← Book details Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 96

Sashe 67

Yar Tsanar Zinari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah ya riga yayi ki mai ƙarfi sha'awa,shi kuma bashi da ra'ayi akan mace,zamanku akwai cutarwa mai tarin yawa Salma,sai dai hanya daya ce wacce za ku bi daga ke har shi ku zauna lafiya cikin kwanciyar hankali ba tare dakun rabu ba"

Dago jajayen idanunta tayi tana kallon mahaifiyar nata"wani hanya ne Mama?

"Zan faɗa maki,amma ki bari sai gaki gani ga kuma Yusuf"

"To yaushe zai zo?

" Ai na faɗa maki yana hanya na tabbatar zuwa anjima zaki ganshi,bari na hado maki shayi sai ki sha kafin a kammala abinci,ni zanje na duba yayan ki a asibiti"

"Ki ce Ina gaida shi Mama,sannan yayi sauri ya ji sauki gobe Birthday dina"

Murmushi tayi tana shafa kanta"baki manta ba"

"Umm"

A ranar ma koda Yusuf din ya iso da wuri bai zo ya duba ta ba duk da Baba ya faɗa mashi batun zubewar cikinta,sai ƙarfe tara na dare,

Duk da bata jin daɗin jikinta a haka ta ƙara yin wanka ta dan shirya sannan ta fito falo in da yake zaune,

Hmm jama'a kuɗi yayi,domin kuwa idan kasan Yusuf ada yanzun in ka ganshi ba lallai bane ka gane shi,
Zama tayi kusa dashi,tana ƙoƙarin ɓoye damuwar dake fuskarta "barka da isowa"

Ko kallon inda take be yi ba"Baban ki ya faɗa min abinda ya faru dake,Ashe ciki gare ki,to Allah ya kyauta,sai dai ki sani nayi farinciki zubewar shi domin ban tashi ajiye yara ba"

"Yanzun duk wannan tafiyar da kayi dan ka faɗa min haka ne?

Sallamar Mama ne ya kase shi daga amsar da zai bata,

" Yusuf video dana gani a wayar ka kai da Baba na menene?

Dagowa yayi ya kalle ta ta kuma kalli Mama da ta zauna"me abinda kika gani?

Share hawayen da ya sauko mata tayi,"Mama ki fada mashi ya min ƙarin bayani "

"Ai ba sai na maki karin bayani ba,itama tana iya maki tunda ta san komai"

"Kunga yanzun ba wannan maganar ba,ke Salma ki bar dauko wannan maganar,domin ba na son na sake jin shi a bakin ki,ni da nake son na samar maki mafita ta yanda zaki zauna da mijin ki lafiya,dan Allah ki natsu ki ban hankalin ki"

Shiru tayi kawai tana kallon Mama,domin ita ta ma rasa me suka maida ita,

"Kuna jina,hanyar da naga zai fi maku shine mai zai hana ke Salma ki yarda da wani namiji,ina nufin a duk sanda buƙatar ki na ɗa namiji ya taso ki ni me wani namijin ya sauke maki,tunda shi mijin ki bai da sha'awa,ko ya ka gani Yusuf?

Dariya ya fashe dashi sosai har da tafa hannu"kai lallai Mama ƙwaƙwalwar ki na ja,ni tuntuni da wannan shawarar kika ba mu ai da abin bai kai haka ba,gaskiya in dai ni ne wallahi ba matsala na amince da wannan shawarar "

Ji tayi kamar bugun zuciyar ta zai fito tsabar yanda yake harbawa,ji take kamar bata fahimce in da zancen su ya dosa ba"Mama me kuke nufi,Zina fa kenan,so kuke ke da Yusuf nayi zina da auren shi a kai na,?

