← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 96

Sashe 51

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hawaye ne ke zuba daga idanun shi yayin da jikin shi yayi sanyi "Na yi danasani yafi a kirga, Nadama nake a kowace safiya a ko wani lokaci,sai dai ɗan Adam bai isa ya mai da hannun agogo baya ba,idan lokacin ya wuce koda da awa daya ne bai isa ya mai da shi baya ba,ina dana sani akan komai dana aikata a wancan lokacin,ina son Salma so mara misaltuwa,a wancan lokacin bam san Me ya shiga kaina ba,son abin duniya da ƙuruciya su suka ja min,ina kallon irin son da take min kamar irin wanda ba zata iya rabuwa da ni ba ne,shi yasa na aikata komai, amma nayi Alkawarin duk in da take zan nimota,zan tabbatar na dawo da ita cikin rayuwar mu koda nawa zan kashe sai na nimo ta"

Bai bashi amsa ba yasa kai ya fita dan jin waɗannan maganganun na Yusuf kona mashi rai suke yi,ko da aman wuta yake yi idan har ta dawo ko inda take ba zasu bari yaje ba balle yayi tunanin mai da ita rayuwar shi Kazantacciya.

___________*LEGOS*

Koda aka kaita Asibiti bata cikin hayyacinta dan haka da sauri likitoci suka karbe ta,ta samu rauni akai sai da aka nannade kan,sai hannun data samu Targaɗe shima aka daure aka sakala hannun da wani abu mai haɗe da Belet har ta wuyanta hannun ya tsaya a kirjinta,

Sai washegari da safe ta bar Asibitin bayan Direban da Alhaji Mansur ya haɗa ta dashi ya gama biyan komai,ba yanda basu yi da ita ba ta zauna ta ƙara hutu amma taki yarda saboda tana ganin aikin dake gabanta,

Gida ta koma tayi wanka sannan ta sha magunguna ta dauki jakka da takardun da take buƙata ta fito,
Ce ma direban tayi ya kai ta gidan yarin da Suraj yake,
"Hajiya ya kamata ki huta" Ya faɗa,

Dan wallahi ba karamin jin jiki tayi ba,har fuskarta ta faɗa saboda stress yawan tafiya da rashin natsuwar zuciya,

"Idan na dawo zan huta" Ta bashi amsa,

Ya ya'iya dole ya tuka ta har in da take bukatar zuwa,nan ma sai da aka dan bata mata lokaci kafin a bata damar ganin shi....

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*51*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Tunda ta shigo cikin wurin ya kafe ta da idanun shi yana ƙare mata kallo tun daga sama har kasa,
Turo baki take yi domin irin kallon da ta tsana kenan a cewarta duk masu irin wannan kallon gulma gare su,

Jan kujera tayi ta zauna sannan tayi sallamah,

Ba tare daya dauke kai ba ya amsa mata,

"Ni bana son irin wannan kallon kamar za'a cinye mutum"

"Idan har kinsan baki da kwarin gwiwa jurewa me na zuwa"

Kauda kai tayi tana hararan gefe "ba sai ka kore ni ba" Ta fada a hankali,

"Ina jin ki"

Daura jakkan hannun ta tayi saman teburin wurin ta ciro wayar ta,
Ƙoƙari take ta kunna amma ta kasa saboda bata saba amfani da hannun hagu ba,hannun dama kuma shine mai ciyo wanda aka nannade,
Dagowa tayi ta kalle shi,har yanzun kallon ta yake bai da alamun ma zai yi magana,

Haushi ya fara ba,amma tunda har bai ji tausayin ta ba yace ta kawo ya taimaka mata ita kuma ba zata taba cewa ya taimaka mata ba,
Dan haka ta Daura wayar a saman teburin ta shiga latsawa dai daya har ya buɗe ta shiga in da take buƙata sannan ta tura mashi a gaban shi,

Mai da hankali kan video dake magana yayi,likitan Grandma ne yake mai bayani akan tafiyarsu har kuma garin da suka isa wato ITALY,sai video fuskarta da aka yi tana kwance amma ya tabbatar mashi daga dukkan alamu za'a dace saboda babban Asibiti ne kuma akwai ƙwararrun likitoci a wurin suna kula da ita yanda ya dace,

Ganin video ya ƙare ne ya turo mata wayar ta gabanta,

Wani karamin takarda ta kara tura mashi"ga address din Asibiti ko da zaka je idan an kammala wannan case din"

"Wani tabbaci kike dashi akan za'a gama?

" Eh to har yanzun gaskiya ban samu abinda nake nima ba,amma ina saka ran komai zai iya juyawa har yanzun muna da sauran kwana biyu a ƙasa "

Lumshe ido yayi ya buɗe bai ce mata komai ba,

Zazzage tarkacen dake cikin jakkan ta tayi sai dai ba takardun data kawo domin ya saka hannun,
Karamin tsaki taja "ina ga na baro su gida,yanzun dole na dawo gobe"

Mikewa yayi yana ƙoƙarin wucewa,
"Ina kuma zaka tafi?

Juyowa yayi kaɗan" Akwai abinda zan maki ne?

