← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 165

Sashe 136

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

POV. Peach Suite ne jikinsa sai farin gilashin da ya kara masa kyau da gwarjini. Gilashin ya cire bayan ya gama waya da Nuwaira ya aje wayar ya fisge kansa ya kwanta jikin kujerar dake juyawa ya cika bakinsa da iska ya busar. So this is me.. Furtawa yayi yana murmushi da mamakin kansa yadda ya zama wani iri saboda soyayya, har yake jin kamar ba zai iya kyale Nuwaira ba ko bayan tafiyarta, yana jin zai saci kafa ya bita ne ko da kuwa kowa be sani ba, domin ya fi jin kaunarta a yanzu fiye da lokacin da take kusa da shi. Mikewa yayi tsaye ya saka hannunsa daya aljihu dayan kuma yana rike da wayarsa ya nufi kofar fita office din yana dialing number Maleek. Wannan karon voice call ba kamar dazun da yayi video ba, shi ma saboda ya ganshi online ne kuma soyayya ta hana shi girman kai ta hana shi danne zuciyarsa daga duk wani abun da yake ji akan Maleek har ya kada kansa ya kira shi, sai dai be bari Maleek yace komai ba ya fada masa zai gaisa da Nuwaira ne. Tsaye yayi a ta inda yake iya hango kasan ma'aikatan dake ya hada hada a kamfanin yana sauraren wayar dake ringing, ta yi ringing ta katse Maleek be dauka ba ya sake kira be daga ba, hakan ya saka yanke shawarar aika masa sako. Pick the call Bata kusa Maleek ya maido masa da reply, sai ya sake aika masa sako. Da kai nake son magana Yana aika sakon ya sake kira, Maleek yayi picking aka rasa wanda zai fara magana a cikinsu, har sai da Maleek ya gaji ya ce. Zan aje wayar i just call na yi magana da kai akan Nuwaira, i know baka ra'ayina but please karka duba wannan, ita ma kanta ba zaka son ganinta a cikin damuwa ba, kuma ba zaka so ganin ta shiga wani yanayi bayan baka nan ba Ban fahimce ka ba Ban sani ba ko ta fada mana, ni dai ta fada min cewar idan ta koma kasheta za'ayi saboda abubuwan da ake ganin ta aikata, a yanzu kuma ka ga ta samu kari, kamar sanja shiga daga wadda ta saba zuwa ya mu, ga kuma addini uwa uba, wannan kadai ya isa ya saka su cutar da ita, kuma ina tunanin zata zubar da duk wani abu da ya danganci tsafi a yanzu saboda ta karbi addinin musulumci, wata kila saboda wannan ma kawai ba za su kyale ta ba, tana fada garinsu ba a karba bako amman please karka barta ta shiga garin ita kadai ya kamata ku shiga tare da ita domin tabbatar da lafiyarta, kuma ka yi magana da su ka nema mata yafiyarsu, ka musu bayanin yadda za su gansu su barta ta yi addininta, na manta ban siya mata littafin addu'ar ba please ka siya mata kamin ku tafi, na san bata iya karatun arabic ba zai fi kyau ka siya mata wanda zata karanta da tarjamal hausa ko turanci, make sure she's safe please Maleek be ce komai ba ya aje wayar bayan Ameer ya gama rattaba masa abubuwan da zai yi Ameer ya roki ne kawai saboda yana ganin wannan ce kadai mafitar da yake da ita, ko da Maleek ba zai yi ba ya dai fada masa idan kuma yana da niya ya tunatar da shi a yanzu. Gabansa na bugawa da karfi ya sauke wayar Nuwaira ce kawai a mind dinsa a yanzu da take kusantar garinsu ne yake tuna abubuwan da ta fada masa, ya san ko da garinsu ba haka yake ba zata samu kalubale idan ta koma musu da sabon addinin balle kuma wani gari irin garinsu zai yi wahala su iya fahimtarta har su daga mata kafa, sai a yanzu yake jin me yasa ma ya barta ta tafi? Me yasa be dange ya hana tafiyar ba? And babu wanda yayi tunani irin nasa? Ko dai yace Maleek ya dawo da ita? Anya zai yarda ma ya dawo da ita din idan ya fada? Ko dai ya kira Ummi ya fada mata? Be kama yanke shawara ba wata zuciyarta ta ce Ameer relax ko da ta zauna dole wata rana zata tafi, kuma babu fa'idar zaman a nan bayan kuma zaka yi ta cutuwa da kaunarta ba, idan kana kaunarta ka bi bayanta bayan tafiyarta sai ka dawo da ita da Hujja a nan ne zaka nuna tsantsar kaunar da kake mata kuma ta san kaunar gaskiya ce Ya amince da shawarar da zuciyarsa ta bashi, da haka ya samu sa'ida har ya koma office din ya hada abubuwan da zai hada ya fita. *** *** Misalin karfe tara na dare Maleek yayi knocking din kofar dakin Nuwaira yana dauke hannunsa tana bude masa, carpet dinta sallah ta ya gani a bakin kofar sai dakin hawaye shakab a fuskarta. Shigowa zaka yi? Be ce mata komai ba ya saka hannu ya dauke carpet