← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 96

Sashe 2

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jacket din saman jikinta ta cire ba tare da tunanin komai ba ta daga rigar dake kasan jaketa din wanda yake fari ne,
Kai jama'a tsarki ya tabbata ga Allah wanda yake makagin dukkakn hilittu,
Idan ka kalli tsarin halitar kirjinta wanda yake a cike a cikin Pink din Bireziya ka gangaro zuwa shafaffen cikinta wanda ya haɗe da baya,idanunka suka sauka a saman ɗan ƙaramin ramin Cibiyar ta wanda ya shige canciki, yayin da aka makala wani ɗan ƙarfe mai matukar jan hankali a wurin wanda na tabbatar na zinari ne saboda yanda wurin ke daukar ido,maranta a shafe yake sosai babu alamun tudu ko wani abu,
Takalmin ƙafarta ta cire sannan ta cire dogon wandon dake jikinta,ya rage daga ita sai pant,jama'a ba zan iya cewa komai ba sai dai ku kwatanta yanda tsarin halittar kugun Biba yake,sai dai abun da zan iya faɗa shine ba tada mugun Hips madaidaicine mai matukar jan hankali,kamar yanda fatar jikinta yake sumul yanda kasan na tarwada tsabar tsamtsi,babu wani tamurewa ko tattarewa a tare da fatan kamar yanda babu nankarwa ko rakainuwa ne oho,babu shi dai a jikinta,
Juyowa tayi ta kalli Ummita wacce ta taso ganin yanda take tube kaya,
Jawo ledan tayi ta ciro wasu kaya ta mika mata"kiyi sauri ki saka mubar nan wurin domin nan da minti ishirin jirginmu zai tashi zuwa NIGERIA"

Amsar kayan tayi ta warware tana kallon ta"Biba ina kika samu kaya"

Ba tare data juyo ba tace"ba nida lokacin amsa maki wannan tambayar kawai kiyi abinda nace in kina buƙatar kasancewa a raye"

Bakinta taja ta kulle yayin data hadiye dukkan tambayar da take dashi,idan sunje gida ta jero mata su.

Dukansu riga da siket ne na atamfa sai jallabiya irin wacce ake ma lakabi bi After dressing,shi suka saka,sai kuma Sun glass na ido babba wanda ya kusan cinye rabin fuskar tasu,
Kayansu ba iri ɗaya bane kowa da irin nashi,

Kayan da suka cire ta kwashe ta maida cikin leda,harta daure ledan sai kuma ta sance da sauri ta ciro wandon data cire,hannun ta saka a aljihum wandon ta ciro wani karamin leda,ta buɗe,sai ga wani ɗan ƙaramin Memory Card,
Maida wandon tayi cikin ledar sannan ta wurga ledan cikin wannan katon rafin,
Motar suka shiga yanzun ma itace a mazaunin direba,kafin ta tayar da motar ne ta mika hannunta ta dauko wani karamin jakkanta wanda yake ɗan madaidaici ne irin na ƴan matan yanzun,buɗewa tayi ta duba passport dinsu,sannan ta ciro wata Android phone ta saka wannan Memory a ciki,ta maida cikin jakkan,
Sai da tayi Ribas sannan ta ja motar da karfi suka bar wurin,wanda tafiyar minti goma ya kai su Airport,
Lafiya aka gama caje su kafin a basu damar shiga cikin jirgi,wanda gaba ɗayan su a lokacin da suka ji jirgin ya lula sararin samaniya dasu suka sauke ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya,yayin da ita kuma take ƙara damke jakkan dake rike a hannun ta,tana mai fatan saukarsu lafiya..
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*03*

Misalin karfe biyar na yamma jirgin su ya sauka a garin Abuja cikin aminci,

Suna fitowa daga cikin Airport din tsayawa tayi tana ƙare ma jeren motocin dake wurin kallo,kafin ta sauke idanun ta a kan wata lafiyayyen Mota mai numfashi wanda wani matashi ke jingine a jiki,
Kauda kai tayi tana tare taxi da hannun wanda nan take ya tsaya,da sauri Ummita ta buɗe ɗayan gefen ta shiga,dan ba a karamin gajiye take ba,
Harta dafa marfin mota zata shiga taji an riƙe marfin,dagowa tayi dan ta ga wani isasshe ne,
Kallon sama da ƙasa take masa wato dai wannan saurayin ne na jikin motar nan,
Dan murmushi ya sakarmata "Barka da dawowa Biba"

Ƙoƙarin shiga mota take yi ba tare da tace masa komai ba,

Da sauri ya kara cewa"Sorry ban lura da ku bane,sannan Oga yace na dauko ki"

Sai da ta zauna da kyau sannan ta jiyo ta kalleshi"bana bukatar zuwa inda yake yanzun domin a gajiye nake"ta faɗa tana kulle marfin matar,
Kasancewar glass a buɗe yake yasa yace"to ki bani sakon na kai masa,domin a matse suke,yanzun haka sun haɗu ke suke jira"

Wani banzan kallo ta watsa mashi wanda sai da gabbanshi su kayi sanyi"ko su da suka aikoka basu isa su sa na yi abinda banyi niya ba balle kai ɗan aiken su"kallon direban tayi "muje mana" Ta fada tana jan tsaki,

Cikin sauri yace"ga katin Hotel din da zaki sauka,an riga an shirya maki ɗaki,
Amma tuni sunyi gaba tunkafin ma ya karasa faɗin abinda ke bakin shi,

Shafa kanshi yayi yana tunanin shi ta ina ma zai fara yaje yace ma Minista tace ko shi bai isa ya karɓi abinda ke hannun ta ba,kai lallai wani abu sai Biba,
Motar shi ya shiga ya bar wurin.