"Amma! " Sai kuma tayi shiru"Anyway babu komai "

Har yayi taku uku taji ba zata iya jurewa ba dan haka cikin jin haushi ta dauki bairon dake gefenta ta wurga mashi da karfi,ai kuwa cikin sa'a ya sauka a keyar shi,

Ko daga kai ta kalle shi ba tayi da dan ita bata masan ya same shi ba tsabar masifar da take yi ita kaɗai "mutum ko tausayi bai da shi,ba zai ma iya cewa me ya same ni ba,sai dai kawai ya kureka da idanun shi kamar wani kunkuru,mtwss ko kunkuru na da ido ne ma oho"ta karasa fada tana daukar jakkanta ta fita ba tare data juya in da yake ba dan ita a tunanin ta tuni ya shige,

Ganin ta wuce ne yasa ya sauke wani ɓoyayyen ajiyar zuciya,
Yasan koma menene ya same ta baya rasa nasaba da wannan case din,shi yasa tun farko yace ta ajeye case din saboda yana mata gudun irin haka,sai dai tunda ta fara ba shida damar da zai dakatar da ita sai dai kawai ya bita da addu'a Allah ya kare ta,
Dukawa yayi ya dauki Bairon ya shige dashi.

_________*KANO*

"Kaka ya kamata ki saka Biba ta dawo in ya so sai a daukar masa ƙwararre lauya "

"Wai idan ta dawo Uwar me zata maka Ibrahim,ni fa ban gane ba,shin zaka samar masa wani lauya a ina,ko ubanka bai iya samu ba sai kai?ni fa bana son haka ka barmu muji da abinda muke ji"

"Kaka nifa tsoro nake ji kar ta saka yaya na ya ƙare a gidan yari,Biba fa a matsayin yar aiki take a gidan nan yanzun kuma wai lauya,duk ta ina hakan ya kasance,ko dama dai tana da wani manufa ne na zuwa wannan gidan"

Gabaɗaya falon shiru yayi yayinda zuciyar kowa ya koma kan kiyasta masa wacece ita din,

Ammi ce ta katse tunanin nasu ta hanyar tacewa"wani irin magana ne haka kike faɗi Amira?koma menene Biba tayi yanzun ba lokacin maida magana da maida tunani baya ba ne tunda har tana iya bakin kokarin ta wurin ganin Yayan ki ya dawo,Lauyoyi nawa ƙwararru aka samu kuma aka roka dan kawai su tsaya masa amma suka kasa,sai ita da take mace ta sadaukar da komai nata domin ta taimaka masa shine har kike da bakin fadin haka?bana son ki zamo mai son zuciya,idan har ba zaki yaba mata ba ki bita da addu'a kar na kuma jin bakin ki a wannan maganar gara ki yi shiru "

Dukar da kai tayi"ki yi hakuri Ammi zan kiyaye"

"Kwana biyu ma ba'a samun number ita Biba dan na kira naji yanda take amma ban same taba na tambaye su Abbu sunce badi san masaukin data koma ba suma kwana biyu kenan rabonsu da ita" Cewar Nurudeen.

"Ka kara kira yanzun ko za'a dace" Cewar Kaka,

"Bari na kira " Ammi ta faɗa tana ɗaukar wayar ta,
Cikin sa'a kuwa sai gashi ringin biyu aka ɗauka dan Video call ne,

"Ammi ina wuni?

Bata ma iya amsa mata ba sai kallon ta da take cikin yanayin tashin hankali" Me ya same ki Biba haka a goshi?

Dan murmushi tayi ganin yanda duk hankalin ta ya tashi "ba komai Ammi kawai dai na ɗan samu Accident ne ƙarami"

"Wannan ai ba karamin bane,kalli yanda dun fuskar ki yasha Plaster"

Shafa goshin ta tayi "babu komai ai naji sauki"

Kaka ce ta karɓe wayar"ke bani in ganta,"
Sake mata wayar Ammi tayi,ta san dole akwai wani abu a kasa,zata kira ta suyi magana amma ba anan ba,dole tana buƙatar kaɗaicewa,ba zata so wani abu ya samu yarinyar ba saboda ita ma din tamkar amana take a wurin ta,

"Ke Habiba me ya faru dake haka?

Sai da tayi dariya" Kaka hatsarin mota na samu amma da sauƙi "

"Garin ya haka ta faru,hala dai kin bari ana ta sharara gudu dake ne?

" A'a kaka kawai dai tsautsayi ne Allah ya kawo,kuma ma abin da sauƙi tunda targade kawai na samu a hannu sai wannan kujewar na fuska,shima zai warke cikin kwana biyu "

"To shi kenan Allah dai ya kiyaye ki ya kuma kare ki dan Allah ki dinga kula"

"To Kaka na godewa sai anjima"

"Yauwa Allah maku Albarka"

Da Amin ta amsa tana kashe wayar.

Mikama Ammi wayar ta tayi"yarinya abin tausayi "

"Kaka ina da magana "

Duk juyowa sukayi kanta, sai dai ita bata damu da suba domin abinda ta ƙudurta sai tayi,
"Maijiddarh ta samu mijin aure"

"Me kike nufi Hajiya Saude?

" Goggon yara abinda kika ji shi nake nufi domin ba zan bar yata tayi ta zama har ta tsofe min a gida ba bayan ta isa aure,tunda Allah ya riga ya nuna mana halin wancan"

"Amma ai kamata yayi ki bari koma menene sai ayi bayan fitowar Sujar"

"Allah ya kiyaye waye yasan sanda zai fito haka kawai,wallahi ba zan jira ba tunda har na samu ta amince tana son shi"

"Kaka ya kamata ki yi mata magana ke ko zata saurare ki" Cewar Goggon yara,

"Me kuwa zan ce mata tunda ta riga ta yanke hukunci,kinsan idan zuciya ta bushe Addu'a ce kawai zata iya sanyaya shi har ta mai dashi mai taushi"
Chapter 51 · 0% Book details