← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 165

Sashe 103

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

need to know who you are, me kike so miye baki so, ya rayuwarki take. It tear me up when you turn me down, ina son na ji umin uwa how it's? To get to know you Yana fada yana kuka kamar karamin yaro. Ta girgiza kai. I don't want to force you Bude motar yayi ya fita ya rufe ya dawo back ya bude ita dai binsa kawai take da ido har ya shigo. You didn't force me, ni nake neman wannan alfarmar, ni dai kawai ina bukatar uwa ne, ko da wata uwarce ba ke ba zata tsaya a gabana tace ita ta haife ni, zan karbeta you leave a empty place here in my heart, i want you to fix it, that's little boy you left is still inside me, and he need a mother, i want to make a motherhood memory now Kuka yake Ummi ma kukan take jikinta na rawa tana son ta taba shi ta kasa, wannan karon ba tsoro ne ya rufe ba kunya ce irin na uwar data kasa bawa anta kulawa har sai da ya bukata. Ya saka rigarsa ya share hawayensa sannan ya fita daga back seat din ya rufe mata motar, jinginawa yayi motar ya na dan lokaci kana ya bude ya shiga ya cigaba da tuki, a gabansa dazun wata ke tsoron rasa nata iyalin shi kuma kari ma ya samu dan haka ba zai iya barin wannan damar ta wuce ba, ko dan ciwon da Waira ta fada masa Ummi tana yi. Kalaman da ya furta mata a yanzu sun yi effecting dinta, ji take kamar wani dafi ya saukar mata a jiki, kalmominta sun tsare jikinsa she couldn't hold her tears har suka isa gidan. Ya faka motar harabar ya ciro tissue da ya gani ya mika mata. I'm sorry please stop crying, a yanzu bana son kowa ya zubar da hawaye a kaina, ni ma ban kyauta miki ba ni ne silar mutuwar yarki Nimra wacce kanwa ce a gurina No Nono daya kuka sha, she and her sister they are my step-daughters, kuma ba kai ne sila ba kawai Allah ya kawo ne, karka haka a ranka, idan ma laifi ne ni ce mai laifi ni ce silar komai Ta karba ta share hawayenta sannan ta bude gefenta ta fita, shi ma fita yayi ya jingina da motar yana kallonta. Waira tana ciki? Kana son ka ganta ne? I always wanted to see her, zata raka ni na dauko wasu abubuwan ne a gida, kamin mu dawo make sure my room is clean Ummi ta kara dubansa da kyau. Da gaske kake Ameer? I need you by my side, ya zan yi? Hannu ta saka ta dafe kirjinta idonta ya sake cika da hawaye. Thank you so much for this opportunity, na gode da ka zabi zama da ni, thank you for everything Ameer Allah ya maka albarka, Waira zata zo yanzu. Thank you Ta furta sannan ta nufi hanyar falon tana jin wani kukan da bata san na minene ba ya sakota gaba, farincikin Ameer zai zauna da ita ne? Ko kuma na kuskuren da ta aikata a baya ne? Ko kuma na rayuwar da take tunanin ba za'a bata aro ta dade tare da anta ba ne? Barin jikin motar yayi yana fara zagaya harabar gidan yana kallon yadda tsarin gidan yake. Ba laifi su ma sun zubar da dukiya a ginin gidan kamar yadda aka zubar a gina na su, domin komai yayi tsarin ginin kadan ya banbanta da na Daddynsa. Yana tsaye Waira ta nufo inda yake da gudu tana murna, doguwar rigar material ce sanye a jikinta sai bakin talkami da karamar safa da ta rufe kafafuwanta kanta babu dankwali gashin kanta ya kwanta da kyau kana gani ka san ya sha gyara, sai kamshi take zubawa irin na manyan larabawa. Welcome A take dadin muryarta da shaukin ganinta ya wanzar da murmushi a fuskarsa. Thank you Ya amsa yana kallon yadda ta bude masa hakoranta ita kawai muryar yace zai zauna a gidan take. Ya kalli kanta. Ke miyasa baki son ankwali? Baki rufe kanki? Kin ga gidan nan akwai maza da yawa kuma za a iya cewa yayi kyau ko ki burge wani Su waye mutane? Ya wara ido yana kalle-kalle sannan ya kalli abun da ya fi daukar masa hankali a fuskarta wato idonsa. Masu aiki aljannu, ranar ma da wani saurayi na ganki a mota ga kuma Maleek da Mahmood Ya karasa yana rage murya kamar baya son a aji. Ni bana son komai a kaina, a garinmu ba a rufe kai, bana son rufe kai na Mu kuma a nan ana rufewa ai, kin ga ko hulace ya kamata ae kina sakawa, idan a garenku ba ayi a nan ai ana yi, ko baki san kin girma ba? You're not that small child Na sani, ni kawai bana son rufe kai ne Sai idan zaki yi Sallah kawai kike rufewa? Ni bana sallah ai Ya matso kusa da ita da mamaki. Ba ki sallah kamar yaya? Baki ga mutanen gidan suna sallah ba? Na gani? Uhmm? Ta motsa kafada. Bana yin