← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 96

Sashe 35

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*36*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Ganin irin kallon da yake jifanta dashi ne yasa tayi ɗan tsam kafin kuma ta kyara tsayuwarta tana ɗauke idanun ta cikin nashi"ummm gama Yayan naku ya zo,bari na baku wuri "ta faɗa tana hawa bene ba tare da ta ƙara juyowaba,
Dan rigima a maimakon tayi ɗakin ta sai shigewa ɗakin shi tayi ta kwanta saman dago tana juyi" Gaskiya wannan gadon yafi laushi,wancan sai saka ciyon baya,ai sai dai kayi haƙuri amma nan dakin zan dawo da kwana".

___ƙara daure fuska yayi wanda dama yake a cunkushe saboda rashin walwala,
Takowa yayi ya zauna a daya daga cikin kujerun,

Nan take suka shiga gaida shi,sai dai bai amsa masu ba sai kallon Aunty Hajjo da yayi"barka da Safiya"

Bata bashi amsa ba sai ma cikin ɓacin rai da tace"Abinda wannan yarinyar ta faɗa gaskiya ne?

Kauda kai yayi be bata amsa ba,to me zai ce mata a gaban kanne shi,

"Suraj tambayar ka fa nake yi,ni da nake son su Abba su huce a maida saka ranar ka da Maijiddarh,amma ji abinda yarinyar nan ke fada"

"Me zai hana ki bincike ta"yayi maganar kamar ba a bakin shi ya fito ba,

" Yaya"Amira ta kira sunan shi cikin jin haushi"dan Allah karka ja mana raini a wurin wannan yarinyar "

Wani mugun kallo ya watso mata"ita din Aunty ki ce idan har ni yayan ki ne,kar na kuma jin zancen rashin girmamawa daga gare ki"
Mikewa yayi yana dosar hanyar barin falon"bana son kananan magana "ya fada yana karasa faɗa.

Ajiyar zuciya ta sauke" Banga me zai hana na kyara ma yarinyar nan zama ba,ku tashi muje "
Haka suka bar gidan cikin bacin rai.

Sai zuwa ƙarfe biyu data gaji da kwanciya ta fito,shine ta kara cin karo da Akwatunan da suka kawo dazu,
Ɗauka tayi ta kai dakin shi ta jera sannan ta shiga budewa,ba laifi an zuba kaya sai dai ba masu irin tsadar nan ba,dan kudi Kaka taba Aunty Hajjo ta hado kayan saboda irin sana'ar da take yi kenan,shine ta zubo waɗannan,gabaɗaya kayan har akwatin idan aka duba kuɗin su basu wuce dubu dari bakwai ba
Karamin tsaki taja,ai ko dan kunnen da take sakawa yafi karfin gabaɗaya kayan balle yanzun data samu yancin akanda da take gidan su,dan haka yanzun sai abinda taga dama,

Daukar pant daya da Bran tayi sai doguwar riga da takalmi flart shoes ta saka,gyalen dan karamin Jallabiya data saka ta yane kanta dashi,
Dubawa tayi cikin kayan kwalli sai dai duk ciki ba kalan product din da take amfani dashi,dan haka man baki kawai ta shafa,ka karamin kyau kayan ya mata ba,dan kalar Ashe ne ma'ana ruwan toka.

Tana cikin fesa turare taji shigowar shi,sai dai bata juya ba dan tana iya ganin Reaction ɗin shi ta cikin madubi,
Murmushi ta saki tana juyowa cikin takun dai daya ta iso gaban shi "Mijina nayi ƙyau"

Ganin baida niyar kulata yasa ta ɗan bata rai "gaskiya Suraj idan ka bata fuska baka cika yin kyau sosai ba,ka dan dinga murmushi mana" Ta karasa faɗa da murmushi a fuskarta,

"What ar you doing? Ya tambaya yana karema dakin kallo harda gadon shi da ke hargize,

Itama bin dakin da kallo take bi" What? Ta maida masa tambayar shi,

Nuni yaimata da akwatunan dake jere da kuma gadon dake a yamutse har zanin gadon ya fado kasa,"what is the meaning of dose thing here?

Bata fuska tayi"ai gadon dakin can ne yake saka ciyon baya shi yasa na dawo nan,idan kuma kaima nan ɗin ta maka We can share this room,kaga sai mu dinga kwana tare akan nan zai fi armashi ko? Ta faɗa tana faɗaɗa fara'ar fuskarta,

Dafe Kwankwaso yayi yana ɗan furzar da murmushin takaici "what is your name ma again?nunata yayi da yatsa " Habiba,for God sake stop being like a real wife,I now you are just Acting,pretending,please a don't want any trouble, keep pretending like one,but stop coming into my way,I don't like you at all,I think you have to know even living with you is like hell to me,Dan haka kici gaba da aikin dake gabanki amma ki fita harka na,sannan ki tattara ki barmin daki kafin ranki ya ɓaci "
Har ya juya zai bar dakin ya kara juyowa "na baki minti biyar" Ya faɗa yana karasa fita,

