Sashe 56
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
watsar da tarbiyar gidansu ta dauki wata bakar dabi'a? Tun yaushe take mata karyar fita zuwa wani gurin tana zuwa nan? Gurin wa take zuwa? Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un Ta furta tana saka hannu ta dafe zuciyarta. Allah ka gani na iyawar iyawata, na ba su tarbiya daidai gwargwadon yadda zan iya, Allah ka kama min, na shiga uku ni Zahra, farko Ameer ta shi ta wuce, daga baya Maleek shi ma ya fara samun sauki a yanzu, sai kuma Nimra, bayan ita kuma sai wa Ta lumshe ido hawaye na sauko mata, son sanin me take aikatawa kuma da wa take aikatawa ya saka ta share hawayenta ta bude motar ta sauko, ta taka da kafa har zuwa inda gidan yake da tunani kala kala. Ta dade a tsaye sannan ta kai hannu ta kwankwasa gate din gidan, babu jimawa mutunen da ya budewa Nimra ya bude mata. Dan Allah tambaya nake ko masu gidan na ciki? Ta kalli Ummi sama da kasa, yana ganinta ya san ba irin masu zuwa manyan gidaje roko ko neman wani abu ba ne domin hannunta ma rike yake da key mota. Aa baya nan lafiya kike nemansa? Lafiya kalau, na yi magana da shi ne yace na zo na same shi a nan To gaskiya be iso ba, tukuna amman dai yana kan hanya tun da kika ga wannan matar ta zo Ummi ta hade yawun bakinta daker. Ko zan iya shiga na jira shi a ciki? Aa gaskiya, saboda be yarda na bar kowa ya shiga gidan nan ba Amman yanzu na ga wata ta shiga Eh to ita ya san da zamanta, shi ya bada umarni da zarar ta zo na bude mata ta shiga Amman dan Allah ta dade tana zuwa nan ne? Wannan kuma wani abu ne da be kamata ki ji shi a bakina ba, domin be kamata na fadi wani abun da ya shafi gidan a gurin bakuwar fuska ba, dan Allah ki jira shi ya zo ko kuma ki kira shi Haka ne, na bar wayata a mota bari na dauko na kira shi Ta juya ta nufi gurin motarta hawaye masu zafi na sauko mata, tana barin gurin mai gadin ya juya ya koma ciki ya dauki tasa wayar ya kira Ameer ya sanar masa abun da ya faru. Ummi na shiga motar ta dafe saka hannu biyu ta dafe kanta ta fashe da kuka.... AMEER POV. Oh Really Kasan ai ba zan iya ce maka No ba, amman dai ka yi sauri domin ba zan dade ba, kasan dole na tafi gurin saloon din kar karyar ta yi yawa Yayi wani shegen murmushi yana lila da kujerar office din. Alright gani nan zuwa Ya aje wayar ya mike tsaye ya dauki keys dinsa ya fice daga Office din, sa sassafar ya sauko ya fito waje da tafiyarsa irin ta zarumai da basa jin wahalar komai kamar yadda basa da nauyin kowa akansu. Motarsa ya shiga ya murza key ya fita daga Kamfanin tana tuki a hankali, ransa be bace ba sai da ya kai gurin traffic, wani guntun tsaki yaja ya danna horn da karfi yana jin kamar ace zai iya taka motocin dake gabansa ya wuce, traffic na aya daga cikin abun da ya tsana a hanya. Ta cikin bakin gilashin motarsa ya hango wata kyakkyawar yarinya take cikin School Bus, tana sanye da uniform ta rumgume jakarta ta Teddy kana ganinta kasan a tsorace take, ta yi parking din gashin kanta baya, fara ce sol bw tabbatar da hakan ba sai da ya sauke gilashin motarsa yana kallonta, ji yayi kamar ya santa ko kuma ya taba ganin wata mai kama da ita a wani gurin sai dai ba zai iya tunawa ba. Amman yarinyar nan kina da masifar kyau Ya fada yana shafa kansa kallonta yake sosai, ita kam bata ma san yana yi ba domin hankalinta yana gurin motocin dake gaban bus dinsu, sai da aka saki green light sannan yaja motarsa zuwa hanyar gidansa yana waigen School Bus din da ta auki wata hanyar dabam. Wayarsa ta yi ringing ya dago wayar ya duba. Hello Ranka ya dade wata mata ce ta zo nemanka.... Ta mamaki ya gama sauraren kiran sannan ya ce. Ka je ka fada mata ba zan dawo yanzu ba Mamaki ya cika shi, domin shi dai be yi da wani za a zo nemansa a gidan ba, gidan ma ba Nimra ba be taba kawo kowa a gidan ba, bw ya jin ko Daddy ya san yana zuwa gidan a yanzu balle kuma wani da be fadawa ba. Ya sake daukar wayarsa ya kira Nimra ya tambayeta ko akwai wanda take tsamanin zuwansa ko kuma ya biyo bayanta. Tana jin haka sai hankalinta ya tashi. Aa amman wa suka ce maka? Ban tambaya ba, na ce ya fada mata ba zan dawo ba, zan tsaya daga nesa na ga ko wacece Nimra ta kashe wayar da sauri ta mike tsaye ta fita daga dakin da take kwance ta fito harabar gidan kamar mahaukaciya. Ta