← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 165

Sashe 53

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuka sosai ba, wata kila labarin Waira ne ya taba ta, daman ya san ta da rauni, shi ma da yake dakakken ya ji tausayinta balle kuma ita. Ya cire hannunsa aya dake cikin aljihu ya saki curtains din. Khadeeja Candy Copyright 2023 Ta saki Ummi da sauri ta daga kai ta kalleta, a take ta mance da kalar nata damuwar, tausayin Ummi ya kamata, tsoro da mamaki suka bayyana a fuskarta. Ummi ta yi kasa ta zauna tana kukan data kasa controlling din kanta, Waira ta bita suka zauna a gurin sai dai ita ba kuka take a yanzu ba, mamaki ne ya kusan kasheta da kuma tausayi. Ganin dukansu jiran mutuwa suke yi. Ummi da ta zo da tissue da sunan ta sharewa Waira shawaye sai gashi Waira ta dauko tissue tana sharewa Ummi hawayenta. Cikin karfin hali Ummi ta yi murmushi ta karbi tissue ta share hawayenta, sannan ta mike tsaye Waira ma ta tashi tana kallon Ummi da wani irin kallo da take jin kamar ace yana iko da damar yaye mata damuwarta ta kawar mata da komai, domin ta rike ta kamar yarta bata taba nuna mata kyama ko hantara a iya zamanta a gidan ba, tana ganinta a ciki yanayi na damuwa sai dai ba ko yaushe ba, domin tana kokarin boyewa saboda yayanta da mijinta, hakan ya saka bata taba kokarin netso ta shiga duniyar tunaninta ta hango rayuwar da take boyewa a cikin ranta ba. Ummi... Waira tana tana son Ummi Ta fada tana kallonta, wani sabon babin kallon tausayi ta budewa Ummi da zarar ta kalleta sai ta hango abun da ta gani daga rayuwarta. Ummi ta rike fuskarta tana dariya. Ummi ma tana son Waira, amman ba haka ake cewa ba, kin kasa iya hausa daidai har yanzu, saboda baki bude baki ki yi magana idan ana hira, cewa zaki yi Ummi ina sonki fadi na ji Ummi ina sonki... Yauwa Yata yar albarka Ummi ta rumgume ta tana murmushin da kusan ya zame mata a dole a kowa ne wuni da dare, domin mutane suna ganin zahirinta ne ba ininta kuma ita kadai ta san abun da take ciki. Sun dade a haka sannan ta riko hannunta suka dawo cikin falon. Yammaci ranar har dare Waira kusa da Ummi ta rayu kamar yadda ta saba wai dai wannan ya kusanci ya fi na baya, ko ina Ummi ta motsa idon Waira na kanta. Dr Zainab suka tattauna maganar yadda Ummi take ganin ya dace da Waira sai dai bata yanke hukunci ba har sai ta ji daga bakin mijinta. Bayan Sallah Isha'i aka sake gabatar musu da abincin da Hanne ta girka, Ummi kuma ta damawa Waira madara da kankara kamar yadda ta saba mata a kowane dare. Tana gama sha ta kwanta akan doguwar kujerar tare da yin matashin kai da cinyar Ummi, Dr Zainab ce ta sauko sanye da gown marar nauyi sai hula a kanta tana rike da wayarta, Juwairiyyya da Yesmin suna dakin Nimra tare da yar'uwarta suna ta hira, Mahmood kuma ya fita tare da Jabir da dan lukuti wato Umar, Maleek ne kawai a Falon sai Ummi da suke kallon wani documentary da ake a Al Jazeera, Hanne ma ta shige BQ bayan gama aikinta a bangaren Ummi domin babu abun da ta rasa a sashenta sai dai kadaici da take fama da shi wani lokaci, kasancewar bata tare da kowa sai ita kadai kanta, da kuma karamin tv da Abiey ya saka mata da startime ta kama channel din da take so a ko wane lokaci. Ummi da Maleek ne kawai ke kallon sai kuma Gwaggon su Maleek wacce ta sauko a yanzu ta zauna tana latsa waya, Waira kam Ummi ce tv ta, daman can kallo ba burgeta yake ba, farkon fara ganin mutane a tv ya tsorata daga baya ta saba sai dai hakan ba saka ta saki jiki ta dauke shi da muhimmanci ba ko wani abun burgewa ba, har yanzu tana kallon wani abun na rayuwarsu dabam da ya sha banban da nata, akwai abubuwa da yawa da bata waye da su ba a tsawon zamanta a gidan, wasu abubuwan kuma basa burge ta, har gobe tana marmarin rayuwarta ta baya kamar yadda bahaushe ya ce sabo turken wawa. Lokuta da dama Ummi zata shigo falon ta tarar kowa yana zaune yana kallo ko taba waya ita kuma hankalinta yana can wani gurin dabam, ko kuma ta boya a bayan kujera ta kwanta idan bata son zama a cikin mutane, shi ma kuma sai idan Ummi bata kusa kamar idan ta leka bangaren Abiey ko kuma wata fitar ta kama ta, ko kuma tana kitchen tana girki. Time to time Maleek yake jefar Waira da kallo a sace, yana mamakin me Ummi ta fada mata take ta mata wannan kallon a yau, ya san ta saba da kallon mutane har sai mutum ya sargu, ba ma kamar Ummi sai dai wannan karon kallon da take yi mata ya so yayi