ita,akan su ba ni yar ina son zan kula da ita,babu musu aka gabi,saboda dukkan mu daya ne,sai dai da Sharadin ba zan taba shayar da ita Nono ba saboda auratayya na iya shiga tsakani,cikin sauri na Amince,bayan kwanaki biyar yarinya taci suna Hafsan (Ammi kenan) na riƙe Hafsat a matsayin ƴar dana haifa,kusan tare da Abdul basit muka yi rainon ta,dan barci kadai ke raba su har girma,dan saboda ita yaki yarda yaje wani gari yin karatu,

Shi kuma bangaren kanina lokaci lokaci na kan je na duba shi,shima ya zama babban mutum har yayi aure,

Lokaci ne yayi tafiya mai matukar nisa wanda a hankali har Allah ya nuna min girmar yarana Hafsat da Abdul,wanda tana da shakara goma sha takwas ta nuna babu wanda take so sama da ya'yanta,idan bashi ba bata jin zata aure wani,mukan dama abinda muke so kenan,ai kuwa ba'a dauki lokaci ba aka ɗaura masu aure,sai dai suna zaune ne tare da ni a nan garin Mardesh,

A lokacin da muka fara fuskantar barazana ta farko shine a lokacin da Hafsat ta haife Suraj,yana da wata biyu,aka kara turo min wasika akan na bayar da wannan Diamond din dana mallaka a wurin Baba na ko a kashe iyalaina,
Da fari na shashantar da maganar,amma da abun ya kai har cikin gidan da nake ake shiga a ajiye mun wasika duk yawan Jami'an tsaro yasa na fara tsorata,na faɗa ma mijina,shine ya bada shawara akan mu dauke takardar Diamond ɗin wanda idan har mutum yayi nasarar satan Diamond din in babu wannan takardar na shaidar mallaka babu ta yanda za'ayi ya iya fitar dashi ko da tsayin shakara nawa ne,haka kuma ko fasashi akayi to tabbas wurin siyarwa da kwaji sai an gane na Ahalin mu ne,

Dan haka muka tattara muka dawo garin London da zama har da su Hafsat,shi kuma takardar muka bada ajiyar shi ba tare da sanin kowa ba haɗe da Diamond ɗin,
Chapter 82 · 0% Book details