← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 96

Sashe 32

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lumshe idanun shi yayi yana jin zuciyar shi na faman yi mashi zafi,har ɓalle idan ya tuna da ita da kuma abinda ta mai,idan har yarinya is capable of doing something like that,to me ne ba zata iya aikatawa ba,wama ya sani ko maza nawa ta haɗa baki dasu irin haka,
Tuna hakan kuma da yayi ne yasa yaji zuciyar sa na tashi sosai,da sauri ya dafa Farhan "tsaya"

Dan juyowa yayi"me kace"
"Ka tsayar da mota"
Samun gefen hanya yayi ya parker,
Da sauri ya fito ya tsaya a gefe ya shiga Kwara Amai,
Sai abun yayi kamar zai tsaya,amma da yayi tunanin Kiss din,nan take Aman ke dawowa har ta hanci yi yake yi,
Shi kanshi Farhan abin ya fara damun shi,goran ruwa ya dauko masa ya kuskure baki tare da wanke fuska,sannan ya taimaka masa ya shiga mota,
Kallon shi yayi zazzaɓin ƴan awoyi amma duk ya fada,fuskar shi yayi ja idan ka sanshi to zaka shaida bai da lafiya dan ko a muryarsa kana iya shaida hakan
"Muje Asibiti?

Jirjiza kai yayi kaɗan yana lumshe ido,

" Jikin ka ba ƙarfi,kana bukatar Medical attention "

"Kai ni masallaci"

Yana ƙoƙarin kara yin magana ne wayarsa da ke ta kara tun dazu bai sani ba ya kara daukar kara,
Kallon wayar yake yi da sunan Ammi ya fito baro_baro,
Sai da yaja numfashi ya busar yana kauda kai kamar ba zai ɗauka ba sannan ya danna wurin amsawa,
Sallamah tayi ya amsa "kazo ina son ganin ka"

"Idan an fito masallaci zan shigo"

"Ok"
Kashe wayar kawai yayi,
Suna isa lokacin har an fara kiraye-kirayen sallah,mutane nata Daura Alwallah,dan haka masallaci suka shiga,kusa da Abbu dake jan carbi ya samu wuri ya zauna kafin a tayar da sallar,
Abbu ya bada sallah har aka idar,bayan Addu'o'i ne ya sanar da daurin aure,kafin aka shiga fitowa da kwandunan goro Sweet da Dabino,
Kowa mamaki ya shiga yi irin wannan daurin aure na Ustaz Suraj,kafin kace me nan take mutanen da suka hallaci sallah a wannan masallacin sun fara Daura magana a social media,cikin kankanin lokaci magana ya zagaye gari wasu su ƙaryata wasu kuma su yarda,
Ana gama daurin aure dady ya dafa Kafadarsa ba tare da yace komai ba ya fita daga masallacin,
Ganin Abbu na magana da mutane yasa ya zame jiki ya bar masallacin ba tare da ya koma ko takan Farhan ba yayi shigewar shi cikin gida,
A hankali yake takawo hannun shi dafe da kanshi dake matukar Sara mashi,
Ji yayi an riƙo shi ta baya wanda hakan ne yasa ya juyo "me yasa zaka amince ka aure ta bayan kasan ina sonta,me yasa zaka dinga cin amana ta ka zagaya kana bata mata rayuwa,sam bata dace da mutum irin ka ba,ba zan kyale ka ba,sai na saka ka sake ta da bakin ka na aure ta"
Ganin bai da niyar ce masa komai ne yasa cikin jin haushi kuma ya sake shi ya wuce,

Shi bai ma sani ba idan da akwai ta yanda zai juya komai da ba'a kawo wannan matakin ba,duk da kalaman Nurudeen ɗin ya bashi mamaki jin yana sonta,karamin tsaki yaja kawai tare da nufar shiyan Ammi,

Zama yayi kawai a kan kushin yana jan carbi ba tare da ya shiga ciki ba,

Amira ce ta fito ta ganshi nan zaune,
Kasancewar taga idanun shi a rufe ne yasa ta koma dakin Ammi ta faɗa mata isowar shi,cewa tayi tace ya shigo,
Tana fitowa zama tayi kusa dashi"yaya"ta kira sunan shi,

Buɗe idanun shi yayi wanda har yanzun suke a firgice ya daura a kanta ba tare da yace mata ko mai ba,

"Da gaske ka auri Biba,an daura maka aure da ita yanxun kamar yanda naji a masallaci?

" Ummm "ya bata amsa a takaice,

Bata fuska tayi tana bata rai" Dama Aunty Maijiddarh ce,yaya Biba fa yar aiki ce ba tayi koda karatun Boko ba,amma Aunty Maijiddarh tayi Degree a bangaren Arabic,gata wayayyiya,amma wannan ko baki kayi ta yaya zata fitar da kai kunya,bana tunanin ma ta iya koda karatun sallah ne,ku malamai wani lokaci ana gaiyatar wurin walima ko wa'azi tare da matan ku,ko kuma su a gaiyace matan naku,gata baƙauyiya ko saka kaya bata iya ba,kalli ma wasu irin manyan kayan da take sakawa kamar wata Goggo,kai kuma duk da kana malami amma kai ɗan zamani ne,ɗan Gaye,gaskiya ni dai yaya an cuce ka sam baku dace ba,bata min ba"

Yasan duk abinda ta faɗa gaskiya ne,duk da akwai wata a kasa tsakanin shi da yarinyar ba haka bane zai sa ya bada kofar da ƙannen sa zasu wani samu dama a gare shi"ita din Aunty kice ki dai na fadar haka a kanta"

Buɗe baki tayi"Aunty kuma?Allah y.....