yawa ko ma yayi. Suna a wannan halin ne Dr ta dauko labarin rayuwar waje wacce ta sha banban da Nigeria kasancewar gidan jaridar suna tattauna abun da ya shafi Africa ne, yadda ake bin doka da order da kuma yadda komai yake a tsare can take ta ba su labari, can jefi Maleek yake sako bakinsa yana fadar wani abun da ya sani a lokacin da Karatu ya kai shi kasar. Shigowa Abiey ne ya tsinke musu hirar waje da suke, annashuwar dake fuskarsa na farincikin ganin yar'uwarsa kuma macen da yake mata kallon uwa abokiyar shawara wacce ke share kukansa tun a wacan lokaci ya saka Ummi jindadi, domin bata da farinciki a yanzu sai an mijinta Abiey. Tsokanarta ya fara yi yana dariya sosai kamar ba shi ba, har buga kafa yake kasa tsabar nishadin da yake ji a yau. Sai da suka yi rabin hira sannan Juwairiyyya da Yesmin suka sauko suka gaishe shi domin ba su san shigowarsa har sai da Ummi ta kwalawa Namra kira. A bangaren ya cire babbar rigarsa ya aje domin yau ko marmarin part dinsa haya yi tsabar murna da farincikin ganin yar'uwarsa, Ummi ta daga kan Waira da ta yi bachi ta aje a kan kujerar a hankali sannan ta tashi ta dauko masa abincinsa ta jera masa komai a inda yake zaune. Abun ka da an'uwa cin abincin da Dr Zainab ta yi a dazun be hanata karawa a yanzu da an'uwanta yake cin nasa ba, hira suka sha sosai har kusan sha aya na dare Ummi tun tana saka baki ana yi da ita har ta fara jin bachi, sai hamma take tana murza ido. Toh Sarkin bachi ya fara kawo ziyara ko? Har yanzu baki daina bachi da wuri ba, na dauka duk kin watsar da ragancin nan ai Karaf Abiey yayi tare numfashin yar'uwarsa yana shigarwa matarsa. Doctor yadda Zahra take da juriya ko ke zaki iya ba a yanzu, duk fa yawancin aikin gidan nan ita take yi, ko bata ti girkin kowa ba sai ta yi nawa saboda ban son abincin kowa sai na matata da uwata kin kuma sani, ai tana kokari ma, da ke ce da yanzu kin yi bachi, ko kin dauka na manta yadda kike ne? Dariya ta saka ta girgiza kai, yadda yake tsokanarta sai ka rantse ita ce kanwa shi ne yaya, ko kuma ka yi zaton yan yaya da kanwa ne ba yaya uwa aya ba. Maleek ya tashi ya fice daga falon yana murmushi daman ya san halin Abbansa idan yar'uwarsa na kusa baya raga mata kamar yadda ita ma take masa idan ta tashi ramawa. Ummi bata bar falon ba sai da ta kira Mahmood ganin shiru shiru be dawo ba gashi har dare ya fara lulawa. Ga mu a hanya, Jabir ne ya debe mu nesa kin san ya kwana biyu be shigo garin ba, amman dai mun kusa isowa gida Toh Allah ya kawo ku lafiya Ya ake wayar kusa da inda Waira take kwance ta dauki babbar rigar da Abiey ya cire tare da jakarsa ta nufi bangarensa, ko minti uku bata yi da shiga ba, ya shigo yana cire agogon hannunsa tare da kiranta da sunan da ya saba kiranta tun kurciya har yanzu da girma ya zo, soyayya bata canja ba balle ya sake mata sunan da har gaban yayansa idan ya kama yana kiranta da shi. Hiayatee ya gidan? Ya aje komai a muhallinsa sannan ta juyo tana taya shi cire rigar dake jikinsa ta dauko masa bathrobe ya saka, sannan ta shiga ta hada masa ruwan wanka. Yau ka yi latti dawowa, na yi zaton zaka dawo da rana ma saboda zuwan Aunty Zainab Na so na dawo, amman aiki ya rike ni Wallahi Ya dai kamata ka huta Abiey, yaranka sun kawo yanzu wani abun za su iya maka shi, by the time ka kawo tsufa hutu ya kamata ka samu, muma iyalinka mu samu time dinka Wani abun dole ne sai ka yi da kanka, ko da na so na cire hannuna abokam kasuwancin ba za su bari ba, amman dai komai lokaci ne Kullum haka kake fada, kuma lokacin tafiya yake yi baya jiran kowa Abiey, lokuta da yawa ina jin son kasancewa da kai amman baka da time sai dare ko kuma da safe kamin ka fita, akwai abubuwan da ya kamata ace kana saka ido akansu a gidan amman rashin zamanka baya bari, nima kuma ba kullum nake son kasancewa da yara ba To zamu duba, abun da Hajiya take so shi za'ayi dole, zamu aje abun da zai aju wanda ya kamata a rage kuma za mu rage, har ma da wanda za a bari In Shaa Allah Toh Allah ya bada iko Ameen Allah ya miki albarka Ta yi murmushi ta bude wardrobe ta fara ciro masa pajamas, shi kuma ya shiga bathroom din, kamin ya fito ta feshe su da turare ta dauko masa maganinsa na ciwon kafafuwa da yake sha ta aje masa tare da ruwa. Sai da ya shirya ya sha maganin sannan ta fita ta koma bangarenta ta hado masa coffee, a lokacin babu kowa falon sai Waira dake bachi da kuma Plasma dake
Chapter 53 · 0% Book details