← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 165

Sashe 50

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya saka bata katsalanta a harkokin gidan duk kuwa da irin yadda Ummi take son ta saki jikinta da su ba komai ta san muhallinsa a gidan ba, kuma bata taba kokarin cilastawa kanta sani ba, domin komai yi mata ake idan Ummi bata yi mata ba, Mahmood ko Nimra zata su mata balle kuma Hanne da Ummi tace ta rika yi mata komai a gidan, Namra da Maleek kadai mutanen da bata taba shan inuwarsu a gidan ba, idan zata zillo ta fadi babu mai tareta a cikin, Namra dai saboda jin kai da ganin level dinsu ba aya ba, Maleek kuma saboda kyamar matan da yake, duk kuwa da kasancewar ya canja sosai ba kamar da yake baya iya zama a gurin da mata suke zaune ba, ko cin abinci tare da kanensa, a yanzu kam ya kan ci ko zama tare da su har ma ya dan tsoma baki idan suna magana amman ban da Waira, komai zata yi ko tace ba zai saka baki ba, duk yadda Ummi zata yi zancen wani abu daya shafeta ba zai ce komai ba, komai take ba zai yi magana ba sai dai ya kalleta. Ita ma kuma bata taba kokarin son yi masa magana ba, tana kokarim kiyaye iyakarta da shi tun a lokacin da ta fahimci yadda rayuwarsa take, ko a kitchen ta shiga idan ta ga shi ne a ciki fitowa take sai yayi abun da zai yi ya gama sannan ta shiga, Ummi ta sha mata fadan hakan har ta fara gajiya, domin so take shi kanshi Maleek ya dawo kamar kowa, wannan ya saka tun tana cilastawa kanta da yayanta da shi kansa zaman a cikin yana takura har ta fara sabawa yana sakewa, domin kullum addu'a take shi ma kuma be fasa ba, azkar din safiya da yamma basa wuce tun a wacan lokacin da yayi mata alkawari. Haka ma idan zai kwanta zai yi addu'a tare da alwala sannan ya kwanta. Duk wani mataki na neman kariya da kuma mafita na halin da yake ciki Ummi ta bi, kuma tana kan bi, addu'ar da Abiey yace zai saka ayi masa bava fasa ba, an roka masa sauki har gaban akin Allah, tare da kyautata zaton addu'ar ta fara karbuwa domin kaso 50 na rayuwar da yake a baya ta barshi a yanzu, kyanar matan da yake ya ragu yanzu ba kamar da ba, sai dai har yanzu baya jin wani hauki ko ko burgewa a game da mace, har yanzu bata iya hada jikinsa da mace ko da kuwa Ummi ce balle kuma wata macen dabam da be taba kawowa kansa zai iya son wata mace balle har ta kai ga ya aureta ba, balle kuma ace wata mu'amala ta shiga tsakaninsu idan ma ya tuna da wannan sai ya ji baya bukatar auren gaba daya, ba dan kuma ba shi da lafiya ba, sai dai halittarsa data kasance haka. Sai da Umar ya gama cin abinci tsab sannan ya tashi ya shiga kitchen ya dauko kalar lemun da yake yana gyatsa ya zuba a cup ya sha sannan ya nufi upstairs. Ana kiran Sallah La'asar suka sauko gaba dayansu a tare, wato Umar da dan'uwansa Jabir sai Maleek dake warware hannun rigarsa Mahmood na gefensa, har suka sauko kowanensu da kalar kamshin turaren da yake, suka fice daga falon Waira bata dago ta kallesu ba, ta mike tsaye ta nufi upstars tana takawa a hankali har ta haye sama ta nufi dakin Ummi ta kwankwasa kamar yadda Ummi ta koya mata ta ja ta tsaya har sai Ummi ta bata umarni shiga sannan ta kai hannunta ta murda kofar ta shiga, suna hada ido da Ummi sai ta nufi Ummi da sauri ta zauna kusa da ita saboda ganin Ummi na kuka. Ummi tana kuka? Ummi ta yi murmushi ta rumgume Waira ta share hawayenta, tana kwaikwayar yadda take hausarta. Ummi ta daina kuka Waira... Ta yi shiru... Dr Zainab ta sauke ajiyar zuciya cike da damuwa take kallon Waira. Waira ba zaki iya tuna yan'uwanki ba? Garinku? Danginki? Da rayuwar da kike? Waira ta kalleta sai kuma ta yi saurin sauke idonta kasa ta kama hannun Ummi ta rike tana kara kwantawa jikin kamar Mage. Haka take min a duk lokacin dana tambaye ba, bata son fada min komai akan garinsu, al'adarsu ko addinninsu, ko wani abu daya danganci rayuwarta ta baya, kuma saboda mu san ina yan'uwanta suke ya saka muka saka a makaranta kuma ake zuwa har gida ana mata lesions da yamma kullum saboda ta iya Hausa da English, ta fada mana komai amman ta ki ba mu hadin kai har yanzu Cewar Ummi cikin damuwa tana kallon Waira. Kuma tana jin hausar da kyau? Duk wani abun da zaki fada da hausa ko turanci tana ji, sai dai gurin maidarwar wani lokacin yakan gagareta ko kuma ta yi ba daidai ba, wata kila shiyasa bata son yawan magana, ta fada min makaranta ma idan ta yi magana dariya suke mata Waira ina babanki? Da