← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 165

Sashe 81

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

ne, dan haka ta dauko ta dawo dinning ta aje cup din ta bude sugar ta saka fiye da cube din da Ummi take saka mata sannan ta dauki daya ta kai baki tana tsotsawa, daki-daki ta bi har ta hada wa kanta tea ta dauko ta fito dinning area din ta dawo falo ta zauna, tana busawa saboda ya rage zafi. Idan Ummi ta dawo zamu ce ta kira Sulem ko? Baby rabbit dinta take tambaya da yarenta tana shafa kansa. Zill na baka labari? A can garin mu ina da bera da yawa a dakina, kuma ina da zakaru, kuma ina da Eid, na san yanzu ya manta ni, ko kuma yana jin haushin guduwa da na yi shiyasa ba zai zo ba na yi kewarshi sosai Shi dai zomon ya zauna a jikimta shiru sai saurarenta yake kamar fahimtar abun da take fada. Yanzu ni da kai Ummi ce mamanmu ko? Ko kuma ni ce mamanka kai ni kuma Ummi ce mamata Ta dauki tea zata kai baki sai ta kalli stairs Maleek dake tsaye rike da key ta gani tsaye yana kallonta. Babu annuri a fuskarta ba kuma fushi yake ba, rashin walwala ne irin ba wanda ke cikin tsananin damuwa domin idanuwanta sun nuna haka as well as fuskarsa. Aje cup din ta yi ta mike tsaye tana kallonsa a zatonta fada zai mata saboda fitar da Jabir yayi da ita, a kokarin ta na kare kanta ta duka ta dauki ledarta da cup din ta nufi inda ta saba boya ta zauna tana sauraren ta ji ko binyo ta zai yi. Shi kam bata ita yake ba, a zahiri ita yake kallo amman a badini tunaninsa da hankalinsa suna gurin damuwarsa ne. Ganin be wuce ba ya saka ta sake lekowa sai ta ganshi tsaye har yanzu inda ta tashi yake kallo sai dai wannan karon ta ga abin da ya daga mata hankali, hawaye ta gani a idonsa, saurin boyewa ta yi gabanta ba faduwa. Tana jin saukowarsa ta takure guri daya ta yi zaton gurinta zai zo, sai ta ji shuru hakan ya saka ta sake lekawa ta ga baya gurin, fitowa ta yi gaba daya, ganinsa ta yi zaune akan kujera ya cije ya cije baki yana kallon wani gurin dabam. Ya Maleek Yesmin ta kira shi be amsa mata ba be kuma juyo ba, sai yayi saurin tashi ya fice daga falon ba tare da ya bari ta ga hawayensa ba. Waira ta kalleta ba wani sabo ta yi da ita ba dan haka bata ce mata komai ba ta koma ta zauna a inda ta saba boya ta dauki tea ta rike da hannu biyu kamar yadda ta saba yi ta shanye duka. Sannan ta sake fasa wata ledar chocolate din ta fara ci tana yi tana lashe hannu, sai da ta gama sannan ta fito rike da cup din ta nufi kitchen jin motsi ya saka ta boye sai ta fara lekawa ta ga Yesmin ce ke kokarin kunna gas sannan ta shiga ta aje cup din ta wanke hannunta, bata san rike sunan Yesmin ba, dan haka ya saka ta matsa kusa da ita ta taba rigarta. Zaki kira min Sulem Waye kuma Sulem? Wanda ya zo, ko ki kira Ummi Ummi tana dakinta, shi kuma Sulem ban san shi ba Tana jin haka ta yi saurin fita kitchen din ta nufi stairs da gudu ta fada dakin Ummi sai ta tarar da Ummi a bathroom. Ummi... Ummi Ta kira sunanta daga bathroom din Ummi ta amsa muryarta a shake. Na'am Baby Waira gani na fitowa Gurin kofar Bathroom din Waira taje ta tsaya har sai da Ummi ta fito, sai ta rumgume ta tana murnar ganinta ita dai idan Ummi bata cikin gidan bata da natsuwa da kwanciyar hankali duk sai ta ji kamar bata da kowa a duniya ta zama marainiya. Oyoyo Yata i miss you Ummi baki tafi da ni ba Waira ta fada tana kallon idonta dake kumbure har bata oya bude da kyau. Waira ko dan kin ji ina ce miki Baby? Ke fa ba yar karamar yarinya ba ce da zan rika yawo da ke, daman can ai ba fita nake da ke ba, dan haka ki daina cewar ma ban tafi dake ba Ummi idonki ya dahu Ummi ta yi dariya tana murza idon. Ciwo yake Kuma Ha Maleek yayi kuka A ina kika gani? Maybe saboda Nimra bata da lafiya ne, kin san tana asibiti ko? Ta daga kai, Ummi ta sake ta ta nufi wayarta dake cikin jaka tana ringing, bude jakar ta yi ta dauko wayar number one of ma su kula da gate din ta ne yake kiranta. Wa'alaikussalam Hajiya an wuni lafiya? Lafiya kalau Na kira wayar Alhaji be daga ba shiyasa na kira wayarki, wani ne ya zo da mota yana son ya shigo ciki, na ce wa yake son ganin wai Zahra Waye shi? Bari na tambaye sunanshi Tana jin lokacin da yake ta tambayarsa ya sunansa amman yaki yayi magana. Musa bar shi ya shigo na gane shi Toh Hajiya Ta aje