din ya shigo dakin ya karasa gurin wata kujera daya dake cikin dakin ya zauna. Zo na nuna miki wani abu Ta isa inda ta risina kasa sai ya bude littafin addu'ar ta turanci ya mika mata. Karanta nan na ji Ta kalleshi sannan ta karanta bakin abun da zata iya ta kalleshi domin bata fahimta. Addu'a ne tsare yinsu a kullum Ya tsaye sai ita ma ta mike tsaye. Ya Maleek ba zan iya kwana a nan ni kadai ba ai, kuma dazun na fita ban gane dakinka ba na dawo Ya juyo ya kalleta. Toh me zaki yi a dakina Kwana mana ina jin tsoro a nan No ba haramun ne kwana daki daya dake musulunci ya hana Amman ai ina jin tsoro Haka zaki yi hakuri, kuma nan akwai tsaro babu wanda zai tana ki Ganin zai fita ya barta ya saka ta ce. Zaka kira min Ameer? Please irin yadda ka kira shi dazun? Dazun ma shi ya kira ba ni na kira shi ba, kuma yanzu yayi bachi Kawai ta bare masa baki ta fashe da kuka kamar karamar yarinya, da mamaki ya juyo ya kalleta ya rasa me zai ce mata, shi ma tashi damuwar ta isheshi zata kara masa da wata. Me aka yi? Ba zaka kira min Ameer ba, daman Sulem ya ce baka min kirki shi ma ka masa rashin kirki, raina ya bace da ka yi fada da shi Munafurci yayi min kenan? Ya ce wani abu na yi miki? So yake ki tsane ni kenan? I already did... Ta fara fashewa da kuka, dauke kai yayi ya fice daga dakin sai ya biyo shi ta fito tana kuka, yana yi yana juyowa ya kalleta ganin da gaske kukan take kuma binsa take ya saka shi tsayawa. Me kike so wai? Karki tara min mutane nan fa Ba zan iya kwana ni kadai ba, idan na tafi dakinka ba sai ka kwanta saman gado na kwanta kasa ba? Ba zan yi hakan ba, ki koma dakinki Ya fada mata cikin tsawa har sai da ta sha jinin jikinta, ya juya ya fara tafiya kenan Ameer ya kira shi sai ya juyo ya aje mata wayar a kasa. Gashi nan ya kiraki Ta karasa da sauri ta dauki wayar sai dai bata ganin komai sai fuskarta. Ni ce ai babu wanda ya kira Ki taba maballi green Yana fada yana tafiya, sai ta taba maballin sai ga fuskar Ameer ta fito yana ganin Nuwaira ce sai ya saki fuska yayi murmushi. How are you? Me kike yi ma kuka? Na fadawa Ya Maleek ba zan iya kwana ni kadai ba, yace shi ba zai kwana da ni dakinsa ba, na ce ya kira min kai be yi ba kuma ina jin tsoro Babu abun da zai same ki just ki yi addu'a, tafi ki kwanta yanzu Ni kadai? Ba gani ba? Zan jira sai kin yi bachi kamin kin kwanta zan koya miki addu'ar tsari Ya Maleek ya kawo min wani littafi ma na addu'a wai Yayi kyau, kin ga zaki iya kenan Haka yayi ta janta ta hira har ta koma dakin, ya tambayeta an kawo mata abinci ta ce an kawo mata na rana da yamma ma an kawo mata haka after Magariba ma an kawo mata. Wayar ya saka ta aje gurin kan gadonta ta rufe dakin yana hira da ita ta shiga bandaki ta yi fitsari ta fito ta hau saman gadon ta kwanta sai ya saka ta dauko littafi ta bude tana nuna masa ya saka ta karanta inda ya ji ta yi ba daidai ba sai ya gyara mata yana karantawa tana binsa har ta karanta addu'ar kwanciya bachi ta kwana tana kallonsa gaba daya ya gama burgeta domin jin take kamar yana kusa da ita ne. Karka kashe wayar Ameer ko da na yi bachi Okay zan yi ta kallonki har ki farka hakan yayi miki? Ta daga masa kai. Ameer i didn't hate you Yayi mata murmushi daman ya san bata tsane shi ba, kawai dai bata mishi irin son da yake mata ne. I know, ki yi ta addu'ar da na koya miki har bachi ya dauke ki Okay idan na koma can gobe zan yi missing dinku all Ina fatar dai wani abun da zai same ki ba, kuma ba zaki jefar da addininki ba Kamin ta bashi amsa har bachi yayi gaba da ita, daman ga gajiyar mota ga kuma na kukan da ta yi ta rusa dazun. Kallonta yake yana murmushi bachi take amman hakan be rage komai daga kyauta ba. Ya fada mata zai yi gadinta kuma yayi sau biyu tana farkawa cikin dare sai ta ganshi idonsa biyu yana kallonta. Ba zaka yi bachi ba Indai zan yi gadinki ki yi naki bachin cikin natsuwa da kwanciyar hankali shi ne farinciki ne, zan yi nawa da rana koma ki kwanta yanzu sallah nafila zan yi Minene Sallah nafila kuma? Dare amman hakan be hana shi bude mata wani sashe na karatun Nafila da fa'idarta ba, sannan ya tashi ya shiga bandaki yayi alwala a lokacin duk tana kallonsa har ya fara sallah sannan bachi ya sake yin gaba da ita. Can cikin bachi tana ji yana kiran sunanta a hankali
Chapter 136 · 0% Book details