← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 96

Sashe 40

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin ta sani sai ji tayi ana Sallamah,
Da sauri ta kara wayar a kunne sai dai sam ta kasa magama,dan jin muryar shi kaɗai da tayi yasa taji faduwar gaban ta ya ƙaru a maimakon raguwa,

Shima daga nashi ɓangaren jin shiru ne yasa shima yayi shiru yana sauraran yanda take sauke numfashi a hankali,
"Idan kinsan ba kida ƙwarin gwiwar yin magana me na kira?

Cikin mamakin abinda ya faɗa tace" Ya akayi kan nice "

"Tambayar da kika kira kimin kenan?

Turo baki tayi" To nama fasa faɗa tunda abinda zaka ce ke nan"

"Shiken " Ya faɗa yana ƙoƙarin sauke wayar,

"Wait, wai kai mai yasa baka iya lallashin mutum bane?yanzun baka son kaji me zan faɗa?ka sani ko abunda zai amfaneka ne?

Dan murmushi taji yayi wanda kaɗan sautin haka ya sauka a kunnen ta," Daga dukkan alamu yau Mage a tsorace take,me ya faru?

Dan shiru tayi kamar mai nazarin abin da zata faɗa,ta kwashi kusan mintuna goma ba tare data iya furta komai ba,yayin da shi kuma yayi shiru shima yana sauraren yanda Lokaci-lokaci take sauke numfashi ba tare daya ce mata komai ba kuma bai kashe wayar ba,
Sai da ta gaji da saƙawa da warwarewa kafin tace"ina ganin kamar akwai abinda ke shirin faruwa"
Jin shiru yayi ba tare da an bata amsa bane yasa ta cire wayar a kunnenta ta duba,ai kuwa har lokacin yana kan layi,hakan yasa ta maida wayar kunnen ta"kana jina kuwa?

Nan ma sai da aka dauki ƴan sakanni kafin taji yace"Umm "

A hassale tace "to baka ce komai ba?

"Ina jinki"

"Ai Nasan kana jina"

Kamar wanda baya son maganar yace"me zai faru?

Wannan karon ta kasa rike bacin ranta dan haka cikin masifa tace "ban sani ba,idan ka ga dama duk in da kake sai ka kiyaye idan kuma ka yi sake ka rasa rayuwar ka kai ka sani"ba tare data jira taji mai zai ce ba ta kashe wayar,dan ba karamin haushi ya bata ba,haka kawai tana ƙoƙarin taga ta ankaran dashi amma ya tsaya yana nuna mata miskilanci,tsaki ta ja,tana ƙoƙarin tashi ne taji saƙo ya shigo wayar ta,kamar ta share sai kuma ta bude "I know you need me a life"
Abinda saƙon ya kumtsa kenan,
Ta maimaita ya kai sau nawa amma ta rasa gane ina ya dosa,
Yinin ranar tayi shine ba'a cikin natsuwa ba,domin hankalin ta a tashe yake,bata san me zai faru da ita ko shi ko Ummita ba,idan har suka ci nasara akan shi kamar sun samu nasara ne a kanta,idan kuma wani abune ya samu Ummita bata masan me zata iya aikatawa ba nan gaba,
Abunda ta jima rabonta da tayi shine yau ta tashi tana yi,wato Sallah Nafila wanda rabon da tayi ta kai shekara uku zuwa huɗu.

