Sashe 8
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daddy ya maimaita. I'm sorry Baba Balarabe In Hausa Ka yi hakuri Baba Balarabe Ya fada muryarsa na rawa irin rawar bacin rai da bakincikin an saka shi bawa wanda yake gani kaskantacce hakuri. Daddy ya kara dowara da na shi. Ka yi hakuri Malam Balarabe Babu komai na gode da karamci Alhaji Allah ya kara kusanci da ma'aiki Baba Balarabe ya fada cikin farinciki domin a gurinsa Daddy ya gama masa komai tun da ya mutunta shi duk da kasancewar a karkashinsa yake. Sai da Baba Balarabe ya fice sannan Daddy ya kalli Ameer da ya matse spoon din hannunsa hannunsa nata rawa kamar mai jin sanyi. Karka sake dagawa wanda ya haife murna balle har ka saka hannu ka mareshi, saboda yana neman abun da zai ci a gidanku ba shi yake nufin Allah baya son shi ba, kuma ba shi zai baka damar wulakanta shi ba, na baka dama ka ji dadi rayuwa ka yi yadda kake so saboda ina kaunarka, na barka dukiyata ka wataya ka yi yadda kake so saboda kar wani ya fika jindadi ko gata, ban yi haka saboda ka wulakanta na kasa da kai ba, ban yi haka saboda na nuna maka akwai banbanci tsakaninka da talaka ba, ban yi haka dan ka wulakanta mutumen da sai Allah ya tsayar da ni ya tambaye ni akan me na bar ana ya wulakantasu ba, duniyar da ta tashi ka gani ban tara ta dan ta gurbata tarbiyarka ba Yadda ko wane harafi da lafazi yake fitowa daga bakin Daddy ya sanar da iyalansa bacin ransa akan abun da an da yake kauna fiye da komai a duniya ya aikata. Ameer ya saki spoon din ya mike tsaye ya fice daga harabar da suke karyar kumallon yana jin yadda duniyarsa gaba daya take tafasa tana fitarta da bakin hayakin kara mai matukar yaji da kaifi saboda bacin rai, da za a fasa zuciyarsa a yanzu wata kila da an tararda goraba da garwashin wuta a ciki. Bedroom dinsa ya shiga, duk wani abu da yake a kasa sai da yayi ball da shi yana ta buga kafarsa a kafa yana cizon baki kamar zai fasa Iips din. Duk saboda kai Maleek aka min wannan abun Ya nufi gurin da ya saba aje keys dinsa ya dauka ya fice. Kamar wanda baya son rayuwarsa haka yake tukin yana sauka daga kan titi sai kuma ya hau, sa'arsa daya babu motoci sosai a titin unguwarsu. Gurin daya yada zango a jiya a nan ya sake yada zango a yau din ma, sai dai a yau cikin motarsa yake zaune bayan ya bude murfin motar yana ta kallin itatuwan dake gurin, tunanin abun da zai yi rama wulakanci da Maleek yayi masa amman ya sake ta ina zai rama idan ya kulla wannan ya kwance wacan. Sannu dai Ya ji an fada bayan mintuna uku da wucewar wata mota ta gabansa ta dawo baya ta faka bayansa, dagowa yayi ya kalli kyakkyawar budurwar da idanuwanta suka taba arba da ita, kunnensa na kokarin turawa kwakwalwarsa daddadar muryarta domin tuna inda ta taba jin muryar. Sannu dai Ya samu kansa da amsawa duk da kasancewar yana cikin bacin rai. Kamar kai ne mutumen jiya mai bura ko? Yayi murmushi da be san ta inda ya fito masa ba ya fito daga cikin motar. Shi ne Yau ba busar ko kana cikin damuwa ne? Ya kalleta da mamaki a fuskarsa. Kina nazartar halayyar dan'adan ne? Ta yi murmushin daya kara mata kyau. Ina zaune tare da mahaifiyata, ina yawan fahimtar damuwarta, hakam ya bude min kofar fahimtar damuwar wasu Ya dan tabe baki try to smile sai kuma ya boye shi. Wani ne ya bata min rai, ina ta kokarin ganin na rama that's why I'm here Miyasa ba zaka yafe masa ba? Be cancanci yafiya ba, ya wulakanta ni kuma ya saka mahaifina ya wulakanta irin wulakancin da ban tana mafarki ba, yayi min abun da na fi tsana a duniya Who's that stupid guy? Wani sakarene da zan koya masa hankali soon In that case kai ma ka yi bincika wani abin da ya fi tsana, so that ya dandana dacin da ka ji, sai dai ban ci ka wuce iya yadda yayi maka ba, zaka iya bincikar abin da baya so sai ka yi masa shi ka ga na zuza kenan Ta fada da murmushi a fuskarta sannan ta nufi motarta. Kar na yi latti bye, sai wata rana idan Allah ya sake hada mu but next time karka yarda mu hadu na ganka da bacin ran nan kuma karka ce min baka rama ba Kallonta kawai Ameer yake cike da burgewa har ta shige motarta ta barshi a gurin tsaye. You're right yarinya, na fi kowa sanin abin da ya fi tsana kanki na ja kin kawo shawara, nice to meet you Ya fada da murmushi a fuskarsa kamar ba shi ne ya gama fushi a yanzu ba. ______________ ...WANI GARI... _Na Khadeeja Candy_ Ko wace dakika da mintuna idan suka wuce basa dawowa, rashin