"To me a cikin,ba gashi shi ya amince ba,ko kina da wata hanyar ne bayan wannan?
" Inna'lillahiwainna'ilaihirajiun"abinda take ta maimaitawa kenan,domin ji take kamar kanta na juyawa,

"Mama keda bakinki kuke cewa na aikata zina da aurena,?Yusuf da amincewar ka,?" Kara kallon su take da kyau dan so take ta tabbatar ko da gaske sune ɗin a gabanta,
"Ke ba Mama ta ba ce,ba maman dana sani bace! Nayi dana sanin kasancewarki uwa a gare ni,Gara ace wasu matsiyata ne iyayena baku ba,na y......

Saukar lafiyayyen mari ta ji a saman fuskarta,, nuna kanta tayi cikin tsananin bacin rai"do you think is easy for me na fada maki haka? Ni fa mahaifiyarki ce,y......

Wani Envelop ya ciro a Aljihun shi ya wurga mata"idan har ba zaki bi wannan hanyar ba,banga anfani zaman mu ba,domin ba na son takura,gashinan takardar saki ne,na sake ki saki biyu"

Daga zaunen da take ba ta san sanda ta zamo kasa ba,ta ma saka cewa komai,sai binsu da ido da take yi har ya juya ya bar dakin,

Cikin jin haushi Mama tace"ai yanzun sai ki samar ma kanki mafita"ta juya ita ma ta bar dakin........

Hmmmm.

🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*67*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*

Ta ma kasa yin kuka,zuciyar ta nauyi ya mata,yayin da idanunta ke ganin dishi_dishi,

Da kyar ta iya mikewa,da bin bango ta isa shiyan mazan gidan,
Ganin falon su a buɗe ne yasa ta shiga,Abdulmajid ne zaune yana cin abinci,
Ganin yanda ta shigo ne tasa ya Mike da sauri yana isa in da take "me ya faru,ke da bakida lafiya da sai ki kirani a waya,

Mika mashi takardar hannun ta tayi,amsa yayi yana fadin" na menene?

Ganin bata bashi amsa bane yasa ya buɗe yana karantawa,sai kuma ya saki murmushi"kai amma na ta yaki murna,at list yanzun zaki dawo hankalin ki,gaskiya naji daɗi "

Hawayen da suka kasa fitowa ne suka sauko "Yaya,Yusuf yaci amana ta, y.....

" Kinga dakata,ai kome ya maki ke kika ja,wani irin bayani ne ba mu maki ba a kanshi,karki manta na faɗa maki komai zai faru tsakanin ke da shi karma ki nufoni da batun dan haka ke ta shafa,ina fatan yanzun zaki yi hankali"

Juyawa tayi inda take jin motsin Abdulmalik,
Shima girgiza kai yayi"kinga je ki kwanta zamu yi magana da safe,dan ni yanzun ta lafiyar Abdulrahman muke ba naki ba"

A haka ta juya ta fito sai dai ba ta shiga cikin gidan ba,domin ji take gabaɗaya duniya ya mata zafi,bata taɓa tsammanin zata haɗu da irin wannan lokacin a rayuwar ta ba data roki Allah ya dauki ranta tun kafin yau.

Ta kusan kai ƙarfe biyu na dare zaune a wurin,ta ci kuka har ta gode Allah kafin ta tashi ta koma cikin gidan,
Ko da ta shiga daki ma kasa kwanciya tayi,sai zama da tayi a kasa,da tayi tunanin zata iya samun sauki a wurin Ƴan uwanta,sai gashi sun nuna mata sabanin tunanin ta,ita kuma wanda take gani tamkar majingina a wurin ta,sai gashi ita ke kokarin turata wuta,yanzun Hope din ta daya ne shine Baba,so take ta ganshi ta faɗa mashi komai ko zai karya ta mata,ya kuma samar mata mafita,
Jira kawai take gari ya waye, ta san ƙarfe takwas take dawowa.