Anashi ɓangaren kuwa yana gama tura mata sakon ya maida kanshi ya jinginar yana rufe idanun shi yana nazarin kalamanta,sai dai baya son ya kawo komai a ran shi,
Jin ana kiran Fasinjojin da zasu tafi Nigeria ne yasa ya tashi ya ƙarasa,dan yanzun jinginsu zai tashi,wanda zai sauka ne a Legos,
Bayan kammala duk wani bincike aka basu dama suka shiga jirgi,bakin shi dauke da Addu'a,ƙarfe shidda na yamma jirjinsu ya sauka a Legos,
Duk yanda yaso ya kwana a gida dole hakura yayi ya kama Hotel saboda ma'aikatan airport din sun tabbatar mashi da babu jirgin Kano sai dai zuwa gobe da safe ƙarfe goma,
Dole ya hakura,
Babban daki ya kama na kwana daya a babban Hotel din daya sauka,wanka ya fara yi sannan yayi ordan Abinci yaci,
Ganin lokacin sallah Isha'i yayi ne yasa ya fito daga dakin bayan ya kulle ya fita domin duba ko akwai inda zai samu masallaci kusa,dan sam baya son yin sallah shi kaɗai a gida ko a daki indai ba ya kama bane,
Tafiya yake yana ɗan duddubawa kafin Allah ya taimake shi ya samu,lokacin ana ƙoƙarin tada sallah,duk da yake masallacin na Yarbawa ne hakan be dame shi ba domin Allah daya suke bauta ma,dan haka yabi su Jam'i har aka idar sannan ya koma masaukin shi,har ya kusa isa daki yaji kamar ana magana ana kuka ta wani lungu,kamar dai ya share sai kuma ya matsa ta wurin yana lekawa,
Wani mutumin ya gani daga dukkan alamu ma'aikacin wurin ne,dan sanye yake da kaya irin na masu aiki a kicin,
Waya yake yana sharban hawaye,
Ganin Suraj din tsaye yana kallon shine yasa ya yanke wayar da sauri yana tambayar shi da harshen Turanci,"ko akwai abinda yake buƙata ne?

Girgiza mashi kai kawai yayi alamun babu,har mutumin zai wuce sai ya dakatar dashi,yana tambayar shi me ya same shi yake kuka"

Kamar bazai faɗa ba amma ganin yanayin Suraj din kamar mai kuɗi kila yana iya tausaya mashi yasa ya faɗa mashi Ƙanwar shi ce ta mutu wata biyu kenan tana Matuwari,shida maman shi dan Baban su ya mutu,kun kasa tara kudin da za'ayi bikin Binne ta,to yanzun gashi a ƙauyen su har an fara yima Mamar shi gori,shi yasa abun ke damun shi,kuma ya roki alfarma wurin aikin shi a bashi rancen dubu hamsin amma sun haka shi"ya karasa faɗa wasu hawayen na zubo mashi,

Suraj mutum ne mai tausayi,wanda ba shida rowa ko kyashi,bashi da nuna Ƙabilanci ko Addini,idan zai maka abu da zuciya daya zai maka ya wuce ba tare daya waiyaye abun da ya maka ba,
Dan haka cikin tausayawa yace,ba tare daya tambaye shi nawa ne kudin ba,yace"Bani Account number ka"

Cikin sauri kuwa ya karanto mashi,rubutawa yayi a wayar ba tare da yace mashi komai ba ya juya yayi tafiyar shi,shima mutumin da kallon mamaki ya bi shi har sanda ya buɗe ƙofar dakin wanda kuma a daidai lokacin yaji Alart, yana dubawa Dubu dari biyu ya gani,
Da fari bai yarda ba,sai da ya kara karanta sakon yakai sau biyar sannan ya tabbatar,ai kuwa tsalle ya kama shi kadai yana kukan murna da jin daɗi,bai taba tsammanin a Musulmai akwai mutanen kirki irin wannan mutumin da yaga sunan shi ya bayyana a Account din wai Suraj ba,abinda ƴan uwan shi suka kasa mai,shi kam ba zai taba mantawa da wannan mutumin ba,ai kuwa washegari da safe zai bar garin ya komai ƙauye,dan ƙanwar shi bikin gata za'a mata.

