← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 96

Sashe 36

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har zata fita sai kuma ta tambaye ko akwai inda ake sai da waya a ciki,nan ma nuna mata akayi,lafiyayyen Iphone ta dauka amma na dubu dari da gamsin ta dauka,a cewar ta gaba ta canja wani,sai kuma tayi ɓangaren gyaran jiki,in da anan aka kara kyara mata suma aka wanke kafa da hannu,sannan aka mata ƙunshi a kumbuna na hannu da ƙafa duka ja,dan bata son barin kumbunan ta fari,
Ba ita ta fito wurin ba sai kusan biyar na yamma,a gajiye suka dawo gida,
Cikin sauri ya buɗe mata ta fito yana ta faman washe baki,dan shikan yau ta burge shi,tunda sau biyu tana aiko mai da abinci bayan haka harda turmin zani biyu masu kyau ta siya ta bashi tace ya kai ma matarshi ko Maman shi,gaskiya ba ta da rowa,
A bakin ƙofar falo suka jibga kayan shi kuma Bala yana kwasa yana ajiyewa a ƙofar ɗakinta na sama,
Ita kuma tana shigar dasu daki,
Sai da ta kammala sannan ta jera komai in da ya dace zuwan lokacin har an tada sallah Magrib,dan haka ƙara kyara dakin tayi ta share ta goge sannan ta shiga wanka,
Tana fitowa tayi sallah sannan ta fito dan mai da mashi da ATM card din shi,
Sai dai tana tura kofar dakin ta shiga taga gabaɗaya yanda kasan ba dakin ba,domin babu abinda ba'a canja ba na dakin tun daga kan gado har komai na banɗaki data leka,sai ƙamshi dakin ke zubawa kamar na sabuwar Amarya,
Tabe taki tayi"kudi na faɗa maka ƙarya "kwalbar turaren data siyo mashi dan karami mai matukar kyau da kamshi ta ajiye mashi nan saman madubi ta fita,
Cike da tunanin ya kamata ta fara gudanar da aikinta zuwa gobe da safe idan ya fita,dan yau kam ta gaji...

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*37*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Tana shiga daki ta turo kofa ta zauna kan gado,
Jakkan data fita dashi dazu ta buɗe,wanda kwalayen Sigari ne guda biyu a ciki,ciro kwali daya tayi ta cire wanda zata sha guda daya sai wani magani data balla guda daya ta raba biyu ta wurga a bakin ta tana tsosa ba tare data damu da dacin shi ba,
Sai da ta tabbatar ya narke sannan ta kora da ruwa ta kunna Sigret tana mashi kyakyawar zuka,
Tana kammalawa ta tashi ta cire hijabin dake jikin ta da zani ta maida kayan bacci wanda yake ɗan ƙaramin pant ida duwawu sai karamin singileti mai tsansi iya haƙarƙari,gabaɗaya tundaga shafaffen cikin ta har zuwa kasan maran ta a buɗe yake,yayin da Cibiyar ta dake sanye da ɗan kamin makale na zinari wanda zaka yi mamakin ta ina aka bula aka saka shi,dan har wani daukar ido yake yi,
Dama gashi suman kanta yasha gyara dan haka ta baje shi a tsakar bayanta yana lilo,
Shafe jikinta da turarukan kamshi tayi kamar yanda ta saba in dai har zata kwanta,
Jin kanta ya fara nauyi ne yasa ta tashi daga gaban madubi ta haye saman gado taja bargo sannan ta rage hasken wutar dakin sosai,
Lumshe ido tayi ta buɗe tana kallon Silin,abubuwa ne da dama suke dawo mata acikin kwakwalwa,ƙara lumshe ido tayi sai ga hawaye ya sauko ta gefen ramin idanun ta,
A hankali bakin ta ya furta "Ma" Ba tare da ta karasa ba ta haɗiye sauran a ranta,tana jin wani abu mai matukar girma da ɗaci yana tsaya mata a makoshi,
Tasan ita yarinya ce mai matukar Kawazucin iyayenta,har balle Mama,ko ina bata yar da ta je ba tare da ita,sai makaranta daya zama dole,to amma gashi cikin lokaci kankani komai ya sauya,tana rayuwa ba tare dasu ba,tana rayuwa ba tare da tasan halin da suke ciki ba,tana rayuwa ba tare da jin muryar su ko ganin su ba,shin suna raye ko sun mutu,
Tunanin hakan ne yasa ta fashe da kuka daga kwancen da take,kuka take sosai kamar wacce aka daka,
Rayuwar ta bai da wani amfani,ta shiga duniya ne kawai saboda bakin ciki,tana son taci gaba da gujewa wannan bakin cikin har zuwa ƙarshe,to sai dai ina ne ƙarshen?ta ina zata bi ta kai wannan ƙarshen?ko yaushe a ciki gudu take amma har yanzun bibiyar ta yake yi,duk da ta canja gari,ta canja suna,amma har yau ba abinda ya sauya,
Sai dai koda kafin ta kai wannan ƙarshen zata rasa ranta a hanya,ba zata taba juyawa baya ba ga inda ta boro,ba zata taba juyawa ba ɓalle ta ga nisan da tayi,ko da hakan na nufin zata iya fadowa daga saman tsaunin data hau,ba zata taba waiwayarsu ba har abada,

