← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 96

Sashe 49

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina butar ganin wannan number da aka kira ka dashi"

"Wayar ya faɗi,an sace wayar"

Jin ji na kai tayi"shin an sace ne ko ya faɗi ?

"Ya faɗi ne"

"Zaka iya komawa ka zauna"

"Na gode" Ya faɗa yana sauke wani ɓoyayyen ajiyar zuciya,

"Ya mai shari'a ina butar kotu ta Bani dama domin nayi magana da Manager Hotel"

Daya daga cikin masunjojin yace" Manager wannan Hotel din baya nan saka makon wani uziri da ya kama shi ta tafi garin su Jos"

Komawa tayi gaban koton"Ya mai shari'a sakamakon rashin kammala haɗa hujjoji na ina rokon wannan koton mai adalcin data ɗaga wannan shari'a daga nan zuwa ranar Ishirin ga watan nan"

Ɗayan Alkalin ne yace"sakamakon duba da wannan lamarin da kotu tayi,Kotu ta daga wannan shari'ar daga yau hudu ga watan April shekara ta dubu biyu da ishirin da uku zuwa goma ga wannan watan na April shekara dubu biyu da ishirin da uku"daga nan ya buga wannan ɗan sandan nasu,

Duk mikewa suka yi cikin girmamawa,
Duk da taso ta samu ƙarin ƙwanaki ta yanda zata yi bincike sosai a kan komai amma shine suka bata kwana shida kawai,
Duk da taga sanda suka biyo dashi ta gabanta zasu tafi dashi gakan baisa ta dakata daga haɗa takardun da take yi ba,har suka wuce dashi,

Tana fitowa ta samu su Dady suna jiran fitowar ta a harabar wurin

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*49*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Karasawa tayi in da suke tsaye,sai da ta kalli agogon dake hannun ta wanda ya nuna mata ƙarfe goma sha-biyu na rana,
"Barka da rana"

"Habiba me ke faruwa ne?cewar Abbu,

Murmushi ta saki,dama ta san hakan zai faru" Ba wani abu bane Abbu,ku kwantar da hankalin ku na maku Alkawarin idan komai ya lafa an gama wannan shari'ar zan sanar daku komai "

Pa ne yace "ki faɗa mana komai yanzun dai,da Ummu Salma muka ji fa kin gabatar da kanki"ya faɗa kamar adan hasale,

" Abu mai muhimmanci shine yanda Suraj zai fito,sannan koma menene ya biyo baya, na bar ku lafiya sai mun haɗu a kutu"tana gama fadar haka ta juya ta wuce,dan ba zata manta maganar A'i da tace mata karta yarda da kowa har a cikin gidan,

__________*Kano*

"Kaka wannan ba Biba ba ce?

Duk ƙara kurama TV ido suka yi,
" Kanbu,wallahi ita ce,kaka nifa na fara tsoron lamarin yarinyar nan,ki duba yanda tayi mana bazata a wurin taron mata malamai,yanzun kuma Lauya?

"Shi yasa naso tun farko na aure ta saboda nasan ita din Materiel ce"

Duk kallon mamaki suke mai,

"Ka nada hankali Nurudeen?

Bata fuska yayi yana kauda kai,dan abinda ya faɗa har cikin zuciyar shi ne,

" Ni dai in komai ya wuce a bin cike ta"cewar Hajiya Rahama

"Wallahi Momy na fasa zama likita lauya zan karanta,dubi yanda Biba ke zuba Turanci kamar ba a bikinta ya ke fitowa ba"cewar Hadiza,

" Ammi me ke faruwa? Ta faɗa tana kallon TV yanda ake zuba challenge,

"Koma me ke faruwa lokaci zai nuna"

_____________tana shiga mota tace ma direban"muje gidan yari"

"To Hajiya" Ya faɗa yana karya kwana,

Koda suka isa buɗe mata kofa aka yi aka bata damar yin magana dashi kamar dai jiya a wannan ɗakin,

Jan kujera tayi ta zauna suna fuskantar juna,
"Ina yini"

"Assalamu alaikum" Ya fada,

"Oh Assalamu alaikum"

"Wa'alaikumussalam,wannan ya zama abu na farko da zaki fara yi aduk sanda muka haɗu"

Turo baki tayi"har yana da bakin korafi"

"I can hear you"

"Akwai abunda nake buƙatar na sani ne?

Ganin irin kallon da yake mata ne yasa tace" Ina nufin a matsayina na lauyan ka"

"Babu"

"Akwai mana,kamar daga lokacin da gawar ya kasance a dakin da kake,ko kuma wani yanayi ko kuma dai abinda kake zargi ko wanda kake zargi, dole za'a samu wani"

"Duka babu" Ya faɗa a takaice,

Ajiyar zuciya ta sauke tana dafe kumatunta,yayin da hankalin ta ya tafi kan wani nazari na daban,

Zame hannun nata yayi daga tagumin da tayi wanda hakan yasa goshinta ya bugu da center table ɗin,

Dafe goshinta tayi tana shafawa,cikin jin haushi tace "me haka?

Kafaɗa ya daga" What"

Mikewa tayi sai kuma ta koma ta zauna da sauri tana sakin murmushi,"yauwa ina Kakan ka take,ina nufin a wani Country take "

Shiru yayi kawai yana kallon ta ba tare daya bata amsa ba,

Ɗan marairaice fuska tayi"bana son irin wannan kallon pls"

Kauda kai yayi yana ɗan lumshe ido kafin yace"me za'a "

"So nake kasa a canja mata Asibiti daga in da take,idan so samu ne har likita ka canja mata,idan kuma ka yarda da wannan kana ita daukar shi aiki har zuwa sanda komai zai kammala ya zama na babu wanda yasan in da take"

Tambayar daya jeho mata ne yasa ta dakata daga maganar da take yi,
"Me yasa zan yarda da ke?

