Sashe 63
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta fito ta saka wando da riga ta sauko kasa bata samu kowa a falon ba sai motsin da take ji a kitchen, hakan ya saka ta nufi kitchen kai tsaye ta leka sai ga ta samu Ummi a tsaye. Ummi ta canja Ta fada tana shafa tufafin jikinta, Ummi ta juyo ta kalleta tana jin kamar zuciyarta zata tsage. Ummi. Meyasa Ummi ba fada fadawa Abiey bata da lafiya? Lafiyata kalau tafi falo ki zauna zan hada miki tea yanzu ke da Nimra A maimakon ta juya ta fita kamar yadda Ummi ta bukata sai ta rugo da gudu ta rumgume Ummi ta fashe da kuka. Waira tana son Ummi Ummi ta shafa bayanta.. Ya isa, bana son jin kuka kowa a yanzu je ki zauna zan kawo miki tea kamin mai lessons dinki ya zo kin ji? Ni ma ina sonki Ba dan ta so ba ta bar jikin Ummi ta fito falo ta zauna ta takure guri daya kamar bakuwa, tana kallon Maleek ya shigo ya haura sama zuwa dakin Nimra, aka sake bude kofar Dr ta shigo tare da Jabir hankalinta a tashe. Ina Zahra take? Ummi na jin muryar Dr Zainab ta fito daga kitchen din ta nufota ta rumgume tana jin wani sanyi sanyi a ranta. Jabir kuma ya nufi Waira dake ta sharar kwalla. Waya taba ki? Ummi zata mutu... Yayi saurin rufe mata baki, a zatonsa kuka da ta ga Ummi tana yi ne ya saka ta tsorata har take furta haka. Subhanallah, ki dina fadar hakan ba abubuwa ne akwai suka faru kuma komai zai wuce kinji? Ta girgiza kai ta fara magana da karfi cikin kuka. Ummi tana kuka, Ummi tana da ciwo Ummi zata mutu, Ummi ba zata fada ba, Ummi tana son mijin Nimra, Ummi ta haifi Mijin Nimra Ta ta saka dayan hannunta ta share hawayen fahimci abun da take nufi bata iya fadar da kyau ba hakan ya saka ta kalli Ummi dake kallonta ta ce Ummi talk, tell them ki fada musu Kusan kowa kallonta yake daga Maleek dake saukowa rike da syringe a hannunsa har Mahmood da ya turo kofar falon ya shigo da zimmar sanar mata mai lessons dinta ya zo, balle kuma Ummi data tsorota da abun da Waira take fada, Jabir kuma be fahimci zancen da kyau ba as well as Maleek sai dai kalmar Ummi zata mutu ta daga musu hankali, Dr Zainab ma bata fahimcin yaren nata ba. Me take fada ne? Ni ban fahimta ba Jabir ya tambaya yana kallon Ummi. Ummi tana da ciwo mai mutuwa Ummi zata mutu Waira tana son Ummi Ta sake fada tare da fashewa da wani irin kuka mai karfi, a wannan karon Mahmood ya fahimcin inda ta dosa, Maleek kuma ya shiga hudu sai idonsa suna akan mahaifiyarsa. Waira ki tafi dakinki yanzu nan? Ummi ta fada, sai Mahmood yayi karaf ya ce. Mai lessons dinta ya zo yanzu nan Okay wuce ki dauko jakarki ki tafi gurin lessons dinki Ta sauka daga kan couch din ta nufi upstarts haka ta raba gefen Maleek da ya gagara saukowa ta wuce dakinta ta dauko jakarta ta sauko ta fice daga falon. Me yarinyar na yi take fada ne Zahra? Dr Zainab ta tambaya. Shirmenta ne mana, da ma kin tafi gurin Abiey kun tattauna zai fi Maleek ya sauko ya nufi kofa ya fice daga zuwa gurin motarsa ya bude ya dauko wata ledar sannan ya dawo ciki ya haura zuwa dakin Nimra zuciyarsa da tunani kala kala. Dr Zainab ta nufi hanyar da zata sadata da bangaren Abiey, Jabir da Mahmood kuma suka zauna a falon Mahmood na labarta masa abun da ya faru a game da Nimra da kuma rashin mutun Ameer da ya sani. Ummi kuma ta koma kitchen din ta cigaba da abun da take tana tunanin inda Waira ta samu wannan labarin, hausawa suka ce sawun giwa ya batar da na rakumi, gaba daya sai tunaninta ya koma gurin Waira. WAIRA POV. A inda suka saba zama su yi lessons ta zauna akan kujerar da aka siya mata da karamin tebur din da take dora littafan karatunta, dattijon da zai yi shekara 50 yana ta zuba mata karatu amman hankalinta baya guri, tunaninta ya tafi akan dalilin Ummi na boyewa kowa ciwonta da kuma burinta akan Ameer, a yanzu kuma ta rasa gane dalilinta na kin son auren Nimra da wanda take so, domin ta ga komai a madafar iliminta sai dai illar ce ta kasa gani har yanzu. Waira? Ta kalleshi da idanuwanta masu kamar na mage. Lafiya kike yau? Ta girgiza kai domin ya saba fahimtarta tun kamin ta fada masa komai, ita kuma bata boye masa damuwarta a duk zuwan da yake gidan, wannan ya saka take jindadin zuwansa fiye da zuwa makaranta da ake takura mata. Ya bar jikin allon ya dawo kusa da ita ta tsaya. Fada min meya faru yau kuma? Ummi tana son Mijin Nimra, kuma Ummi tana da ciwo, kuma ciwon