Sashe 101
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta ga ko zai sha abun da ta hada masa da hannunta. Daf da zai mike tsaye ya yi sipping tea sau daya ya aje cup din ya mike tsaye. Waira zan tafi Gida zaka je? Ya amsa mata kai, sannan ya kalli Ummi da hannunta ke dafe a kirji hawaye na sauko mata saboda Ameer ya sha abun da ta hada masa, kuma ya ci cake din da ta yi, the most beautiful thing ya zauna a falonta peacefully babu hayani yana hira da Waira. Kin manta school bag dinki shiyasa na kawo miki Thank you Waira ta fada sannan ta kalli Ummi. Ummi zan saka shi Ummi ta daga mata kai, ya kalli Ummi. Sai da safe Ya dauke kai ya nufi kofar fita, Waira ta bi bayansa sai ya tsaya ta iso ya kama hannunta suka fice daga falon. Daman to him rike hannun mace ba wani big problem ba ne, ita kuma ba haramci ba ne a addininta. Sai da ya fice sannan Ummi ta lumshe ido tana murmushin dake dauke da hawaye, she never thought abun zai zo kusa kusa kamar haka. Saboda ita ne or saboda Waira ne? Saboda da Waira ne. Ta bawa kanta amsa, tana bude idon zuciyarta na raya mata, abun da idanuwanta suka kasa gani tuntuni. Maleek ya wuceta gabanta kamar zai tashi sama ya aje mug din hannunsa kan dinning, sai a lokacin hankalinta ya dawo kansa. Maleek ba ku gaisa da Ameer ba, yau ya shigo gidan nan lafiya kalau kamar ba shi ba it's not wonderful? Maleek ya kasa cewa komai, ya sani matukar ya bude baki da zimmar magana abun da zai fito bakinsa ba zai yi ma Ummi dadi ba, and ba zai iya fada mata magana marar dadi ba saboda uwarsa ce. Kujerar dinning yaja ya zauna yana da girgiza kafarsa da alama kufular ta kai masa matuka. Farinciki ya saka Ummi barin falon ta nufi bangaren Abiey domin labarta masa abun da yake faruwa shi da yayarsa tsohuwar likita mai zaman kanta wato Dr Zainab. Tafiyar da Ummi ta yi ba karamin dadi yayi ma Maleek ba, daman so yake ya horar da Waira irin horon da ko kallon Ameer ba zata sake sha'awar yi ba. Ya mike tsaye da zimmar leka windows ya ga abun da take sai gata ta turo kofar falon ta shigo hannunta cike da dollars, tun da take a rayuwa a gidan bata taba rika kudi ba, bata san yadda suke ba, ba a taba bata ance je ki kashe shi ba, bata taba gwada siyen wani abu ba. Komai yi mata ake ko a school da sa'aninta suke siyen abubuwa da kudi be taba damunta tace zata siya ba, saboda sanin da da ta yi ba lallai ta iya cin abun da suke ci ba. Tana karewa falon kallon ta ga babu Ummi a ciki sai ta tsaya cak tana kallon Maleek gabanta ya hau faduwa da mugun karfi, ba dan yanzu da ta dawo falon ta ga Maleek ba, ba zata iya tuna yana zaune a falon ba, domin daukin ganin Ameer ya mantar a ita wani Maleek ma. Karaso mana Ya fada yana wani kashe ido dake tabbatar mata ba karamin duka zata sha ba idan ya ta shiga hannunsa. A gurin ta zubar da kudi ta har ta nufi stairs da gudu sai kuma ta dawo ta nufi inda Hanne take zaune ta fada jikinta da sauri ta fashe da kuka jikinta ya fara rawa. I'm sorry Hanne ta maida ta bayanta ganin Maleek ya tunkaro inda suke. Ayi mata hakuri yallabai a daga mata kafa Maleek be ce komai ba daman kuma ba zai ce ba, ya ayyana a ransa sai ya doketa a yau ba Hanne ba ko da kuwa Ummi ce a falon. Yana isa ya fisgota jikin Hanne ya jefar da ita kan kujera ya nufi gurin da Kristen yake ya ya cire wayar da zai iya cirewa ya nufo Waira, a maimakon ta tashi ta gudu stairs ko waje sai kawai ta yi zaune a gurin sai kuka take tana jarfar da hannu. Yana auna mata daya ta daka tsalle ta kwala wani uban kara tana murza jikinta, bata san wata rana da take da wayo da aka daketa da wani abun dukaba tun tana garinsu, sai daia yi mata hukunci idan ta yi wani abu, shi ma kuma ba sosai ba, bata taba sanin zafin jikinta ba irin yau. Mahmood ne ya sauko da gudu stairs saboda ihun da take, kamar zai same ya fadi haka ya iso gurin ya fisge bulalar da Maleek yake shauda mata. Meye haka me ta yi? Ta tashi da sauri ta boya a bayan Mahmood tana kuka sosai kamar ranta zai fita. Maleek can't tell laifin da ta yi dan haka ya fice daga falon yana hakki kamar shi aka daka ba shi yayi dokan ba. Mahmood ya kalli Hanne da mamakin abun da Maleek yayi ya ce. Me ta yi? Toh Wallahi ni ma ba zan iya fada ba, dazun dai gaban Hajiya aka yi komai, balle na ce ko ta yi