Da sallamah ya shiga dakin duk da yasan ba mai amsa mashi,zama yayi kan kushin yana cigaba da jan carbinshi ya ɗauki wasu yan lokuta a haka fakin ya mike,kai tsaye banɗaki ya shiga ya leka sai dai babu komai a ciki,haka kurum yake jin wani irin a jikin shi kamar akwai abinda ba daidaiba a dakin,sannan kamar kanshin dakin ya canja mashi,har kasan gado ya duba sai dai bai ga komai ba,
Mikewa yayi yana tunanin gara kawai ya fita ya masu magana a canja mashi ɗaki ko kuma yama bar Hotel din gabaɗaya,dan zuciyar shi ya fara bashi Something is not right some were,Gara ma kawai ya tafi,
Har ya kai hannu zai buɗe Sif din kaya yaji ana danna karrawar dake nuna alamu ana buƙatar shigowa,da yaso ya share har ya dauko kayan shi,wanda ba komai bane sai karamin jakkan shi mai ɗauke da wasu takardu nashi,
Jin yanda ake danna kararrawar babu kakkautawa ne yasa yaje ya buɗe ƙofar,
Tsayawa yayi yana kallon su cikin mamaki yayin da mamakin shi ya karu a sanda daya daga cikin su yaja hannun shi ya saka mashi Ankwa yana fadin"you are under Arrest,Abisa laifin kisan kai"

Wannan karon abin yazo mai ata inda bai taba zata ba,kisan kai kuma,kisa fa!inna'lillahi wa'inna ilaihi rajiun,abinda yake ta maimaitawa kenan,

Shiga cikin dakin suka yi yayinda sauran mutum uku suka da suke riƙe da shi har cikin dakin,
Kallon ikon Allah kawai yake yi,har zuwa sanda daya daga cikinsu ya buɗe Sif din,ta iya yuwa su basu shiga Shock ba,amma kam shi yayi suman wucen gadi yayi,
Domin Gawar Mace ce makale a jikin Bangon Sif din yayin da jini ke zuba a jikinta kamar yanzun aka yanka ta,haka kuma an cire idanun ta da Harshen ta,
Duk kiran sunan Jijos kawai suke kasancewar su Arna,
Ko mintuna biyar ba'a yi ba,sai ga masu binciken gawa da Ƴan gidan Jaridu sun shigo dakin yanda kasan wadanda dama a shirye suke,
Nan take aka shiga ɗaukar shi hoto tare da gawar,
Abin karin girgiza a wurin shine Jakkan shi da aka buɗe aka samu Idon matar da kuma harshen ta a ciki,
Tunda yake bai taba shiga tsananin tsoro da tashin hankali ba irin wannan,da ba ɗan karfin Addu'ar da yake yi ba da tuni shima ya yanke jiki ya faɗi,
Daya daga cikin ma'aikatan ne ya ɗaga gabjejen hannun shi ya koda mai lafiyayyen Mari,"dama ku musulmai ba kuda imani,to Asirin ka ya tonu yau"
Rintse ido yayi yana jin raɗaɗin marin a saman fuskar shi wanda nan take wurin yayi jawur dashi kasancewar shi farin mutum,
Nan suka jawo shi suna cukui_kuye dashi suka fito dashi daga dakin,
Bai ma ƙara tabbatar da abinda ke faruwa dashi da gaske bane sai lokacin suka fito dashi wajen Hotel din,
Dandazon Yarbawa ne wanda suke dauke da makami akan lallai sai an miko masu shi sun ƙona shi da ranshi,
Nan take ƴan sanda suka zagaye shi yayinda jifa ta ko'ina tashi yake yi suna burin dai su same shi,
Cikin haka ne wani daya wurgo katon dutse bai tsaya a ko'ina ba sai gefen goshin shi,ai kuwa nan take jini ya balle ya shiga bin gefen fuskar shi,
A haka suka jefa shi a cikin motar su suka wuce dashi yayi da shi kuma a nashi bangaren yake ji kamar duniyar ce ta kife gaba daya,ko kuma mafarki ne yake yi ba gaskiya bane,sai dai duk yanda yaso ya farka daga wannan mummunan mafarkin abin ya gagara,domin iduk sanda ya motsa acikin waɗannan maguzawar yake ganin shi zaune a wulaƙanci,
Yau shine haka,a garin mutanen da basu san darajar musulmai ba,shi SURAJ ABDUL BASIR,
Acikin abinda bai wuce mintuna ishirin ba komai ya canja.
Chapter 40 · 0% Book details