← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 165

Sashe 58

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

balle kofar nan kuma idan aka balleta sai na rabaki biyu sai dai a buga ni a Jarida ki bude dakin nan na ce Abiey calm down bari na yi magana da ita Ya dakawa Ummi tsawa. Ya zaki ce na kwantar da hankalina? Kamar baki san girman abun da ta aikata ba? Dole na yi magana da ita Zata bude amman ka matsa jiki kofar zan mata magana zata bude Ya matsa gefe yana sauke numfashi da karfi, rabon da ya samu kansa a bacin rai irin haka tun a lokacin da Deen yake raye. Ummi ta matsa kusa da kofar ta ce. Nimra... Na'am Sai ta amsa cikin kuka muryarta na rawa gwanin tausayi. Bude kofar nan, zamu yi magana da ke Aa Ummi aa dan Allah Ki bude na ce, so kike ki sake bata mana rai? Tambayarki zamu yi kuma dole ne ki amsa mana zamu yi magana ta fahimta ne ki bude kofar Ummi ma da kamar fada take mata maganar domin ita ma nata ran a bace yake. Sanin Abiey zai fi yi mata sassauci idan Ummi tana kusa ya aaka ta nufi kofar ta bude tana kuka sai ta matsa baya da sauri. Ummi ce ta fara shigowa sannan Abiey da sauri Nimra ta yi gefen Ummi sai Abiey ya daka mata tsawa. Karki kuskura taba min mata, dawo nan ki tsaya...! Wani irin dauke numfashi ta yi kamar zata shide, saboda tsawar ta ratsata kanta shiga har cikin jikinta, sai ta dawo ta tsaya a inda ya nuna mata jikinta na rawa. Tun yaushe kike aikata fasadin nan? Me ya saka baki bashi damar zuwa gidanku ba kika zabi kebewa da shi? Saboda ba za su yarda ba Abiey, kuma ba mu aikata fasadi ba Abiey, Wallahi ban aikata zina ba For how long kike tare da shi? Ummi ta tambaya. Anfi shekara..... Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, waye ubansa a garin nan dan gidan uban waye? Akan wani dalili kike haduwa da shi a wajen gidanku? Abiey ya tambaya yana matsawa kusa da ita, muryarsa kuwa kamar zata tashi akin. Matsawa ta yi baya tana kallon Ummi kamar tace Ummi zo ki cece ni ba dama. Bata ankaro ba Abiey ya kai mata mugun naushi a fuska sai da hokoranta aya ta dago bakinta ya cika da jini, wani tsalle ta ta yi, ta yi baya da sauri ta rike bakin ta haura saman gadonta. Wayyo Allah na na shiga uku, Ummi ki taimake ni Abiey ka yi hakuri dan Allah Waye shi na ce? Ya sake daka nata tsawa, a rike ce ta fara zazzago masa bayani. Ameer ne, Ameer dan gidan Alhaji Bashir, wanda suka yi fa a da Ya Maleek, Ameer din da na bawa Motata ta tafi da ita Katsina Ameer in... Bata karewa ba Abiey ya daga mata hannu ya rumtse ido, Ummi kuma ta fadi zaune tana kallon Nimra cikin matukar tashin hankalin da ba a saka masa rana. Bakar zuri'a, bakin jini, ubansa ya gama shi kuma yanzu na shuka min nashi, so yake ya lalata min zuri'a so yake ya asa min bakincikin da ubanaa ya bari... Abiey ya fada cikin wani irin fusata da be san ma iya abun da zai fito daga bakinsa ba. Kamin ya juyo gurin Ummi. Duk laifinki ne, babu gargadin da ban miki ba akan yaron nan, ta ya za'ace yarinya tana fita waje ta hadu da wani sama da shekara aya baki sani ba a matsayinki na uwa sai bayan da ya gama lalata min Ummi ta mike tsaye tana kallon mijinta cikin wani irin bacin rai ta amsa masa. Kwarai laifina ne Alhaji Aliyu sai ka hada ni da ita Nimra ka binne...! Ta daki kofar akin da karfi ta fice fuuu kamar zata tashi sama..... MALEEK POV. Ohhhh Ya fada yana buga teburin dake gabansa, bayan Abiey ya fada masa ya tafi makarantar su Waira ya ji abun da yake faruwa saboda sun buga masa waya kan cewar ta yi fada, kuma ya kira wayar Mahmood be samu ba, ga Ummi ya ji yanayinta da matsala zai tafi gida. A dole dolensa ya tashi tare da wayarsa da key din motar ya fice daga office din, yana gwada kiran Mahmooda ya ji ko zai same shi ya fada masa Abiey yace ya tafi saboda shi ya fasa zuwan, be samu ba har ya shiga motarsa ya murza key ya dauki hanyar makarantar. Har ya isa cikin makarantar be daina karan Mahmood ba kuma be samu wayar ba. Cikin makarantar ya shiga gurin principal din ya gabatar da kansa, sai suka isa da shi gurin vice principal, a nan ya samu Waira zaune rumgume da jakarta, tana ganinsa ta mike tsaye da sauri ta nufo inda yake wai ita ta ga wanda ta sani sai kuma ta ja ta tsaya tunawa da basa shan inuwa aya. Gurin ya samu a one of visitors chairs ya zauna yana kallon mutumen da ya mika masa hannu suka gaisa. Sunana Maleek na