← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 96

Sashe 75

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kira ne ya shigo wayar Abdulmalik wanda tun jiya ake ta dun shi da kira amma yaki dagawa kasancewar shi sam baya son ɗaga baƙuwar number,
Tsaki yaja yana faɗin "wannan ko maye ne haka zai ganni ya barni"

"Kai dawa? Cewar Abdulmajid dake ƙoƙarin mika ma Abdulrahman kofin shayin daya hada mashi,

" Wallahi tun jiya wani number ya azabeni da kira"

"To ja ɗauka mana,ka sani ko wani ne da ka sani,ni bansan me yasa kake da irin wannan ra'ayin ba,irin kune idan mutum na niman taimako har a kashe shi baku sani ba saboda wannan ɗabi'ar"

Dariya sukayi shida Abdulrahman dake kurban shayin shi,

"Yama katse bari a ƙara kira sai na ɗaga"

Bai ma gama rufe baki ba kuwa sai gashi an ƙara ƙiran,ɗauka yayi tare da yin sallamah,sai dai jin muryar wanda ke magana ne yasa da sauri ya saka wayar a amsa kuwa ta yanda duk zasu iya jin abinda na cikin wayar ke faɗa,

"Hello,Hello Abdulmalik kana jina Yusuf ne"

"Wani Yusuf? Ya tambaya kamar bai gane me magana ba,

" Yusuf mijin Salma"

"Oh kana nufin tsohon mijin Salma?

" Kaga ba nida lokacin wannan yanzun haka ina Kano na gano Asibitin da salma take ba ta da lafiya sai dai an hana ni shiga dakin da take,dama na maku alkawarin ai duk inda take zan nimota,yanzun haka gani a gaban dakin,dan haka kuna iya zuwa a yau ku dubata ku gani"

Duk shiru suka yi suna sauraren shi har ya kai karshe"yanzun kai kana kofar dakin Salma ne?

"Eh" Ya bashi amsa,

"To ina zuwa" Yana fadar haka ya kashe wayar yana kallon su "hmmm lallai Yusuf,hala shi bai san yanzun sama tayi ma yaro nisa ba ne?

" To me zaka yi da kace ya jira ka?

Ɗan dariya yayi yana kallon agogon dake manne a jikin bangon dakin,"nasan yanzun haka Suraj ya kusa isowa,"mikewa yayi"bari naje na manna mai hauka,domin yanzun ne lokacin ramuwar gaiya "

"Kai dai ka yi a hankali kasan sai za'a ma aiki,karkaje ka yi wani dogon magana"

Bai gama sauraran su ba ya fita yana dariya kasa_kasa.

___________A babban haraban Asibitin motocin suka yi parking,daya daga cikin security din ne ya buɗe mashi ƙofa,har ya sako ƙafa daya waje yaji wayar shi na ƙara,dan dakatawa yayi gani number da take kiran shi,
Sai da yayi ɗan jim kafin ya ɗauka wayar,sai dai bai yi sallamah ba kasancewar ya san da wanda yake magana,

Daga ɗayan bangaren ne aka kira sunan shi cikin harshen Turanci "Suraj Albishirinka?

Murmushi yayi jin abinda yace ya san tabbas akwai labari mai daɗi kenan" Goro fari kar Dr"

Kamar a mafarki yaji yace mai "Kakar ka ta tashi "

Shiru ne ya rasa wayar har tsayin mintuna biyu,
Ya san dama za'a rina "kana jina Suraj"

Wani dogon ajiyar zuciya yaja yana saukewa yanayin da yaji idanun shi na cika da hawayen da bai san ko na menene ba"Umm"

"Da gaske nake yi ta farka bayan dogon suma na tsayin shekaru goma sha ɗaya,sannan munyi observing din ta babu wani damu sai dai dan wanda ba'a rasa shima cikin lokaci ƙanƙani zata dawo dai-dai domin nan a kwai kayan aiki sosai wanda zai taimaka mata har jijiyoyin ta su sake,"

Murmushi ya sake wanda ke fita tare da hawayen dake sauka a fuskar shi "ina take?