Shiru tayi na wasu sakanni yayin da suka shiga musayar kallon na sakanni kafin ta dauke nata idanun" Wannan zabinka ne ka yarda da ni ko akasin haka"busar da iskar bakin ta tayi sannan ta dawo da kallon ta kanshi"ni ba kamar yanda kake gani na nake ba,ko da yake ina dauke da Najasa,haka ne tunda ni din *ƘARUWA CE* kana iya saka Hausar a haka,ta iya yuwa kasan abinda ya shigo da ni rayuwar ka ko baka sani ba,amma ina mai tabbatar maka haɗin kanka shi kawai zai saka mu tsira tare da kai,
Idan kuma har mukaci nasara zan bar rayuwar gabaɗaya ba tare da na bar maka wani abinda zaka tuna da ni ba,"

Jin kalmar data kira kanta dashi kaɗai ya saka zuciyar shi dukawa,
"Idan har baki ci nasara ba fa?zaki fita ki bar rayuwata?

" Duka daya ne?idan ka yi tunani akai kana iya sakawa a kira ni"ta faɗa tana mikewa,

Har ta kusa kaiwa ƙofa ta ji yace"Germany,Berlin, Mitte,Orthopedic Clinic (Campus Charite Mitte)
Takardar da ke ajiye a gabanshi da biro ya ɗauka yayi dan rubutun da bai wuce layi uku ba ya turo mata,sannan ya tashi ya wuce,

Murmushi ta saki tana bin shi da kallo kafin ta dauki takardan ta fita,

Daganan ta wuce cike da tunanin dole gobe zata tafi domin bata da isasshen lokaci.

______karan saukar Mari ne ya karaɗe dan madaidaicin falon,
Cikin masifa da tsananin bacin rai yace"i will killed you,me yasa baka faɗa min tun tuni ba sai yanzun,gashi saboda kai aikin da muka yi shekaru muna shiryawa kana kokarin ruguza komai,bayan mun sha matukar wahala kafin mu samu wacce zata iya "

Cikin tsoro da rawar jiki ya tsugunna a gabanshi "dan Allah shugaba kamin rai ba zan sake ba,ko da na bar ta Lafiya ta qlau ban San zata mutu ba"

Wani marin ya ƙara sauke mashi yana huci,"ita ce yanzun ta tsaya masa a matsayin lauya,bayan kwangilan da muka dauke ta,kalli sakon data turomin"ya faɗa yana nuna ma Abokin nashi saƙon,

"Yanzun mu kirata muji me zata faɗa"cewar Chief,

Duk na'am suka yi da hakan,dan haka wayar shi da yake kiranta dashi ya ɗauka ya shiga kiran number ta,
Sai da yayi ringin uku ba'a dauka,har ya cire rai za'a daga sai gashi yaji an daga,
Sai saita kanshi yayi,kafin ya ce" Me haka ke nufi?

Daga in da take zaune tana shirya wasu takardu ta bashi amsa"kamar me kenan?

Danne duk wani bacin ranshi yake kokarin yi"Ummu Salma,"

"Suna na ne"

"Sunan ki fa?Kotu fa?Barrister?me kike shirin yi ne,me manufar ki na kare wanda kike aiki a kanshi?ina bukatar karin bayani domin kinsan haka baya cikin tsarin aikin mu"

Dariya tayi irin mai tsayawa a zuciya na takaici "tsarin aiki fa kace?ohh na manta ashe aikin yana da wani tsari?" Ajiyar zuciya ta sauke tana busar da iska mai zafi daga bakin ta"ina da amsar duk tambayoyin ka,sai dai ba zan amsa maka su ba,da kanka zaka fitar da amsar ta hanyar aiki na,
Hmm kai har kana da wani ka'idar aiki,ai tuni na ajiye naka aikin a sanda ka karya alkawarin mu,mun maka aiki na tsayin shekara huɗu,amma ba kaji kunya ko tausayi ba ka kashe Ummi ta,sai dai ka sani wannan shine babban kuskuren da ka yi a cikin aikin ka wanda zai iya mai da maka aikin ka Sifili,kamar yanda bansan ko kai waye ba haka kaima baka san kome a kai na ba,dan haka wasa tsakanina dakai yanzun aka fara,
Ba zan taba bari ka samu nasara ba sai na tarwatsa duk wani guziri naka,sai na baiyana ka a idanun kowa"

Cikin tsawa mai haɗe da bacin rai yace"ke har wacece ke da kika isa ki bata shirin da ake yi tun kafin ki zo duniya,ke a tunanin ki zaki iya?shin zaki iya wasa da wuta a tsakiyar Teku?

"Idan har kai da wuta kake wasa to ni ruwa ce mai matukar sanyi,wannan wutar da kake takama dashi sai na kashe shi na bi ta kanshi"

"Zamu gani tsakanin ni da ke,?ki jira yi saƙonni na"

Dariya tayi,"babu abinda zaka iya domin ni *YAR TSANAR ZINARI CE* mai tattare da abin mamaki iri-iri,
Idan har ka iya to zaka iya taba ni ka zauna lafiya,idan kuma ka bata rawar ka da tsalle to dafi ne dane wanda yafi na maciji hatsari,idan ka shirya rasa rayuwar ka sai a kafta"Ta karasa faɗa tana sauke wayar domin dama ta tsammace abinda yafi haka daga gare shi,

A nashi bangaren buga wayar da kasa yayi yana wani irin huci kamar zai yi aman wuta tsabar bacin rai,
" Ina son a nimomin duk wani bayani dangane da wannan yarinyar"

"An gama Shugaba" Suka fada cikin girmamawa,
Chapter 49 · 0% Book details