nufi gurin mai gadin tana masa tambayoyi. Dan Allah wacce ta zo ta fada maka wace ce ita? Aa bata fada min ba Dan Allah fita ka tambaya wacece ita kuma wa za a ce masa idan ya dawo Ba musu mai gadin ta fita ya leka waje har sai da ya hango inda Ummi ta aje motarta ya taka ya isa gurin yayi knocking din glass din motar ta bude masa idonta har ya kumbura tsabar kukan da take a motar, jiki ya mutu domin ta riga ta san mai afkuwa ta afku. Hajiya na kira shi yace ba yanzu zai dawo ba, amman wa za'a ce masa idan ya zo? Zaka iya kiran min yarinyar da take cikin gidan nan? Gaskiya ba zai yiyu ba To dan Allah zaka iya ba ni aron wayarka? Saboda tawa wayar tana gida na manta Sai da ya dan dade yana tunani sannan ya ciro wayar ya mika mata, ta karba ta saka number Nimra, Nimra dake tsaye jikin gate tana jiran dawowar mai gadi wayarta ta fara ringing sai ta ki ta yi picking har kiran ya tsinke, sai da aka sake kira na biyu sannan ta daga. Hello Nimra kina ina? Jin muryar Ummi ya haifar mata da sarawar kai, ta juya ta kalli gidan. Ina gurin Saloon Ummi Saloon din kenan a cikin gidan wani? Yaushe kika lalata kanki Nimra? Me muka miki da zaki watsa mana kasa a ido? Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un ki fito yanzu nan ina jiranki a waje Kalaman da zata hada ta tari furucin Ummi sai ta rasa har Ummi ta yanke wayar, kuma ta kasa fita ta kasa komawa ta kasa yin komai sai gumi take tana hawaye kamin ya duka a gurin ta fara kuka... Khadeeja Candy Copyright 2023 Ji ta yi kamar hanjinta za su fito a lokacin da wayarta ta sake yin ringing, wani irin rawa jikinta yake kamar mazari, sai dai ganin Number Ameer ya saka ta yi saurin dauka. Hello Ameer Ummi ce? Wace Ummi? Na santa ne? Mahaifiyarmu Ta sake fada cikin kuka. Oh Really wow i like it What do you mean you like it? Na kusa karaso bari na zo sai mu yi magana No no no karka zo kar ta ganka tana waje tana jiran na fita Ya yanke wayar ba tare da ya sake ce mata komai ba, tana kokarin kiransa Mai gadin ya dawo min sai ta yi baya da sauri a zatonta Ummi ce ta shigo ciki. Ina take? Ta wuce Ta juya baya tana dora hannunta a saman kai. Na shiga uku na lalace? Waya fada Ummi ina zuwa nan? Toh Wallahi ban sani ba Ya amsa kamar da shi take magana, sai ta juyo ta daka matsa tsawa. Kai dan Allah ba da kai nake ba, ka rufe min shegen bakinka, ai duk laifinka ne Ya tabe baki ya koma gurin zamansa yana fadin Allah ya kara daman ina bakincikin abun da kuke aikatawa, zamani ya lalace yara sai fadarewa suke Da gudu ta shiga falon ta zauna saman kujera tana kiran wayar Ameer dake ta ringing ya ki ya daga. Ka daga Ameer ka daga Can kuma ta yanke kiran tunawa da ta yi da Ummi ta tafi, kusan tun da take a rayuwarta bata taba shiga tashin hankali irin wannan ba, bata saba yi na Ummi karya ba a lokacin da ta koyi yin karyar kuma ba ta yi zaton asirinta zai tonu ta wannan hanyar mafi muni ba. Shigowar Ameer ya saka ta mike tsaye da sauri ta nufi inda yake shi ma ya nufota. Ya aka yi haka ta faru? Ban sani ba, wata kila wani ya fada ma mata ne, ko kuma ya kawo ta nan Na so na tararda da ita da sai na yi mata bayani ko yanzu zamu tafi gidan tare zan fada mata komai Wane irin bayani kuma? Ameer are you okay? Zan yi magana da ita tukuna Ya kama hannunta. Nimra ina fatar kin shiryawa wannan, daman soyayya dole akwai kalubale balle kuma irin ta mu da muka boye, amman ni I'm ever ready to marry you, ban san miyasa iyayenki suka tsane ni ba, but i trust you na san zaki iya shiga ko wane irin hali saboda ki ga soyayyarmu ta daure haka ne? Ta daga mishi kai. Good kamar yadda zan iya aikata komai akanki, and ina tunanin wannan dama ce a gareki da zaki bayyana musu wanda kike so, kuma ki fada musu cewar ba zaki auri kowa ba sai wanda zuciyarki take so, matukar suna kaunarki na tabbatar za su bar mu mu auri junanmu, kuma ki daina wannan kukan haka ba wani abun tashin hankali ba ne, zamani ya zo da an daina abubuwa da yawa, yanzu an waye ba kamar da ba ne zuwan dakin saurayi ba wani abun ba ne, kawai dai boyewar ne ina tunanin zai zama laifi a gurinsu, shi ma kuma laifinki ne domin tuntuni na yi ta neman ki ba ni damar bayyana kaina a matsayin masoyinki kika ki, i hope ba zasu ce za su raba ni da ke ba Nimra, saboda zan iya mutuwa idan iyayenki suka