" Tana barci a yanzun haka amma daga nan zuwa awanni uku zata tashi,zan haɗa ka da ita,sannan yaushe zaka shigo domin tana buƙatar ka a kusa da ita?

"Nan da awanni goma "

Murmushi shima yayi daga nashi bangaren "sai mun ganka" Daga nan ya sauke wayar,

Hannun ya daga yana kwararo ma Ubangiji yabo da kirari domin ya dawo mashi da ran da ya daɗe da fara cirewa a lokacin da bai yi tsammani ba,
Karasa fitowa yayi yana saisaita yana yin sa,a yanzun burinsa daya ne shine yaga fuskar kakar tasa,

Tafiya yake yi cikin yanayin da zai nuna maka shi din lafiyayye namiji ne mai jini a jika,da kuma takama da kuruciyar sa,yayinda security din shi ke taka masa baya suna doshi cikin Asibitin.......

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*76*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Murmushi kawai suka yi,

"Karku damu babu wata matsala tattare da ita" Cewar likitan da ya gama dubata,

Godiya suka yi masu sannan suka wuce.

Kaka ce da ta kasa hakura tace"Abdulrahman ko?ta faɗa tana nuna shi,

Girgiza kai yayi"A'a Abdulmajid "

"Yauwa Abdulmajid me yasa tunda kuka zo baku shigo cikin gida ba,sannan a ina kuke zaune?

"Da fari a Hotel muka sauka,amma sai Suraj ya matsa sai mun koma gidan shi,"

Kallon su tayi tana kara kallon Biba dake kwance "daga dukkan alamu ku ba matsiyata bane balle ace sabida hakan Biba ke aikatau,ko dai akwai wani dalili ne?

Duk kallon Nurudeen suke suna tunanin amsar daya dace su bashi,

" Tabbas maganar daka faɗa gaskiya ne,sai dai ka sani ita wacce kuke kira da Biba ba shi bane asalin sunan ta,Sunan ta shine Ummu Salma Abdullah,yace yar gata kamar sauran yan gatan yaran da iyayensu ke ji dashi,ita din sanyin idanun ahalin mu ne,abu ɗaya kawai zan iya faɗa maku Kaka"ya juyo yana fuskantar Kaka"tsayin Shekara biyar kenan da muka kwashe muna nimanta bayan barin ta gida,cikin ikon Allah kwanaki uku da suka wuce muka samu kira daga mijinta Suraj,ya faɗa mana yasan komai game da ita,sannan a lokacin da take jin cewar ya kamata ta koma wurin iyayenta da yan'uwan ta,sai gashi ta haɗu da wannan hatsarin, dan haka Kaka muna masu matukar baku haƙuri akan ɓoye maku ita wacece da Salma tayi,sannan muna matukar gode maku akan riƙe ta da kuka yi hannun biyu,Ubangiji ya albarkaci rayuwar ahalunku,sannan Kaka kiyi haƙuri dama muna shirin zuwa har gida wurin ki idan munga ta farka lafiya ita da ɗan uwan mu,da fatan zaki yafe mana?

Murmushi ta saki yana rike hannayen su,"babu komai Allah ya yafe mana ya muka bata lafiya"

Da Amin suka amsa,

Balki ce tace"me yasa to ta bar gida"ta faɗa tana tsare Abdulmajid da ido,

"Idar har ta tashi in har tana da ra'ayin faɗa maku zata faɗa,"

Tabe baki tayi"to ai shikenan"

Murmushi yayi yana rayawa a rashi wannan sai an yi tsiwa,

Nurudeen ya ɗan kara kallon dakin kafin yace"ina Suraj din yake?