dawowar yana nufin rasa abubuwa da dama ciki har da lokaci idan baka yi amfani da shi a lokacin da ya dace ba, kyaunku ba zai tabbatar har a bada ba, ku yi aure a lokacin da maza suke ganinku suna yaba surarku har suna sha'awar aurenku, idan lokaci ya wuce za ku neme su ku rasa a lokacin ido zai rufe wata kila ku fadawa wanda be dace da aurenku ba, ba ni da buri a yanzu kamar ganin aurenku Ta sauke hannunta daga fuskar Nimra tana murmushi. Zamu yi aure Ummi, ni kin riga da kin san inda da wanda nake so kuma da zarar ya dawo daga Umra zan masa magana ya turo, sai dai ki yi ma Namra wa'azi ta rika sauraren masu zuwa gurinta, domin ita ce mai girman kai Namra dake ta danne danne da complete ta dago a fusace tana kallon kanwarta, wato Husainarta. Okay haka kike zama gurin Ummi kina min munafurci ko? Kina ruwanki da rayuwata? Maybe I'm not ready now ko kuma dukan masu zuwan basu min ba Ummi ta lankwasa kai tana kallon yarta. Na fa san halinki Namra, taya za a ce duk samarin dake nuna suna sonki babu wanda yayi miki? Ummi I'm serious gaba dayansu ni ba su min ba Ba ki sake jiki da su taya za'ayi ki san wadanda suka miki? Da wandanda basa miki? Cewar Nimra, domin ita ce mai far'a da saurin sabo ga son mutane, yadda take friendly da kowa sai ka dauka tana kaunar duk namijin da ta yi arba da shi ne. Nimra this is my life, can you please mind your own business? Ni fa ba irinki ba ce kowa far'a kowa dariya har wanda be kamata ace yana sonka ba ya zo yana maka maganar soyayya Ummi See? Kin ga abun da nake fada miki ko? Fadin rai ba zai bar ta ta kula samari ba Namra ta dauki fillon kujera ta jefawa Nimra, Hajiya Zahra ta yi saurin saka hannunta ta tare. Gaskiyar da ba ki so, dole mu fada miki, kuma karki yarda na sake jin bakinki ya furta cewar baya son kowa? Miyewa ta yi sauye bayan fadar haka ta nufi wata karamar kofa dake falon ta bude ta fita tsakar gidan da ko'ina yake tsab, matsawa ta yi kusa da flowers ta mika hannunta tana taba su a hankali, babu ranar da bata tunanin anta, babu ranar da zata zauna ta yi hira da yaranta akan rayuwarsu bata tuna da anta, damuwarshi ta haifar mata da damuwa da yawa, ta haifar masa da rashin kuzarin iya rike kanta a duk lokacin da ta tuna kamar yadda hawaye suka fara wanke fuskarta, ta kasa cire kanta a damuwa ta kasa daina tunaninsa duk da kasancewar likita ya gargadeta da ta cire damuwa a ranta saboda hawan jinin da take fama da shi. A tsorace ta juyo jin muryar Mahmood yana kiranta. Kamar hoto ya tsaya yana kallonta ganin hawaye a idonta. Ummi lafiya? Ta taba fuskarta sai ta ji hawayen sa bata san lokacin da suka sauko mata ba, murmushi ta yi ta share hawayen. Lafiya kalau, yanzu ka dawo? Eh ni ma dauko Abiey, amman Ummi ba lafiya ba kalli fa kuka kike yi Tunani kawai nake yi, makomar yayana idan bana raye that's... Ta karasa wasu hawayen na sauko mata. Haba Ummi ki daina kawo wannan abun a ranki please, ba zai taba faruwa ba tare zamu rayuwa In Shaa Allah Ya rumgume yana jin wani emotional, he can't imagine his life without her, ta ya za su iya rayuwa. Ummi ba zamu iya rayuwa ba idan babu ke, babu wanda zai rayu babu uwa a kusa da shi kuma ya more rayuwa, there's no love like a mother love for her child Kalaman da Mahmood yayi sai ya kara sakata cikin damuwa, ta kara tausayin anta, su da suka san dadinta suke fadar haka ina ga wanda be sani ba. Lumshe ido ta yi wasu hawayen masu zafi suna sauko mata, su da suka rayu da ita kenan suka san dadinta ina ga wanda ya rayu shi kadai be san dadinta ba. Ko waye mahaifiyarsa a yanzu? Ta tambaye kanta, kamin ta dago fuskarta ta share hawayen ta nufi kofar fita daga gurin tana sauke kanta kasa domin bata son yaranta da suke falo su lura da kukanta. dakinta ta shiga ta ci kukanta iya wanda ya isheta sannan ta wanke fuskarta ta shafa hoda da kwalli saboda ta bata da fuskar kukan amman ina ya kasa boyuwa a idon mijinta, domin a duk lokacin da ta shiga bangarensa idonta yake fara kallo ta nan yake iya karantar damuwarta. Zahra kukan me kika yi? Ya tsayar da shirya kulolin abincin da take kuma ta kasa hada ido da shi. Na tashi ne bana jindadin jikina Amman ba zan fita ba haka na barki ba, wani abun ya faru ne? Ko yarane suka bata miki rai? Ta kalleshi tare da girgiza masa kai. No, ina tunanin ana ne, na kasa manta ciwon har yanzu, ban san ranar da zan warke ba Kamar daukewar wutar nepa haka Abiey yayi shiru be sake cewa