zo ne akan maganar wannan yarinyar Ya nuna Waira. Eh mahaifinka ya kira ai ya fada cewar ba zaka samu zuwa ba, amman ansa zai zo Lafiya me ya faru? Fada suka yi da wata yarinyar, ita dai yarinyar tace Waira ta fara tsokanarta, sai suka fara fada shi ne ita Waira ta dauki dutse ta buga nata akai kanta har da jini yanzu haka ita ma mahaifinta yana hanya Maleek ya juya ya kalli Waira da ta rumgume jaka, sannan ya juyo ya kalli mutumen. Waira bata da fada gaskiya, sai dai ko idan ita yarinyar ta fara taba ta Ba a gane gaskiyar kowa, ita ta kasa magana daidai yadda za a fahimce ta Maleek ya dauki takadar dake gaban teburin mutumen ta pen ya mika mata. Rubuta abun da ya faru Ta karba ta soma rubutawa tana hawaye. Kullum tana tsokanata tace min ni ban iya hausa ba, kuma bana magana da daidai, tana ce min kuma kafira ban san me hakan ke nufi ba, ko ta rika min dariya, shi ne yau da aka kai mu park ta tsokane ni kuma na buga mata dutse saboda ta fi ni girma ba zan iya fada da ita ba Ta mika masa sai ya karanta ya mikawa mutumen, mutumen ya karba yana tsaka da karantawa mahaifin yarinyar ya shigo tare da ita, har wani hakilo yake yana an taba masa ya. Wannan ne mahaifin yarinyar? Aa yayanta ne bismillah zauna mana Ba zan zauna ba, kuma sai na dauki mataki akan abun da aka yi ma yata matukar ba ku hukunta yarinyar nan ba sai kun ga abun da zai biyo baya domin a be fi a ba Ka yi hakuri ka zauna muna tattauna ne a akan maganar? Tattaunawar me? Ga ciwo kuna kallo ta ji wa yata kuma ku ce kuna tattaunawa karshenta a ba ni hakuri bayan an cucu yata Toh me kake so ayi maka Malam? A fashe mata kan ita ma? Bayan kuma yar ka ce take tsokanarta? A take fada ya kaure a tsakaninsu, domin Maleek ya kasa jurewa da abun da mutumen yake yi ne, suka yi ta fadawa juna magana daker aka shigo tsakaninsu, Maleek ya saka Waira a gaba suka fito daga cikin makarantar zuwa gurin motarsa. A nan Waira ta nade hannayenta ba zata shiga mota ba, daman can bata kebewa daga ita sai shi a mota ba, fadan da ta ga yayi da wacan mutumen ya saka ta tsorata tana ganin kamar itama fadan zai mata idan ta shiga motar. Ya bude mata motar da kansa. Shiga mu tafi Ta lake kafada. Shiga ko na mareki yanzu nan Ya daka mata tsawa, sai ta shiga motar da sauri ya rufe ya zagaya dayan side din ya shiga ya saka key, wani yanayi ya samu kansa a ciki na dabam, domin be taba kusanci da mace a mota kamar haka ba, be ma taba daukar mace a motarsa ba, sai wannan karon wanda ya tabbatar da acan da ne ba zai ma iya ba, ko da kallonta ne balle har ya dauketa. Waira bata son Abiey, Abiey ya kira waya yayi mata fada, Waira bata son Maleek, Maleek ya zo da mota yayi mata fada ta shiga Mota Ta fada tana takurewa gurin daya sai hawayen da suka fi kama da na shagwaba take. Ya kalli gefenta ya dauke ido. Baki son uba, baki son ansa sai ki kashe su toh Tana jin hakan ta san bakar magana yayi mata sai kawai ta fashe da kuka, ta kama zoben dake wuyanta ta rike. For the first time ya ji kukan mace ya sauka a kunnensa daidai wa daida ya cika kwakwalwarsa. Ohhhhhhhhh miye wannan kuma? Zaji min kuka for sake i hate this crying, Abiey why zaka aiko nan? Kai Ya bude wani guri a motarsa ya dauko airpod ya saka a kunnesa ya kunna Bluetooth din wayarsa yayo connected ya kure karatun Qur'ane dan ya daina jin kukanta. Har aka isa gida bata daina kuka ba, shi kuma be bata hakuri ba ko kallon inda take be yi ba. Tana ganin ya cire abun kunne ya kashe motar sai ta bude muryarta mai kara ta kwala ihu just to annoy him tun da ta lura baya son kukan. Louder please Ta kara karawa tun da ya bukaci haka. Very good well done, to fitar min a mota please... Bata fita ba sai cigaba ta yi da kukan, shi kuma ya bude motar ya fita ya barta a ciki. Yana shiga cikin falon ya san ya lafiya ba, domin tun a downstairs yake jin kukan Nimra bama kamar da ya haura sama. Dakin mahaifiyarsa ya fara shiga sai ya same ta tsaye gaban madubi tana hawaye, kamar jiran take ya shigo sai kawai ta juyo ta fara bashi labarin abun da ya faru tana ta maimaita gurin da Abiey yake dora mata laifi, tun fara bashi labarin har ta gama hawaye take. Ba zai bar ni da abun da ya ishe ni ba, sai ya dauko wani laifin ya dora min? Maleek be ce komai ba ya juya a fusace ya fice daga dakin Ummi, be yada zango ko'ina ba sai akin Nimra, yana shiga ya
Chapter 58 · 0% Book details