Ta dauki lokaci mai tsayi tana kuka kafin daga nan Sarkin iya sata ya dauke ta,wato Barci wanda tayi shi ba dan daɗi ba,

Jin yanda jikinta ke ciyo ne ya sakata tashi zaune ba tare data buɗe ido ba,dan ƙwayar data ci tuni ya gama jukuwa,
Saukowa tayu daga kan gado ta dawo kasa ta kwanta,nan ma ba daɗi taji ba sai ma mulmula data gama yi ta kara tashi, kai tsaye fita tayi ta nufi ƙofar ɗakin shi wanda yake kallon nata,
Turawa tayi ta shiga ba tare data damu da duhun da ɗakin ke dashi ba,
Da lalube ta faɗa kan gado tana jawo bargon data ji a shimfede ta shige,
Cikin ƙanƙanin lokaci barci mai matukar daɗi yayi awon gaba da ita,dama kuma gashi yanayin garin yau akwai sanyi,

Kiran sallah dake shigowa kunnen shine ya tilasta shi ƙoƙarin buɗe ido wanda yake jin yayi masa nauyi,
Ɗan shiru yayi yana saurare kamar mai nazarin wani abu,
Tabbas yana shakan wani irin kamshi wanda ya san ba daga jikin shi yake fitowa ba,sannan yana jinshi kamar a jikin mutum,
Hannu ya miƙa ya kunna wutar dakin gabaɗaya,sannan a hankali ya shiga yaye bargon dake jikin shi,
Wani irin zabura da yayi ya faɗo daga saman gado hakan yasa itama ta firgita ta mike tsaye cike da tsoro tana kalle_kallen ko abun gudu ne ita ma ta gudu,

Kallo daya ya mata ya kalli kanshi ai dasauri ya runtse idanun shi yana fadin"Bismillah,A'uzu billah,ya haiyu ya Kaiyum"
Da sauri ta duro daga saman gadon cike da tsoro ta dawo ta bayan shi ta rike mai hannu,cikin muryar Tsoro tace"Suraj mu gudu,ni tsoro nake ji hala maciji ka gani,dan Allah ka fitar dani "dan ita a rayuwar ta ba abun da take tsoro irin maciji,

Ba tare da ya kalli in da take ba yace" Fitar min a daki"

Gabaɗaya ma rungume shi tayi ta baya tana kwantar da kanta a bayan shi wanda bai saka riga ba,"A'a babu inda zan je,sai dai in goya ni zaka yi,tsoro maciji nake yi"