Katseta yayi"ina Ammi?

Tsabar takaicin rashin bata amsa da baiyi ba yasa da hannu kawai ta mai nuni da hanyar dakin Ammi,
Bai ce mata komai ba shima ya Mike ya wacewar shi ɗakin,

Da sallamah ya shiga,tana zaune saman darduma ta amsa mashi,
Shigowa yayi ya zauna dan nisa da ita kaɗan yana tankwashe kafa,
Da hannu ta mai alama da ya matso,
Matsowa yayi zuwa in da take,
Tsira mashi ido tayi na wasu ƴan sakanni,yayin da kanshi ke duke,
Hannun ta daya ta daura saman fuskar shi "are you ok?

Jinjina kai yayi" I am fine"

"But you are not"

Dan murmushi ya kakaro "I will be ok in time"

Ajiyar zuciya ta sauke"kayi haƙuri wannan ne kawai mafita"

"I hate it"

"Ni ma haka,sai dai at this stage dole ita kadai zata iya tunda ita ta fara,we have to Trust her,we have no option,you have to endure it,can you do it for me? Ta faɗa idanun ta na cika da hawaye,

Hannun ta dake saman fuskar shi ya rike ya sumbata" Insha Allah,for you and grandma"

"Thank you and im Sorry it all my fault from the beginning"ta faɗa hawaye na ƙara bin fuskarta,

Rungume ta yayi " Haka Allah ya tsara tun farko,ke ma ba yin kanki bane,ya kamata ki bar faɗin haka a yanzun"

"Har sai ranar da komai ya zo karshe sannan zan huta"

"Komai ya kusa zuwa insha Allah"

"Ya kamata ka tafi Asibiti tare da Farhan"

"Na ji sauƙi"

Girgiza kai tayi"ka kula da kanka shine abu mai muhimmanci"

"Zan kula Ammi,"ya faɗa yana ƙoƙarin mikewa,

" A ina zaku zauna?

"Sai yanda su Abbu suka tsara"ya fada yana mata sallamah tare da barin dakin cike da tunanin me zai je ya tarar dakin Kaka.

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*34*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Bakin shi dauke da sallamah ya shiga falon bayan sun amsa mai,

Sai da ya zauna kusa da Kaka sannan ya gaishe su,amsawa suka yi ba cikin walwala ba,shiru yayi kawai kanshi a duke ba tare da ya kuma cewa komai ba,

Abbu ne ta kalli sauran mutanen dake falon,sannan ya ce"Alhamdulillah Allah mun gode maka daka tsara mana wannan ranar a haka,ina fata wannan ya zamo izina a sauran yaran gida,me kokarin aikata irin wannan kuskuren sai ya kiyaye ya kuma san me zai iya faruwa dashi,kai kuma Suraj mun maka haka ne bawai dan ba musanka ba,sai dan muna son kare mutuncin ka dana wannan gidan shi yasa,sannan iyayen ita yarinya sun zo kuma an daura aure cikin mutunci dan haka dole mu gode ma Allah "

Duk jinjina kai suka yi cikin gamsuwa da maganar shi,
Dady ne yace"to yanzun ina zai zauna da matarshi "

Goggo ce ta amshe maganar da faɗin "me kuma zasu zauna su yi mana a gida?ai shi yanzun ba ƙaramin yaro bane tunda har yasan ya saka mace a ɗaki,dan haka ya tattarata suje can gidan shi su karata tunda Allah ya hore mashi,mu kuma ya bar mu muci gaba daba ya'yan mu tarbiyya yanda ya kamata"

"Sosai ma maganar ki gaskiya ce,ni yanzun gashi can an bar yata da jinyar zuciya,dan haka abun ya isa haka,muma a ba ya'yan mu wuri su sha iska"cewar Hajiya Saudat,

Abba Mustapha da tunda suke magana bai saka masu baki ba, yadan yi kyaran murya,kiran sunan shi yayi wanda hakan ne yasa kowa yayi shiru yana jira yaji me zai ce "Suraj"

Dago kanshi dake duke yayi ya amsa a hankali "Na'am Abba"

"Shin ko Kanada abun faɗa"

"A'a Abba"

"A kan hukuncin da muka ɗauka fa,shin baka ganin bamu maka adalci ba,gashi ko dangin mahaifinka bamu ni ma ba"
Dan guntun murmushi ya saki wanda ya ɓoye sirrin dake ranshi,tare da raunin shi,"ku din ma iyaye na ne,duk hukunci da kuka yanke zan karbe sa hannu biyu"

"Na gode da girmamamu da ka yi,yanzun ka ɗauki matarka ka tafi da ita gidan ka,idan akwai abunda kake buƙata ka kirani ka sanar da ni"

Mikewa yayi,domin dama dauriya ce kawai yake yi,"na gode Abba "sallah ya masu sannan ya fita,

Kallon sauran yaran dake falon yayi" Ku tashi ku tafi na sallame ku"

Duk tashi sukayi suka fita kowa da kalan abunda yake sakawa a zuciyar shi,
Chapter 32 · 0% Book details