zai kasheta ta mutu kamar Waira, amman ba ta fada ba, Ya Maleek ya daki Nimra kuma Nimra tana son... Ta kasa karawa domin bata rike sunansa ba saboda haka bata san yadda ta kwatanta shi ko ta kira shi ba, Dattijon yayi murmushi ya dauko kujerar ya dawo kusa da ita ta zauna. Ki daina damuwa da matsalar wasu, ke ma kina cikin taki matsalar ai, ki daina kuka haka nan kukanki yana saka ni jin babu dadi Ta amsa tana kallonsa idonta na sake cika da wasu hawayen. Ya saka hannunsa aljihu ya dauko apple ya mika mata sai ta karba ta rike, a can idan suna darasi take cin apple kullum idan ya bata yau kuma da take cikin kuka da bacin rai sai ta kasa ci ta rike Apple din kawai a hannu, mikewa yayi tsaye ya nufi jakarsa ya bude ya dauko farin zomo ya nufota da shi ya dora mata saman jiki sai ta saki apple din da sauri ta rike zomon. Neman wannan zomon ya saka ban zo jiya gurin darasinki ba, ina fatar kina son shi Sosai sosai Ta rumgume shi a jikinta tana jin kamar beranta ne na baya data rasa. Thank You Murmushi da farincikin da ya gani a fuskarta wanda ya kawarda bakinciki da bacin ran da take ciki ne yafi komai faranta masa rai kuma daman abun da yake son gani kenan. Ta mike tsaye ta aje zomon zata rumgume shi sai yaja baya da sauri. Aa aa aa, dauki jakarki ki shiga ciki darasi ya kare sai gobe idan na dawo Ta juya ta dauki zomon da ya fara neman gurin boya tana dariya fararen hakoranta a waje kamar ba ita ba, ta dauki jakarta da dayan hannunta ta fito daga gurin ta nufi part din Ummi da gudunta, tsaye yayi yana kallonta da murmushi a fuskarsa har sai da ta fice sannan ya nufi jakarsa ya dauka ya fice daga gurin, har ya isa gate be daina waigen part din kamar ya san zata dawo ta daga masa hannu, sai gata ta fito daga part din tana masa waving hakoranta a waje. Daga inda yake ya daga mata hannu sannan ya fice yana tafiya kamar mai ciwon kafa. Bayan ya wuce ta dawo cikin falon ta fara neman zomonta da ya bata daga inda ta aje shi. Uteee Teee Uteeee Kiransa take da yarenta kamar an fada mata yana jin abun da take fada, abun da bata taba yi a gidan ba wato magana da yarenta shiyasa har yanzu babu wanda ya san kalar yaren da take a gidan. Ukur tek fi, utee utee kat... Fada masa take idan ya fito zata ba shi abinci mai kyau mai dadi. Ta fara leken kasan kujerun dake falon sai ta hango inda yake boye jikin wata kafar kujera, rarrafe ta yi ta isa gurin ta kama shi ta fito tana dariya ranta fal da farincikin da ta manta when last ta yi murna na samuwar wani abu. Daga yau sunanka Zill Ta fada da yarenta sannan ta mike tsaye ta nufi hanyar Kitchen. Tana bada baya Maleek ya saukowa daga stairs din da yake tsaye ya nemi guri ya zauna da mamakin yaren da ya ji a bakin Waira. Ita kan tana leka Kitchen din ta ga Hanne da Ummi a ciki sai ta ja ta tsaya ba tace komai ba. Me kike so Waira? Barta ta dauki abun da take so, it's high time ace komai sai an yi mata, ita ma ya kamata ta fara mu'amalantarmu kar mar yan'uwanta Ummi ta fada tana juyowa ta kalleta, sai Waira ta lake kafada tana son yi kukan shagwaba. Waya baki zomo? Ummi na tambaya sai dariya ta biyo bayan kukan da Waira take son yi. Teacher.... Ta amsa tana shafa shi. Ke kika ce masa kina so? Ta girgiza kai. No amman tana so Ina so Ummi ta gyara mata. Ina so Ta sake fada. Ummin za ci abinci To zo ki daukar masa Ta shiga cikin kitchen din ta nufi gurin da ake aje kayan marmari ta dauki kwatankwacin abin da ta san tana ci ta saka a plate. Hanne ta kalleta tana gyara tumatur ta ce. Zomo ya fi son gi a da salat ko karasss Waira ta kalli Ummi. Ummin zaki siya Karass, gida salak Muna da karas a fridge ai sai dai a nemo gi a da salat, Hanne duba mana Fridge akwai karass ki dauko mata Hanne ta nufi inda Ummi ta fada ta bude ta dauko ledar karass biyu, domin Ummi tana sakawa a kullashi a leda kamar na siyarwa aje idan an antashi amfani sai dai a dauko kawai. Waira ta karba ta dora sannan ta fito falon hannunta rike da plate daya dayan kuma rike da zomo, wayo idonta ya fara yi tana kallon inda zata aje zomon be gudu ba, duk abun da take Maleek be kalli inda take ba. Takowa ta yi a hankali sautinsa ganin shi kadai ne a falon, kusan lokaci daya aka cire masa tsoronsa daman ta rage tsoronsa domin ya dan canja ba kamar da ba, dazun ma saboda ta ganshi da bulala ne ya saka ta tsorata. Ta nufe shi ta