Sashe 99
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
dubansa gurin Waira. Shiga mota na kai ki gida Ta girgiza kai da sauri hawaye na mata zuba, jikinta sai rawa yake ita dai daman can bata son ta ga ana tashin hankali balle kuma a yanzu da take ganin kamar saboda ita ne komai ya faru. Da ido Maleek yayi mata alama da ta wuce zuwa gurin motarsa. Ta fara takawa Ameer ya fisgota ya dawo da ita. You should know your limit kai ba ubanta ba ne da zaka rika juyata yadda kake so she's under no one control but me Saboda kai ne ubanta kenan? Saboda ni ne silar zuwanta nan Maleek yayi murmushi da ya fi kama da dariya. Yarinyar da ka ce baka sani ba? Yarinyar da ka bari a mota saboda kana tunanin ta mutu? Yarinyar da ka wulakanta? Ashe dai ka santa kenan Maleek what a shame Okay that's enough, kuna kunyata kanku ne kawai a gaban idona, ku daina saka ta a cikin matsalarku you guys have no idea what she's going through Ummi ta kama hannun Waira dake ta kuka ta nufi motar da suka shigo da ita ta barsu a tsaye idan ma cinye junansu za su yi sun dade ba su yi ba. Ganin ran Ummi ya bace ya saka Maleek bin bayanta ya bar Ameer tsaye a gurin yana kallonsu. Ummi da Waira baya suka shiga shi kuma ya shiga gaba yaja motar suka kama hanya. I warned yarinyar nan, Ummi do you plan this? Yanzu kuma ni ce bar zargi ka gama da da zaka dawo a gurin uwarsa? Ummi ta ya aka yi ya san lokacin da suke tashi? How ma ya zan makarantarsu? Kuma ke kika ce kar school bus ta dawo da ita, secondly tun dazu nake cewa mu taho amman baki fito ba sai da kika tabbatar ya dauketa Idan ma daukarta yayi me ye matsalarka? Shi ma yana da iko da ita kamar yadda kake da, babu ubanta a cikinku Ba shi da iko da ita Ummi, be san cinta da shanta ba be san gurin bachinta da karantunta, be san damuwarta da kukanta ba, be san farincikinta ba dan haka ba shi da wata isa ko iko akanta, a gidanmu take Under my father control, ba zan taba bari yayi iko da ita ba he's late, yana son iko da ita ya barta a daji ta wahala har ta kusa mutuwa, no one ba zan ba shi wannan damar ba Thank you Ummi ta fada masa, sai ya juyo ya kalleta. I'm sorry bana nufin bata miki rai, ki yafe min please Ummi bata ce masa komai ba ta maida hankalinsa gurin titi, hakan ya saka shi juyawa ya cigaba da tukin, suna hada ido da Waira ta madubi gaba ya dalla mata harara, sai ta yi hanzarin rufe idonta ta kife kai jikin Ummi. Ko da suka isa gidan Jabir na tsaye harabar gidan tare da Juwairiyyya, Dr Zainab kuma tana tsaye bakin entrance da alama magana suke. Maleek ya fara fita sannan ya budewa Ummi ta fito Waira ma ta fito ta kama hannun Ummi ta rike saboda tana ganin kamar Maleek dukanta zai yi. Ba ku tafi ba? Ummi ta tambaya. Dr Zainab ta kalleta tana fadin. Yanzu za su wuce, na ce masa da ma yayi cancelled flights din gobe mu tafi tare Mommy ni fa yadda kika san ina kam kaya haka nake, kara dai na tafi kawai sai kun iso Da Juwairiyyya za a tafi? Ummi ta tambaya. Juwairiyyya ta amsa matada kanta. Aa rakiya zan yi ni sai gobe zamu tafi Jabir ya kalli Waira dake tsaye kusa da Ummi tana kallonsu. Waira kawata babu sallama? Ta kalli Maleek dake tsaye ya saka hannayensa aljihu. Zan masa sallama Da kai yayi mata alama da tafi, sannan ta saki Ummi ta nufe shi da gudu ta rumgume. Maleek ya yamutsa fuska kamar wadda yayi arba da abun kazanta. Haka ake good bye ke kowa abokin rumgumarki ne what's wrong with you? Bata iya banbance halal da haram it's not her fault Cewar Mahmood yana kokarin rufe kofar falon Ummi. Jabir yayi murmushi sannan ya dagota daga jikinsa. Me zan siyo miki idan zan dawo? Wata kila ba zaka dawo ka tararda da ni ba Me yasa kika saka tunanin a ranki Waira? Idan kuma an yafe miki fa? Ta yi shiru tana kallon kasa. Maleek ya sauke ajiyar zuciya a sirrance sannan ya ce Waira shiga ciki, Jabir muje na sauke ka Ta matsa baya tana masa waving sannan ta nufi kofar falon Ummi. Allah ya kiyaye Jabir Ummi ta fada sannan ta bi bayan Waira. Jabir ya amsa da Ameen sannan ya karaso gurin Maleek yana fadin. Please don't be so harsh to her, idan abun da take ikirari ya faru abun da kake mata zai yi ta damunta Ku ne dai kuke ganin kamar ina matsa mata, amman ni na san ina daga mata kafa sosai Ya fada sannan ya bude motarsa ya shiga. Sai da Maleek da Jabir suka bar gidan tare da Juwairiyyya da zata masa sallama sannan ya Dr ta koma ciki