wayar ta nufo falo Waira ta biyo bayanta. Yesmin dake zaune ta dago tana kallon Ummi wadda ta zauna kan kujera idonta na kan kofar falon, juyawa Yesmin ta yi ta kalli kofar sannan ta juyo ta kalleta. Ummi lafiya Ummi ta daga mata hannu alamar ta dakata. Da wani irin karfi aka murda kofar falon aka turota, daga Ummi har Yesmin da Waira sai da suka mike tsaye suna kallon Ameer da ya shigo falon fuska babu annuri, kai tsaye ya nufo inda Ummi take domin ba kallo kayan alatu suka kawo shi ba balle ya tsaya bata lokaci. Tsaye yayi a gabanta kamar without any rest yana mata wani irin kallo da ya fi kama da tsana. Waira ta saki baki tana kallon Ameer da mugun mamaki shi kam ko ganinta be yi ba domin baya ganin kowa a falon sai Ummi kadai daman zuwan nata ne. Yarfar da hannu ta fara yi tana son ta tuna sunansa ta kasa amman tabbas ta gane shi, abun ka da mai son mutane ta ga wanda ta sani sai jin yayi an shiga tsakanin shi da Ummi an rumgumeshi da karfi. Yana kokarin saka hannu ya ture kowaye ta dago kai shi kuma ya sauke nasa kan kasa dan ganin wanda ya yi masa wannan kasadar. Murmushi take masa mai sauti hakoranta a washe, lokaci daya ya gane wacece ita, ya tuna inda ya fara ganinta, alakarta da gidan ta tuna masa cewar ita ce yarinyar da ya saka a motar Nimra, daman Nimra ta fada masa yarinyar tana gidansu, a yanzu ya gane duk ganin da yake mata a gidan take. Yesmin ta fisgeta ta jefar da karfi kan kujera. Baki da hankali daga ganin mutum zaki tashi ki rumgume shi? I know him i know him Idan kika taba shi sai na kusa kasheki. Kai.. Ya zaka shigo cikin falo ka nufi uwar masu gida kai tsaye ko baka da hankali Ta fada tana kallonsa kamar yadda yake kallonta cikin bacin rai, shigarsa da yanayinsa be yi mata kama da mahaukaci ba, balle ta ji tsoronsa kama yayi mata da marasa tarbiya yan tijara. Yesmin stay out of this please, Ameer me kake so? Ummi ta fada sai ya dawo da dubansa gareta. Shaida abun da zai saka na yarda da abun da kika fada Ribar nawa zan ci idan na yi maka karya? Na san wannan abun zai iya kai ni gidan yari idan har karya ne, to akan me zan yi haka? Ina da yaya mata kuma Allah ya ba ni mata idan ba ni da hujja ba zan yi haka ba, idan aka auna jinina da naka na tabbatar results daya zai ba da, ba dukiyar Mr Bashir nake kwadayi ba nima Allah ya rufa min asirin da zan iya yin komai... Amman jira ni ina zuwa Ta nufi stairs da sauri dakinta ta fara shiga ta bude wardrobe dinta, sai da ta fara kokarin sauke akwatin sannan ta tuna Maleek ya dauki jakar, da sauri ta fito dakinta ta shiga dakin Maleek akan gadonsa ta tararda jakar wasu takardun a watse wasu kuma be taba su ba, wadanda be taba din ba ta dauka tana dubawa har ta kai ga evidence din da take son nunawa Ameer ya sauko da sauri ta iso inda yake ta mika masa. Kallon envelop din yayi ya kasa mika hannu ya karba, kamar wanda aka cewa makomarsa ce a ciki. Shaidata tana nan, kuma ka tambaye duk abun da kake so zan amsa maka... Cikin nauyin jiki tana zuciya ya karba ya bude, takardar yarjejeniya ya fara cin karo da ita kalar wadda Hajiya Jamila ta bashi, abun da ke rubuce a can shi ne a rubuce a nan babu banbanci har kwanan wata. Daga kasan takardar kuma hoton mahaifinsa ne da ya kara gasgata masa cewar tabbas shi ba an Mr Bashir ba ne. Domin kamanin dake jikinsa da fuskarsa su ne a jikin hoton banbancin wannan hoto ne da ya dade shi kuma yana a tsaye ne a zahiri. Zubewa yayi kasa guiyoyinsa ya fashe da kuka ya rumgume hoton a kirjinsa. Me yasa zaki yi haka? Me na yi miki? Dukawa ta yi tana kuka Baka min komai ba Ameer, ban aikata hakan saboda son zuciya ba Ta mika hannu zata taba shi sai ya daka mata tsawa da zai da ta zabura. Don't touch me I won't i won't Ta rike hannayenta da sauri. I'm sorry Ameer na san ban kyauta ba, amman ban aikata hakan da nufin bana son ka ba dole ce ta saka Da kina so na, da baki siyar da ni ba tun farko, kuma da baki bari na rayu a gurin wani da yake amsa sunan Ubana ba, da soyayyaa bata barki kin kai wannan lokacin ba tare da ni a kusa da ke ba Wallahi soyayyar ka bata bar ni na samu farinciki da kwanciyar hankali ba, a kullum da kai nake wuni na kwana a zuciya, ina tunani a wane hali dana yake ciki Ni ba anki ba ne, you have never been my mother and you
Chapter 81 · 0% Book details