Duk wani addu'a da ya zo bakin shi faɗi yake a zuciya,ba tare daya dire wani ba yake daukar wanu,rokon Allah kawai yake daya mai tsari da ita da kuma sharrin ta,

Da kyar ya iya danne zuciyar shi"ki hau kan gado bari saka kaya sai na fitar dake "

Bata ci masa musu ba ta hau kan gadon ta tsaya tana kallon shi har ya saka doguwar Jallabiya ba tare da ya juyo ba ya nuna mata hanyar waje "zoki fita"

Makale kafaɗa tayi"Umm Umm"

Ranshi ne ya bala'i ɓaci dan haka juyowa yayi yana fuskantar ta dan dai kawai taga bacin rashin,sai dai duk yanda yaso ya jure kallon ta kasawa yayi,saboda yanda gabaɗaya ta turo baki ta narke yanda kasan wata Baby,gashi kuma duk wani motsawa da zata yi sai sharasharan rigarta na sama ya daga wanda hakan ke kara bayyana cikakken Kugun ta,da kuma ramin Cibiyar da ɗan makalen ke ɗaukar hankalin shi,
So yake yaga me a wurin,dan bai taba tsammanin ana saka abu a wurin ba,dan bai kasance mai kallon tsiraicin mace ba,
Da hannu ya nuna cibiyar nata"me kika saka anan"

Kallon inda yake nunawa tayi,ɗaga rigar sama tayi tana kallon shi"me?

Ɗauke kai yayi yana jin kanshi na sarawa,kafin ya tako inda take,ba zato taji ya jawota ya daura saman kafaɗa,a bakin ƙofa ya dire ta "ki cire wannan abun na Cibiyar ki" Garam ya maida kofar ya kulle,
Ƙwanƙwasawa ta fara tana kiran yazo ya buɗe mata,sai dai bai da alama zai buɗe,
Cikin jin haushi ta buga ƙofar ta da ƙofar,sai kuma ta dafe ƙafar tana faɗin"uch"falo ta koma kan kushi ta yi kwanciyar ta,har ya fito ya tafi masallaci ya dawo tana kwance,
Ruwan sanyi ya dauko a firig ya buɗe,
Ji tayi yanda ruwan sanyin ke ratsa ta yasa ta tashi a firgice tana niman wurin gudu,sai dai rike mata hannu yayi da hannun shi daya,duk yanda taso ta kwace kasawa tayi,haka kuma duk yanda taso ta rungume shi yaki bata dama,
Hakan yasa kawai ta sadakar ta tsugunna a gabanshi ta dukar da kai har sai da ya karar da gogar ruwa masu azaban sanyi a kanta,
Ji take kamar ta sheke saboda sam bata shiri da sanyi shi yasa ma ko abu mai sanyi bata cika sha ba,
Gashi ba kayan ƙwarai ne a jikin ta ba,ga sanyin AC dake ƙara butso sanyin,ta jike sharkaf yayin da
sumanta ya rufe mata fuska,
Dagota tsaye yayi da hannun shi dake cikin nata,
Murmushi ya saki wanda har tana iya jin sautin shi a kunnen ta,
Ta kasa buɗe ido saboda ruwan dake diga daga cikin kanta,ga kuma suma daya rufe mata rabin fuska,

Hannun ta ya riƙe duka biyu ya daura a saman ƙafar shi,
Suman daya rufe mata fuska yasa hannu yana maida mata dashi gefe,
Kallon lip din ta yayi yanda yayi jawor yana dan motsawa saboda rawar sanyi da take yi,
"Buɗe idanun ki"

Kin buɗewa tayi,saboda yanda ranta ke tafasa,

Ba zato taji hannun shi a saman boturan maɓallan rigar ta shara_shara na saman,

Duk da haka bata buɗe ido ba, sai ma ƙara rintsesu da tayi,
Chapter 36 · 0% Book details