tare da Yesmin, Mahmood kuma ya shiga tasa motar ya fice. Ummi ta raka Waira har dakinta ta dauko mata tawul din da zata daura tana tambayarta. Waira ta Ameer ya ci cake din da na hada miki Eh ya ci Da gaske? Waira ta daga mata kai tana murmushi kamar yadda Ummi ma take murmushi kamin Waira ta gusar da murmushin sakamakon amsar da ta bata. Amman da na ce ke kika yi sai ya zubar Wata kila zai dauke ni lokaci kamin Ameer ya fuskanci abun da nake nufi ya yafe min, zan jira har lokacin da zai fahimci gaskiya, har zuwa lokacin da zuciyarsa zata bude ya fahimce ni, sai ban sani ba ko rayuwa zata ba ni aron lokaci Waira ta karbi tawul din ta daura. Ummi school bag dina da ragowar cake din yana can a motarsa mu kira shi mu ce ya kawo Ummi ta girgiza mata kai. Zamu bari sai gobe da safe sai mu kira, kin ga yanzu ransa a bace yake Okay Ummi Ummi ta shafa fuskarta. Allah ya miki albarka Ameen AMEER POV. Binsu yayi da kallo sai da suka wuce sannan ya shiga motarsa ya mika hannu ya rufe motar, zuciyarsa na mugun tafasa, a yanzu ya fahimci abun da take fada cewar Maleek baya sonta, daman can ya san halin Maleek baya son mata ko yan'uwansa ne balle ita da ta fado daga sama. Ba ma abun da ya bata masa rai kamar gadarar da Maleek din yake nuna masa. Zan gyawa yaron nan zama, sai na bashi mamaki Ya juya ya kalli jakarta da cake dinta dake cikin motar, sai ya daki sitiyarin motar da karfi, yana jin haushin yadda take tsoron Maleek. Ni na jefaki a wannan halin, zan rabaki da gidan nan soon Ya fada daidai lokacin da ya faka motarsa a harabar asibitin Hikima domin hankalinsa ba zai kwanta ba idan be je ya duba tsohuwar da ya kade ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya mika hannunsa ya dauko jakar makarantar ya bude ya ciro littafanta yana dubawa, da textbook ya fara kamin ya duba notebook, ba laifi tana rubutu yadda xa a fahimta even though bata gwane sosai ba rubutun yan p rimary 4 take yi. Yana dubawa maganar da suka yi a dazun tana dawo masa, tausayinta ya cika masa zuciya. And she's right shi be rasa gata ba, kuma matar da take ikirarin ita mahaifiyarsa ce tana dakun zuwan ranar da zai karbi hakan, and he would ko dan abun da ta fada masa cewar Ummi tana dauke da cutar Leukemia, ba sosai ya san komai akan cutar ba, amman ya san cuta ce mai hatsari dake farautar rayuwar an adam. Ya aje mika hannuna ya dauko box din cake din da ta bari ya dauka ya bude, kallon shape din cake din yake yana, kamin ya fi karfin zuciyarsa ya kai hannu ya dauki spoon din dake gefe ya gutsiri cake din ya ci. Da hannu yafi dadi mu bama ci da spoon Maganar Waira ta fado, masa sai ya aje spoon din a muhallinsa ya zari tissue ya saka ya dauki cake din yana ci. Sai da ya ci kusan rabi sannan ya rufe mata saura ya saka mata a jakarta ya aje jakar gefe ya kwanta jikin kujerar yana sauke ajiyar zuciya, duk wata magana da Waira ta yi masa sai da ta dawo masa a lokacin, ta fada masa kusan abun da mahaifinsa Mr Bashir ya fada masa amman be fahimta ba sai a yanzu. Bude motar yayi ya fito nufi cikin asibitin, ya isa Emergency ya nufi dakin da aka ya barta sai ya tarar wasu ne ba ita ba. Nurses din dake gurin ya tambaya ta fada masa cewar an canja mata daki. Wani ta saka yayi masa jagora har dakin da aka maidata, Mutumen na nuna masa dakin ya juya yayi tafiyarsa. Ameer ya kalli room number din dakin sannan ya murda kofar ya shiga, first abun da ya fara arba da shi is Humairah tana tsaye gurin kan tsohuwar idonta yayi ja har ya kumbura, kana ganinta kasan ba kadan ta yi kuka ba. Tsayawa yayi yana kallonta da mamaki ita ma kallon mamaki take masa, Mamarta kuma ta mike tsaye tana kallonsa domin ta gane shi ne mai gidan yarta Humairah ta rike fuskarsa tun a ganin farko da ta yi masa, shi kam ba dan ganin Humairah ba da ba zai iya shaidar fuskokinsu ba daga ita uwar har kakar. Me kik.... Kakarki ce? Ta daga masa kai. Kai ka kadeta? It wasn't intentionally, zan wuce ne ita kuma zata je karbo sadaka Ya karasa gurin gadon. Ya jikinta? Da sauki amman har yanzu bata dawo hayyacinta ba Ba zata dawo hayyacinta da wuri ba, tana bukatar lokaci Ina wuni ranka ya dade Mahaifiyarta ta gaishe shi kamar zata risina. Lafiya kalau Ya amsa yana jin wani iri. Sannan ya kalli Humairah ya ce. Za'ayi muku komai a nan, zan tafi gida yanzu anjima kadan za a kawo muku abinci tare da kudi ku siye wani abun, kuma idan