A haka ta zauna idanun ta a bushe ar garin Allah ya waye,ganin ƙarfe tatwas da mintuna goma ne yasa ta fito,babu kowa a falon nasu masu aiki sun kammala gyara,dan haka dakin shi ta nufa kai tsaye,
Har ta kai hannu zata tura kofar dakin ta ji hayaniya na tashi yana fitowa daga cikin dakin,
Dakatawa tayi sai kuma ta juya zata koma,dan ta san Mama ce a dakin,yanzun kam bata shirya haɗuwa da ita ba,
Sai dai jin an kira sunan Yusuf ne yasa ta daka,

Baba ne ke faɗin"dan ya sake ta me na bacin rai a ciki,bai mata ƙoƙari ba,saboda ni ne fa ya amince ya aureta har yake zaune da ita, "

"Amma shine zai sakar min yarinya a gaba na,wallahi karya yake bari mu haɗu dan abin ba zai mai daɗi ba"

"Karma ki fara,domin kin San yanda nake son Yusuf ina iya yin komai akan shi,har ta ke ina iya rabuwa dake"

"In dai akan waɗannan ƴan iskan abokan harkallanka ne ai kasaba"

"Ni bansan in da yarinyar nan ta gado irin wannan jarabar ba na tsiya,ke me yasa ba zaki koya mata irin yanda kike yi ba"

"Me nake yi?

" Kin dai san ba zan taba bari Yusuf ya haihu ba,ki bata shawara tabi ta hanyar da kike bi,idan tana son yara ko nawa ne taje ta haifa zamu karba "

"Wai me yasa baka da adalci ne a rayuwar ka,kana son yanda ka bata min rayuwa na bata rayuwar yata,saboda ba kai ka haifa min ita ba,na tabbatar ubanta ba zai taba son haka ba"

Dariya ta ji ya fashe dashi sosai kafin yace"sannu,yanzun ke a yanda kike idan aka ce ki faɗi waye uban Abdulrahman zaki faɗa,balle na sauran yaran naki,na tabbatar ko wanne da ubanshi,ita wannan yar gwal din naki Nasan ko kashe ki za'ayi ba kisan wanda ya maki cikinta ba,saboda tsabar mazajen da kika bi"

"Me ka maida ni,ko da yake koma me na zama ai kai ne Sila tunda baka biya min buƙata na sai dai kace na nime wasu mazan tunda kai maza ƴan uwan ka kake bi,
Kuma yara na duk nasan Ubannin su,ita Salma ne dai kawai ba zan iya gane waye mahaifinta ba,kuma koma waye bai da amfani tunda kai kaji zaka iya karɓar ya'yan dan kawai ka ɗauke zargin mutane a kanka,
Kaga bama wannan ba,yanzu ya zamu yi da batun Yusuf?

"Ki bar batun Yusuf,domin ba zan iya hakura dashi ba ko nan da can,Gara da auren ya mutu,ki je can ki san yanda za ki yi da ita"

Da rarrafe ta karasa shiga cikin daki,banɗaki ta shiga ta dinga kwara amai kamar zata amayar da kayan cikin ta,
*ban taba sanin cewar ni ƴar Zina bace sai yau!a zinan ma ba'asan waye yayi ciki na ba!haka kuma yanni na maza suma duk ba Baba bane ya haife su,Mama zina take yi!Baba kuma Madigo!harda mijina!sun ciyar damu da haramun!sun tufatar damu da haramun!sun saka munyi ilimi da haramun!wannan dalilin ne yasa na ajiye duk wani abu da nasan su suka yi min,sai wanda na siya da kuɗi na,shi kaɗai na dauka,a wannan lokacin ban ƙara awa daya ba acikin gidan na ajiye ma su Mama wasika na bar gida,wannan shine dalilin da yasa nayi nisa da rayuwar su,na bar masu komai nasu,domin ba zan iya jurewa ba,ba zan iya ba,idan na zauna tare dasu bayan nasan zunubin da suke aikatawa mutuwa zan yi*
Chapter 67 · 0% Book details