Mama? Uhmm-hmmm ai idan zaki shekara kina tambayarta wannan ba zata amsa miki ba, ba zata ce miki komai ba, kuma har kwakwalwarta sai da aka duba mana lafiya wai ko ta manta wani abu ne, amman aka ce mana lafiyarta kalau, sai dai idan asiri aka yi mata aka rabata da yan'uwan har ya saka bata son maganar su, ko kuma wanda ya saka a motar wata kila wani abun yayi mata daya danganci sihiri saboda ta manta komai kar ta fada Toh... Allah ya baku kenan, sai ku rike ta har ta yi aure Ummi ta yi tare tana shafa gashin kan Waira. Tashi kije BQ ki kira min Hanne ta zo ta yi serving din baki Waira ta aga daga jikin Ummi ta fice daga dakin zuwa kiran Hanne. Ummi zata yi magana wayarta ta yi ringing sai ta kalli wayar tare da kai hannu ta dauka. Nimra kina ina? Ina gurin Saloon Ummi Tun zafe har yanzu da La'asar? Eh akwai jira ne, ban ma samu Saloon din ba sauran mutun aya akai gareni Gwaggonku ta zo tana ta tambayarki Daga can cikin wayar ta kwala ihu tana zumudi. Oyoyo Mommy ta iso, gani tafe na ma fasa Saloon din Ummi ki ce in amata barka da zuwa Toh sai kin iso Ummi ta sauke wayar tana murmushi. NIMRA POV. Ameer na rike da hannun Nimra dake waya da Ummi hankalinsa kuma yana gurin wakar da Humaira take rerawa. Idan ka biye ta kan saurayi, sai ya kai ka ya baro, samarin yanzu yan shan minti ne, yar'uwa ki yi hankali Duniya budurwar wawa yarinya ki yi hattara... iyeee yaraye nanaye Humaira.... Kusan kullum idan ya zo gurin sai ya ji tana rera wannan wakar tun yana daukar abun nata shirme har ya fara tunanin ko da shi take, domin yana yawan zuwa gurin a yanzu kasancewar gurina da babu mai saka maka ido saboda privacy na gurin, idan har yana son ya fita ya shakata da Nimra to nan ne kadai gurin da yake zuwa da ita, saboda bata yarda su fita wani gurin gudun kar wani daga cikin familynta su ganta tare da shi, har gobe tana gudun labarin da zai je kunnen mahaifinta akan alakarta da Ameer. Duk kuwa da irin shakuwar da suka yi da juna a yanzu, da kuma irin yadda sonsa yake da tasiri a zuciyarta, Kullum da kalar karyar da take saboda ta samu ta fito daga gida ta hadu da shi, idan zata shigo a nan sai ta rufe fuskarta ruf da mask da glass saboda kar a ganeta, haka ma idan zata je gidansa. And kullum idan suka zo gurin Humaira ce kadai Ameer ya yarda ta yi serving dinsu, yanayin yadda kullum yake jinta da kamshi ya tabbatar zata yi kokarin tsabta, kuma yana mata haka ne saboda ya takura mata, duk yadda zai bi ya tsallawala rayuwarta idan ya shigo gurin sai yayi, ya kasa korarta ko sakawa a koreta tun bayan rokon so called Kakarta ta yi masa, sai dai ya saka mata ido da yawa ta yadda da zarar ta yi kuskure kadan sai ya mata hukunci mai tsauri, I sauran jama'ar dake aiki gurin tun basa kula har suka san irin takun sakar dake tsakansu. Ita kuma takan yi kokarin ganin ta yi avoiding ko wane kalar mistake saboda ta ba shi kunya. A kullum idan ya shigo gurin tare da Nimra sai ta rare masa wannan wakar, saboda yadda yake hugging dinta ko ya rike hannunta a gaban Humaira, ko kuma mutanen da suke kai da kawo wato ma'aikatan gurin, daman can Ameer be san wani abu kunya ba, ko da ba halinsa ba ne zai zabi yin haka saboda ya zubar da kimar Nimra duk abunda yake yana yi ne da ganganta, ita ma kanta Nimra da farko ba son hakan take ba sai dai tana kyalewa ta jure saboda farincikin Ameer, zuwa yanzu kam ta fara sabawa kanta da rabar jikinsa har abun da ya fi wannan ma. Idan shi kadai ya zo gurin ko da wani daga cikin abokansa tana da kalar wakar da take rara masa idan tana zirga zirga a gurin ko kuma ta zo kawo musu wani abun. Idan kuma da Nimra ya zo da kalar waka da take musu, zuwa yanzu dai ya haddace duka wakokin saboda yawan rarewar da take. Nazarinsu ne be gama yi ba. Babe.. Nimra ta fada bayan ta sauke wayar cike da zumudi. Ya dauke idonsa daga barin kallon Humaira dake goge desk tana ta rera wakar har dan kada kai. Uh.. -hmm Yayar Babanmu ce ya zo, kuma Ummi tace tana ta tambaya ya kamata na tafi kamin a sake kirana Ya murza yatsun hannunta dake cikin nashi. Tun yanzu? Ba mu dade da shigo gurin nan ba Amman mun dade a can ai, kuma ka ga na yi karya tun safe fa na fito gida Ai ba gajiya nake da ganinki ba Na sani, ai gobe da jibi na nan ko? Yeah, shiyasa nake son gidanku a san da ni amman kin ki yarda Ba yanzu ba Sai yaushe? Kullum cewa kike ba yanzu ba, to sai yaushe? Sai nan
Chapter 50 · 0% Book details