A wani Hotel mai suna Majestic suka sauka,wanda yake ba wani babba bane anan suka kama ɗaki daya ita da Ummita,

Suna shiga dakin ta kalle ta "Ummita kiya mana order abinci dan yunwa nake ji" Ta fada tana wurgi da jakkanta kan gado"yauwa ki hado da kayan da zamu saka"

"Ba yau zamu koma gida ba"

Hanyar wata kofa tabi wanda take da tabbacin bayi yi,"sai zuwa gobe"

Ganin ta shige bayin ne yasa ta jawo jakkan data ajiye ta bude, wasu wayoyi ne a ciki kusan guda uku,daya daga ciki ta ɗauka ta buɗe bayan marfin,sai ga sim card a faɗo,ɗauka tayi ta saka acikin wayar sannan ta kunna,
Dama kuma su nada Company da suke ordan abinci,nan ta danna masu kira,bugu biyu kuwa aka dauka nan ta faɗi kalan abincin da suke buƙata,sannan ta masu transfer na kuɗi harda kalan kayan sawa da suke bukata,

Ta dauki lokaci mai ɗan tsayi kafin ta fito wanka daure da ɗan ƙaramin tawol wanda da kyar ya gama rufe mata mazaune,idan kuma har za tayi kyakkyawar dukawa kuwa to tsaf za'a iya ganin jikin ta,

Faɗawa tayi kan gado tana sauke ajiyar zuciya ta jawo filo ta rungume,
Ko kafin Ummita ta fito wanka tuni tayi barci,

Koda ta fito kallon ta tayi ta girgiza kai,ita dai tamkar wacce ba tada wata damuwa a zuciyar sai dai in bata kwanta da sunan barci ba,nan take kuwa barci zai dauke ta,

Ganin haske a wayar ta ne yasa ta dauka ta kara a kunni,cewa kawai tayi"ok"sannan ta kashe wayar,
Bata damu da saka wani abu da zai rufe mata jiki ba ta fita a haka daga ita sai karamin tawol ita ma irin na Uwar dakin ta,sai dai ita nata ya danfi sauka duk da bai gama kaiwa guiwa ba,a haka ta buɗe ƙofar dakin da suke ta fita,
Kasancewar Hotel din mai dan girma ne kuma ba laifi a kwai mutane kowa na harkan gaban shi,amma duk da haka duk inda ta gifta sai ta ja hankalin jama'a,domin kuwa ita ma ba baya ba wurin ƙira sannan zama da Biba dole ta koyi kyaran jiki,
Ba abinda ya shafe ta a haka ta je ta amso kayansu ta dawo dashi,

Zama tayi ta ci iya wanda zata iya ci sannan ta ajiyewa ma Biba nata,dan tasan idan tana barci bata son a tayar da ita...
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*04*

Washegari kuwa basu baro Hotel ɗin ba sai zuwa yamma,dama kuma ya garin Abuja yake in dai yamma tayi da traffic,yau kuma sai abun yayi yawa fiye da kullun,
Taja tsaki yafi a kirga ta kalli Direban Texi da ya dauko su"Malam hala dai akwai abinda yake faruwa ne a garin nan yau"

Dariya mutumin yayi "hala dai Hajiya baki da labarin yau a garin nan muna da babban baƙo"

Ummita ce tace"Babban baƙo kuma,daga ina? Na ga dama ai garin Abuja kullun cikin karɓar baƙi muke,abun dai na yau ne naga yayi yawa"

"Ai in fada maki Hajiya yau babban malamin nan wanda ake ji dashi a kasa baki daya shi ne zai kawo mana ziyara a garin Abuja,kuma ga shi jama'a daga ko'ina a faɗin Nigeria zuwa suke domin halarta wannan taron Wa'azin"

"Ni kuwa waye wannan malamin"

Dariya yayi "Bara dai na faɗa maki sunan da Matasa ke masa laƙabi da shi,wato YOUNG USTAZ"

Lumshe ido tayi sakamakon faduwar gaban da taji haka kawai daga jin sunan da aka kira,dama kuma tun tambayar farko data mai bata kara fadin komai ba duk maganar da suke tare da Ummita suke,

Maimaita sunan Ummita tayi "Young Ustaz kuma malam,maimakon naji kace Shik wani ko Malam wani"

Murmushi yayi"saboda ko ke kika gan shi kinsan ya dace da a kira shi da young din,domin kuwa shi din yaro ne matashi wanda yake ji da ɗanyen ƙuruciya,da kuma baiwar ilimin Addini da Allah ya mashi,hmm young ustaz kenan,duk yanda ake maki bayanin shi to ya fi nan sai dai kin gan shi kawai,yauwa yau ki kasance a gaban talabijin za'a hasko wa'azin,zaki ga yanda tsantsar kyau da kamala ke zuba,za ki ga......

Da sauri ta katse shi saboda ji tayi kamar kanta na juyawa"ya isa haka Malam sauke mu a nan"

Tsayawa yayi kuwa suka sauka a bakin wani gida matsakaici mai matsakaicin ƙyau,
A kwai mai gadi a ƙofar gidan,wanda yana ganin su ya mike da sauri ya buɗe masu karamin kofa yana gaishe su,

Gidan akwai fili sosai ga wurin parking motoci,wanda naga manyan motoci masu matsifar tsada guda uku,kaloli daban-daban,

Tsayawa tayi a bakin korido tana jiran Ummita data je dauko makulli a ƙasan wani tukunyar fulawa,
Tana daukowa tazo ta buɗe suka shiga,
Chapter 2 · 0% Book details