Sashe 125
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
a gidan, bayan kuma shi ya wulakanta yarinyar sai da suka dauketa ta waye a hannunsa sannan yanzu zai ce ita yake so, ni kuma ina ganin kamar hakan be dace ba, Kuma Mama Mr Bashir ya bukaci ya auri wata ya masa karya cewar wai ya auri Waira tun da a lokacin da ya fara ganinta, ina ganin kamar idan Mr Bashir ya san gaskiya ba zai jidadi ba, kuma be kamata Ameer yayi masa haka ba, amman idonsa ya rufe shi yarinyar kawai yake so, zuciyata zafi take saboda na fada masa haka Mama... Cikin kuka ta fada musu abun da ya faru, a inda ta yi sa'a tana rufe baki Ameer ya turo kofar dakin ya shigo, sai ta zabura ta mike tsaye ta gyara mayafin abayarta daya sauko kafadarta ta nufi gurin da aka aje kulolin da suka yi amfani da su ta dauka ta fice daga dakin. He just don't know why he didn't hate her bayan duk abun da ta yi masa ba bacin rai a yau, but a haka har ma kallon fuskarta yake har ta fice. Bahijja ta mike tsaye ta ba shi kujera. No ba zama zan yi ba, na zo na dubata ne kawai Aiko kara ka zauna domin akwai magana da yawa abakina Fadar Hajiya tana gyara kafarta mai ciwo. Kalli Bahijja sannan ya kalli Hajiya zuciyarsa na raya masa Humairah tace musu wani abu kenan. Akan me? Bahijja sai motsawa Hajiya ido take tana son karta fada amman Hajiya ta yi kamar bata gani ba. Humairah ta zo mana da wani labari a yanzu, wai kana da son wata yarinya yar wajen Zahra, wata take riko ne? Har ka gani kake so? Ya dan sauke kai kasa kunya is not part of abun da yake ji sai a gurin zababbun mutanen da akan zuba masa kunyarsu a lokaci daya, ba tare da shayin komai ba ya ce. Eh yarinyar ni ne silar zuwanta a garin nan gaskiya, kuma a yanzu ina son na aureta saboda ina sonta Yanzu Ameer bayan duk abun da Zahra ta yi, har ka ga ya a gidanta ka ce kana so? Ai kamar ka karfafa mata guiwar abun da ta yi ne Ya daga kansa sama ya sauke. Hajiya kullum kina min magana kamar Ummi makiyiyata ce, kina manta cewar ita din uwata ce, ko da haihuwata ta yi ta yanke ni na mutu na sake tashi hakan ba zai canjata daga kasancewa uwa a gareni ba, abun da ta yi min it hurt amman ya kamata mu bar komai ya wuce for now Hajiya taja dogon numfashi mai tsarke makoshi ta sauke tana kai. Idan kai ya wuce a gurinka ni a gurina be wuce, kai da ace ina da hali da sai na yi shari'a da wannan matar domin bakin ciki da ta saka min a zuciya ba karami ba ne Saboda me? Bama yin kuskure ne? Babu wanda yake a daidai right? Ta yi kuskure kuma ta gane kuskurenta a yanzu tana kokarin ganin ta gyara komai ne, bana jindadin yadda kike zaginta ina jin ciwo, dukanmu muna kuskure Ummi a yanzu bata bukatar tsinuwa ko tashin hankali sai farinciki, and idan har ba bata so ba zata daga hannu ta marin yayanta a gaban idona ba saboda sun fada min magana marar dadi, sannan ta furta cewar bata yafewa Namra ba idan ta sake aikata abu makamancin wannan? Ina ya ganin kaunata a idonta babu uwar da bata son yayanta, so please ku daina fadar abun da be dace ba akan Ummi Hajiya ta kalli Bahijja idonta na tsufa na cika da kwalla. Amman ita ce ta saka kake son butulcewa Alhaji Bashir? Mutumen da ya rike ka tsakani da Allah? Ya so ka a lokacin da ta jefar da kai ta baka baya? Ba butulce masa zan yi ba, ni na ga yarinyar ina so, kuma daman kamin yanzu iyayen yarinyar sun ba ni ita... Abun da ka fadawa Alhaji zaka fada maka? Haba Ameer ai wanda yayi maka riga da wando ya suturtaka be cancanci wulakanci daga gareka ba, Alhaji Bashir ya maka komai kuma har yanzu yana kan yi maka gashi kana ganin yadda yake wahala da mu So Humairah ta fada muku komai kenan, bana bukatar na yi sharhi, likita zai sallame ki gobe, zan zo na kaiki gida Yana fadar hakan ya juya ya fice daga dakin, har yanzu wani abu na bangaren girman kansa da ganin ba zai bi ra'ayin wasu ba sai nasa be sauka ba, sai dai ya ragu da kaso 50% cikin 100. After ya fito daga dakin cikin motarsa ya shiga ya zauna, kalaman da Humairah ta fada masa suna da matukar zafi kuma sun bata masa rai ba ma kamar inda take cewa bata alfahari da shi, ya zama mai son kai, shi kuma har ga Allah be ga haka ba saboda ya nuna abun da zuciyarsa take kwadayi take so sai ace ya nuna son kai how. Jin yayi an yi knocking glass din motarsa hakan ya saka shi juyowa ya kalli gilashin, wani