Duk da maganganun shi sun soso mata zuciya nisa ba kusaba,hakan yasa ta lumshe idanun ta na wani lokaci kafin ta buɗe tana ƙoƙarin shanye duk wani ɓacin ranta,
Zaciyarta take lallashi,tabbas da ba dan akan aikinta take ba da Suraj bai isa ya faɗa mata irin waɗannan maganganun ba,sai dai zata dinga tuna Ummita wanda hakan ne zai kasance mata ƙwarin guiwa,zata iya jurewa ko dan ita,tayi haƙuri da duk wani abunda zai mata har zuwa sanda zata samu nasara ta fita rayuwar sa,zata dauki ƴar uwarta su koma kasar waje kamar yadda suka tsara,to amma me take da yace tana pretending ne akan komai,ɗan shiru tayi tana nazari,ko da yake yasan basu son juna shi yasa ya faɗi haka,to kuma yace aiki,wani aiki yake nufi,wani zuciya ne ya bata amsa to ko dai yasan aikin da take yi ne,da sauri ta girgiza kai,ina ba zai sani ba,ta yaya ma zai sani,kawai dai yana nufin,shiru tayi to yana nufin me?ajiyar zuciya ta sauke koma dai me yake nufi bashi yake nufin yasan komai ba,
Ɗan murmushi ta saki wanda ita kaɗai tasan ciyon da take ji a zuciyar ta dole ta maida shi murmushi,
A kwatunanan ta fito dasu ta ajiye a ƙofar dakin ta sannan ta sauko kasa,
A falo ta same shi yana waya,
Zama tayi tana jira ya kammala sai dai yana ganin ta zauna ya mike yana ƙoƙarin barin wurin ba tare daya katse wayar da yake yi ba,

Ganin abunda yayi ne yasa ta tashi tabi bayan shi har zuwa falon gidan na biyu,sai dai jinta a bayan shi yasa ya katse wayar ba tare daya kammala ba ya juyo yana kallon ta"Lafiya? Ya tambaya,

Sam ita bata son wannan tsaretan da ido da yake yi,sai kace mai ƙoƙarin daukar wani abu a fuskar ta,bai san irin kwarjinin da yake mata ba,dauriya kawai take yi tana nuna masa gagaranta,
Tsuke baki tayi tana juya idanunta a hankali tace"bana son irin wannan kallon"

Babu zato taji yace"idan baki da ƙwarin gwiwa jurewa ki daina baiyana"

Da sauri ta kuma juyowa,
har yanzun kuma idanun shi tsaye suke a kanta,sai dai duk yanda taso fassara yanayin fuskar sa ta kasa,"idan da banida shi da ban shigo rayuwar ka ba"

Giranshi daya ya daga"duk juriya irin na mage ba hakan ke nufin zata kai labari ba"

"Duk iya farauta irin na Zaki hakan ba yana nufin wata rana zai nime taimako wurin mage ba,sai dai kuma ina mai bashi shawara da yabi takunshi a hankali domin shima gab yake da fadawa hannun mugayen mafarauta,wa ya sani ko mage ce kawai wacce zata iya taimakon shi a wannan lokacin" Ta faɗa tana ƙoƙarin daura nata idanun akan nashi,sai dai tsabar mugunta Inji ta irin nashi sai dauke kanshi yayi a kanta yana canja zance ba tare da ya faɗi komai ba kamar yadda taso,sai cewa yayi"me kike buƙata "

Haushi ya bata,amma ita ma sai ta share,ko ba komai a juye zuwa rafi wata rana Tulu zai fashe"ina buƙatar ATM card din ka,zan fita siyayya akwai abinda nake buƙata "

"Me yasa sai nawa,in baki da kuɗi ki bar fitar mana" Ya juya zai tafi,

Gaban shi tasha tana wani marairaice fuska"Allah sarki kai da malami ne,mai tsoron Allah,kuma kasan haƙƙoƙin miji akan matar shi,ko da ta ƙarya ce,balle namu an shafa fatifa,k.. "

Mika mata ATM card din yayi daya ciro a cikin walet"Mage mai kwanciyar ɗaukar rai"

Da sauri ta amsa"wata rana Magen ce zata taimake ka"

"8487" Ya faɗa yana barin wurin,

Jujjuyawa take a hannun ta"Ohho dai ba dai ka bani ba,ka ji a jikin ka"ta fada tana fita falon gabaɗaya,

Tsayawa tayi tana kallon motocin dake fake a wurin ajiye mota,
Direban gidan ne ya taso da sauri yazo inda take"Hajiya fita zaki yi ne?

"Eh ina makullin wannan motar? Ta nuna wani sabuwar mota Maron kolo dake cikin leda alamu ma ba'a taba amfani dashi ba,

" Yana wurin Ubangida domin ba'a taba amfani dashi ba"

Gaskiya motar ya tafi da imanin ta,taji kewar tuƙi,ji take kamar ta buɗe ta shiga taja,sai dai bata son nuna zalamar ta a fili,dan haka tace"ɗauko ma kulli muje shopping "

Da sauri yace"An gama Hajiya "

Shi ya buɗe mata ta shiga sannan ya ja suka tafi,
Babban wurin siyayya na garin Kano ya kai ta,
Farko layin data fara shiga shine na kayan shafa,Glow gold ta dauka man da take shafawa,wanda kudin sa Naira dubu saba'in ne,sai kuma Sabulan wanka na ruwa da turare wanka kala-kala,man baki, da jan baki,sai kuma turaruka inda anan ne tayi ainahin ɓarna da kuɗi,
Bangaren kayan sakawa ma ta kwasa ba kaɗan ba,dogayen riguwa jallabiyoyi,dana kanti,ƙananan kaya wanduna da riguwa sai after dress,pant da bran,takalma,Agogo,sarka na wuya da kunne,man wanke kai dana kamshi,a takaice duk wani abunda ta san tana buƙata ko kuma zata buƙata sai da ta siya,dan bayan but din motar sai da aka cika shi da kaya,
Chapter 35 · 0% Book details