"Dazu tafiyar gaggawa ya taso mai kuma ya tafi"Abdulmajid ya basu amsa,

" Bayan anyi ma matar shi aiki ba zai iya tsayawa ta farka ba,yanzun har a kwai tafiyar da yafi matarsa muhimmanci?

Duk shiru suka yi an ma rasa mai bashi amsa,

"Ai ya kira ni ya faɗa min,kuma na tabbatar da koma menene ba karamin abu bane" cewar kaka,

Ba tare daya ce komai ba ya juya ya bar dakin,

"Mu zamu tafi amma dai zuwa gobe zaku shigo ku dubamu ko?

" Insha Allah Kaka"

Har bakin mota suka raka su sannan suka dawo ciki.

Basu jima da tafiya ba ta farka,nan ma sai da likitoci suka ƙara dubata suka tabbatar da cewa babu wata matsala sannan suka wuce suna masu matuƙar farin ciki,sannan da gindaya ma yanninta abinda ya kama tayi da wanda bai kamata tayi ba a yanzun.

Tunda ta buɗe idanun ta take bin ko ina da idanun ta,da take ganin kamar mafarki take yi ko kuma tayi wani irin tafiya ne mai matukar nisa wanda har yanzun bata dawo ba,ko kuwa ta dawo ne,
Duk in da suka bi da ido kawai take bin su,

Ji tayi an riƙe mata hannu,tare da kiran sunan ta"Salma "

shin da gaske da sunan data manta an taɓa kiranta dashi yanzun dashi aka kira ta,
Tsira mashi ido tayi tana buɗewa yayin dake lumshewa duk a lokaci ɗaya,

Ganin yanda hawaye ke fita daga cikin idanun su ne yasa a hankali ta kwada kiran sunan su dan son tabbatar da ko da gaske su din ne zaune a gabanta,
"Yaya Abdulmajid" Ta furta a hankali,

Kara matse hannun ta suka yi cikin nasu yayin da Abdulrahman ya kara fashewa da kuka"dan Allah ki yafe mana kanwar mu"

"Da gaske ku ne?

" Mu ne,Salma!mu ne"

Mai da idanun ta tayi tana lumshewa jin ta gaji da magana,

"Yaushe kuka zo?

Ganin tamkar ta gaji da maganar ne yasa yace" Muna nan tare da ke,ki samu ki huta zuwa da safe zamu karasa magana "

Tun tana kallon su har bacci mai nauyi ya kara dauke ta,

Sanin dokar Asibitin na ba'a kwana da mara lafiya ne yasa dole ganin baccin ta yayi nisa suka koma masaukin su bayan sun duba Abdulmalik.

Washegari kuwa koda suka shigo cikin Asibitin ƙarfe takwas na safe,dan lokaci ne ake bari a ga masara lafiya,
Tana zaune a saman gadon ta an ɗan dago da gadon ta yanda zata fi jin daɗin zama,idanun ta a lumshe suke sai dai ba barci take yi ba,

Jin sallamar muryoyin da take dokin ji ne yasa ta buɗe manyan idanun da suka shanye saboda ciyo tana daurawa a kansu,

Su kansu kallon ta suke yi cikin tsananin bege da kewa,domin shekaru biyar ba wasa bane,

Tabbas suna,domin a jiya gani take tamkar mafarki kawai take yi,

Gani suke yanzun da ta bude ido kuma ta tashi zaune sai tai masu girma,sai suke ganin tamkar ba wannan yar kanwar tasu ɓace wacce suke kula da ita a duk lokacin da take tafiya,sai suke ganin tamkar ba ita bace take zama a cikin su suke wasa tare da dariya tare,suke kuma dauke duk wani kuruya da hauka bana,yau sau suke ganin ta fita masu daban tamkar dai an canja ta,

Jin hawaye ya sauko daga cikin idanun ta ne yasa tayi sauri saka hannu tana sharewa,sai dai kuma sun kasa tsayawa sai ma ci gaba da zuba da suka ci gaba da yi,
Chapter 75 · 0% Book details