farin matashi sa'arsa mai jini a jika ya gani tsaye sanye da kananan kaya wando da riga ya daure gashin kansa da ya zubo bayansa kamar mace, fuskar matashin na dauke da murmushi da kuma annashuwa a lokaci daya. Cikin farinciki da zumudin arba da fuskar da aka dade ba a hadu ba Ameer ya bude motar ya fito suka rumgume juna. Long time bro ya kake? Ya sake shi yana amsawa. Lafiya kalau, ya bayan rabuwa? Sai alheri, Eid ko? Idan ban manta ba Eid yayi murmushi mutane sai kallonsa suke domin yanayin yadda ya kulle gashin kansa ya nuna alamar shi din ba bahaushe ba ne, hasken fatarsa ma ya nuna haka domin ya sha banban da hasken fatar Ameer duk kuwa da kasancewar shi din ma fari ne. Me ka zo yi nan? Eid ya daga kansa ya kalli sararin samaniya sannan ya sauke kan yana murmushi. Na zo yin wani aiki ne, har zan wuce sai na hango ka a mota, kai me kake yi? Ameer ya saka hannunsa aljihu thinking of what to say. Just... Am... Oh na zo duba kakata ne da aka kwantar, sai na dan rage zango a mota, aiki kake a nan? Bana aiki a cikin mutane irinku Farko haduwa da kai a waje ma haka ka fada min Ashe baka da mantuwa, ya sarewa? Tana nan, kwana kin baya ma da na gwada busar akwai wata yarinya ta ce kai dan'uwanta ne sunanta Waira Eid ya dan matse ido alamar tunani. Ni? Ban santa ba gaskiya Aiko har da sunanka sai da ta fada, kuma ta ce duk garinsu babu mai yin busar sai kai Haka ne, maybe yar garinmu ce, amman be zama lallai na santa ba, amman ita zata iya sani na, anyway busata dai na zo na karba Kamar ya? Ana karbar busa? Ya za'ayi bayan kuma ka koya min Toh zamu gani dai, yanzu ka dawo nan da zama ne? Daman a nan nake, karatu ya kai ni Europe Hakan na da kyau, ina maka fatan nasara Eid ya mika masa hannu suka gaisa. Ameer ya saka hannunsa aljihu yana lalaben wayarsa. Let me get my phone mu yi pic na nunawa Waira dan garinsu It since like Waira dai budurwarka ce Ameer yayi murmushi ya duka cikin motarsa ya dauko wayarsa. She's the love of my life, ina sonta sosai gaskiya kuma so na aure Eid ya dafa kafadarsa yana murmushi. Ka yi sa'a kai ne, sai dai duk da haka zan fada maka ka yi hankali, ba aure daga garemu kuma ba ma aure daga wasu, idan ma ita Waira din ta yaudareka da zancen zata aureka to zata wahalar da kai ta fada min komai, amman duk da haka ina son aurenta na shirya bada komai akanta, ina son yarinyar nan Eid fiye da tunaninka Wani kuma ya rigaka sonta, tun tana karama yake kiwon abarsa har ta kai ga girma Waye kenan? Ka ce baka santa ba? Ita ma kuma bata fada min tana soyayya da wani ba Kawai na ayyana hakan ne a raina, kasan mafi akasiri mata masu kyau haka ake musu, kuma na san tun da ka ce kana sonta tana da kyau Tana da kyau sosai gaskiya, irin kyau nan mai daukar hankali Eid ya dauke hannunsa ya matsa gefensa sosai Ameer yayi selfie din sannan ya sake daukarsa shi kadai, sannan suka yi sallama Ameer ya shiga motarsa da zumudin zai tafi ya nunawa Waira dan garinsu. Eid kuma ya nufi cikin asibitin yana yi yana waigen Ameer... WAIRA POV. A hankali ta fara bude idonta tana ganin dishe-dishe kamar wadda ta dade a sume, ta maida idon ta rufe ta sake budewa still the same thing, ta dago hannunta ta murda idon ta sake budewa wannan karon da dan sauki tana iya kallo da shi saidai ba kallo irin na mai gani normal ba, haka dai ta daure ta tashi zaune ta kai hannu ta dafa kanta ta shafa goshinta ya rufe idon na wasu mintuna sannan ta sake budewa tana kokarin tuna abun da ya faru sai ta kasa, ita dai abun da ta sani Ummi ta fada mata Malamimta na kiranta after ta fito ta ga malamin ya bata baya, bata sake sanin me ya faru ba, sai a yanzu da ta ganta a kasa kwance. Mikewa ta yi tsaye tana jin wani abu mai kamar jiri yana dibanta tana daga kafar daker tana takawa idonta na wanyewa a hankali har suka koma daidai, sai dai jirin be daina daukarta ba har ta tura kofar falon ta shiga. Bakin kofar falon ta tsaya tana kallon cikin falon kamar wata bakuwa sannan ta cira kafa ta taka a hankali zuwa kitchen, hannu ta mika zata dauki cup har ta riko cup din ya subuce a hannunta ya fadi kasa ya fashe, ta sake mika hannu ta janyo wani shi ma ya sake faduwa sai ta rike sink din da kyau jin tana rawa kamar zata fadi. Are you okay So take ta juyo ta kalli mai mata magana amman ta kasa. Maleek ya karasa cikin kitchen din ya