irin addinku Ohh too bad, Babe you missed alot, akwai wani irin natsuwa, da imani da kusanci da aminci da rahma da tsaro a cikin ganawa da Ubangiji, shiyasa bana yarda ko da raka'a daya na rasa balle kuma jam'i, kin bar dadi yarinya Bana son na bar addinina, ko malamin dake mana lessons ya ce kar na kuskure na sake aikata laifi biyu kar na bar addinina Christian ne? Aa irin addininku yake Kuma yake son hana ki, yana son karki kwashi rahma da lada ne kawai, ke baki ga yadda Ummi take yi ba? Be burgeki ba? Ya burge ni, amman dai bana son na bar addinina No one will force you, sai dai na miki alkawari matukar ina gidan nan sai rayuwarki ta haskaka zuciyarki ta bude ki karbi gaskiya Zancen zama a gidan da yayi ya tuna mata da abun da Ummi ta fada mata, cikin zumudi ta ce. Ummi tace zaka zauna a nan da gaske ne? Wai na raka ka zaka dauko kayanka? Yes for, for her. Happy? Ta yi tsalle. Yes, can I hug you? Da can da kike rumgumata izini kike nema? Toh ai Ya Maleek ne ya ce ba kyau, wai harame ne Ta fada a shagwabe tana dan turo baki gaba, kalmar Haram ta kira da Harame domin haka kalmar ta zauna a kanta. Ya sakarwa fuskarta ido babu ko kyaftawa. Ke ai yanzu baki san banbancin Haram da Halal ba, hukuncin be hau kanki ba Ya rage tsawo tare da mika bakinsa ya sumbanci karan hancinta, yana dagowa motar Maleek na kunno kai cikin gidan, sai da ya kalli motar sannan ya sake maida bakinss ya sumbanci saman fatar idonta dake rufe tun a lokacin da ta ji numfashinsa na kokarin kwaurawa da nata. Jin karar motar ya saka ta bude idon da sauri ta juyo tana kallon motar dake fake saitinsu sai dai nesa da su, hakan kuma be hana ta yi ido hudu da Maleek ba, da ya kasa fitowa motar sai kallonsu yake, ya in duniya na uku na shirin haduwa a kirjinsa, yan sojojin zuciyarsa sai kawo makamai suke, jinin dake circulating a a jikinsa yana jefo masa da bomabamai. Ameer ya kai hannu ya juyo da fuskarta ta fuskance shi, sai ya sakar mata murmushi. Waya baki wannan zoben? Ya kai hannunsa ya taba zoben wuyanta, ta sauke kai ta kalli zoben. Sulem Wane Sulem? Bata amsa masa ba ta juya ta kalli Maleek da ya bude mota ya fito idonsa na kansu. Ameer ya sake kai hannu ya juyo da fuskarta. Hey kalleni a nan karki sake juyawa, Sulem dan'uwanki ne? Ta girgiza kai tsoro na bayyana a fuskarta. Sai ya saka hannu biyu ya tsinka sarkar ba tare da tsayawa ya ji waye Sulem din a gurinta ba. Kai waya ce ka tsinka ina so fa Zan siya miki wani, bana son ganinki da abun kowa sai nawa Tana mika hannu ta karba sai yayi baya da hannu yana murmushi, kamin ya juyo ya kalli Maleek dake magana yana aje numfashi da karfi. What a shame kamar kai? Yaushe ka gama da Nimra kuma ace cikin gidansu kana kokarin yi ma wata? Na yi zaton abubuwan da suka faru sun koya maka darasi, ashe kara maka kawai suka yi A take murmushin da fuskarta Ameer ya gushe, Waira ta koya bayan Ameer ta boya ganin Maleek ya tsaya daf inda take tsaye, sai tunaninta ya bata cewar dukanta zai yi. Ban zo dan yi rigima da wani ba, ban kira sunan wani ba, dan haka bana gayyatarka a rayuwata, ni ba yaro ba ne kamar kai, ina magana da Waira ne kawai, kuma ina tunanin babu alakata tsakanin Waira da Nimra, dan haka zanen kaddarar kowa ma dabam ne Hakane. Shiyasa ya zama abun dariya da mamaki idan aka ganka da wata, watan ma yarinyar da ka yi ikirarin baka sani ba, baka tsoron hakki zai bibiye rayuwarka? Kissing her ka taba ta ba abun kunya ba ne a gurinka Maleek Ita fa bata san banbancin halal da haram ba, a addininta komai daidai ne? Me kake kokarin karewa game da ita? Kai da na san babu ruwanka da rayuwar mata amman har kake iya magana saboda na taba ta? Miye damuwarka da haka? Ko dai kai ma ka fara rai ne? Na yi tunanin mataccen ne kai ai Ameer ya fada sannan ya kama Waira ya dawo da ita gabansa ya rike hannunta. Ni da kai muna da alaka da Nimra Ummi ta fada min, amman wannan ajiyata ce, ka daina shiga tsakanin bawa da Ubangidansa Yana fadar hakan ya nufi inda ya faka motar Ummi. Maleek ya hade yawu da karfi ya danne numfashinsa da duk wani bacin rai dake kokuwar barin zuciyarsa ya fito fili. Jin kamar ba zai iya jurewa ba ya saka shi juyowa ya kalli Waira dake kokarin shiga motar. Waira wuce ki shiga cikin gidan Kamar daman can umarnin take jira sai ta a juyo da sauri ta kalleshe ganin babu wasa a fuskarsa ya saka ta bar
Chapter 103 · 0% Book details