laifi, wata kila ko dan ta shigo da kudi ne yayi mata wannan dukan Kudi? Ta nuna masa inda ta zubar da kudi, Mahmood ya nufi kudin ya dauka yana dubawa. Waya baki dollars haka Waira? Kofa kawai take iya nunawa, kuka ya ci karfinta ta yadda bata iya furta komai. Kofar Mahmood ya nufa ya leka waje be ga kowa ba ya dawo cikin falon. Babu kowa kin san wanda ya bata kudi Ya mikawa hanne tambayar kamin ta amsa Ummi ta shigo falon Yesmin na bayanta rike da warmers. Da sauri ta karasa gurin Waira dake kuka ta rikata. Waira kamar makira tana ganin Ummi sai ta zube a jikinta ta kara fashewa da kuka. Sosai ran Ummi ya bace bayan Mahmood ya fada mata abun da ya faru, sai ta hau masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. To me zai saka ya dake ta? Waya sani, Mahmood kira shi mana Mahmood ya dan daga gira yana kallon yadda ran Ummi ya bace, rabon da ya ga bacin ranta irin haka an jima. Upstarts ya nufa ya tura kofar dakin Maleek, sai da ya karewa dakin kallon be ga kowa ba, motsin da yaji na ruwa a bathroom ya tabbatar masa da yana ciki. Alhaji fito ka taba Waira Ummi na nemanka kasa Mahmood na rufe baki sai ga Maleek ya fito daure da tawul, gudun ya batawa Ummi lokaci ya saka shi saka short tare da jallabiya ya sauko kasa, be karasa saukowa ba yaja ya tsaya jikim stairs yana kallon Ummi wadda ta bude nasa sabon shafin ihu. Tun da kake a gidan nan ka taba ganin na taba yarinyar nan? Ka taba ganin na saka hannu na daketa? Akan me kai saka zaneta? Tun farkon zuwanta gidan nan ka tsinka mata mari ba tare da hakki ba Wacan marin mistake ne Ya amsa yana jin kamar ya karasa ya kara mata dukan domin har yanzu zuciyarsa bata daina tafasa da abun da Waira ta yi ba. Da mugun fusata Ummi ta ce Wannan kuma intentionally ko? Ummi baki ganin abun da take yi? Mu fa musulmai ne, kina kallom yadda take a jikin Ameer amman baki ce mata komai ba, ta raka shi baki hanata ba, ta dawo da kudi a hannunta duk be miki ciwo ba sai dukan da na yi mata? Haba Ummi, ko dan abun da yayi Nimra ai ya kamata ce an saita yarinyar nan a hanya domin ita na lura sam bata da hankali kuma bata san ciwon kanta ba Idan ya bata kudi, wata kila ya bata ne dan ra'ayin kansa, bana tunanin Waira zata roke shi kudi, kana ganin yawan kudin ma kasan ba rokonsa ta yi ba, saboda ita ya zo gidan nan yau, saboda ita ya sha abun da na zuba masa, idan ba a gode mata ba be kamata a saka mata da duka ba, saboda ita ana zai dawo gareni Hakan na nufin ke kika bashi damar yaje ya dauke ta a school kenan? Abun da kike kokarin ginawa a tsakaninsu is very wrong Ummi Ummi ta mike tsaye. Ni mahaifiyarka ce, this should be the last time da zaka ce I'm wrong, ni ban gina wani abu a tsakaninsu ba, duk wata alaka ko shakuwa da soyayya da ka gani a tsakanin Waira da Ameer su suka gina abarsu, ba ni da masaniya akan zai je ya dauketa a makaranta karka sake zargina, kuma karka sake saka hannu ka doki Waira, an yi n karshe Daker ya samu saukar da numfashin da ya hau masa saman zuciya. Sannan ya juya ba tare da ya sake cewa komai ba ya shige dakinsa. After two weeks later... Yana tafe Fiyya na bayansa rike da basket din da Mummy ta zuba masa kulolin abincin da za a kawo asibitin. Shi ya fara tura kofar ya shiga ya rike mata kofar ta shiga sannan ya rufe. Fiyya ce ta fara karasawa gurin gadon ta aje musu abincin tana yi ma Tsohuwar ya jiki tare da isar musu da gaisuwar Mummy, domin ita bayan kwana biyu take zuwa ta duba su, kanensa kuma time time idan zai so ko direba zai kawo abinci, Ameer kan kullum idan zai je aiki ko ya dawo sai ya shigo asibitin duba tsohuwar, domin jin yake kamar nauyinta a yanzu yana kansa. Ya jikin? Ya tambaya yana kallon Tsohuwar dake rike da ayaba tana ci. Jiki Alhamdulillah an nan, Allah yayi albarka kana ta fama da dawainiya Humaira ta mike tsaye ta bashi kujera, sai dai ta san ba zai zauna ba, domin ba gwada zama a dakin ba duk zuwan da yake. Kullum zai kin kin ba ni kujera, kuma kin san ba zama nake ba Ta yi murmushi. Ina jin ba dadi ne ace ina zaune kana tsaye Kuma kullum sai na tararda ke a nan ke kike jinyarta bayan ga mahaifiyarki, ba kasafai nake tararda ita, Allah yass dai kina zuwa aiki Duk lokacin da zaka zo kana sa'a da ina nan ne shiyasa, aiki kuma na daina zuwa ai tun a wacan