← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 165

Sashe 83

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Littafin WANI GARI na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660* Kamar mashayi haka Ameer ya isa gaban motarsa sai budewar ya gagareshi, saboda rashin kuzari da kuma rawar da zuciyarsa take wadda ta haifar da jikinsa zazzabi. Jinginawa yayi jikin motar ya kife kansa wasu kalar hawayen sauko masa wadanda be san daga ina suke fitowa ba. Sai dai ya san a rayuwarsa be taba kuka da bakinciki da jin tashin hankali a lokaci daya kamar yau ba. Meyasa ma ya zo duniya? Akan me rayuwarsa zata yi tsayin da zai ga wannan bakar ranar a yau? Da ace ya mutu kamin yau da yafi masa domin be sam komai ba. Matar nan kullum addu'a nake mata ina jin na rasa wani gurbi na uwa, ina jin abubuwa da yawa da ace tana raye ba zan aikata ba ko na rasa ba, ashe tana raye, ta kuma san ina raye amman ta kasa zuwa duba ni ta kasa nemana sai a yanzu da ta shirya tarwatsa rayuwata, me zai saka ya zubar da hawaye? Akan macen da bata cancanci zama uwa a gareshi ba? Wani bangare na zuciyarsa ya karanta masa, a take ya ji kukan ya yanke masa, kuzarin da ya rasa ya taho da gudu ta yarbe shi, fa sauri zazzabin ya bar jikinsa. Sai ya bude mota ya shiga yayi reverse, yanayin yadda yake tuka motar har ya fice be nuna yana cikin tashin hankali ba, duk kuwa da kasancewar hakan ya kasa boyuwa a fuskarsa. Tafiya mai nisa yayi kamar zai fita garin Abuja, kawai be san inda zai tafi ba, ya tafi gidansa ya kebe shi kadai? Ya kama hotel ya zauna? Or yayi ta driving har ya gaji? Ya rasa na zaba atsakanin abu ukun da zuciyarsa ke lissafa masa. Sai dai definitely ya san baya bukatar zuwa gida a yanzu, ji yake kamar ba zai jure kallon Mr Bashir a matsayin wanda yayi adopted dinsa ba not his biological father, duk rayuwar da suka yi a tare duk wahalar da Mr Bashir ya sha a kansa ace ba mahaifinsa ba ne? Ya dauki nauyinsa ya rike shi tsakani da Allah all this ahi ba mahaifinshi na gaskiya ba ne? All this wealth da ya tashi a ciki ya ga Mr Bashir na juyawa har ta kai shi ma ya isa sarrafa wani abu daga ciki, ba mahaifinsa ba ne? Yadda yake sakar masa kudi da duk wani iko da gata still he's not his biological father? Even for once Mr Bashir be taba nuna masa cewar shi ba ansa ba ne. Ya cire shi a kowace kalar rigima ya bashi damar aikata duk abun da yake so ya daure masa gindi still ba mahaifinsa ba ne? Zuciyarsa ce ta buga da mugun karfi abun da kwakwalwarsa take kalato masa ya fi karfin tunaninsa, wani hudu bakincikin mai zafi ne ya rufe masa kirji. A take ya ji babu wanda yake bukatar gani kamar a lokacin kamar Mr Bashir, kamar mahaukaci haka ya taka burki ya juya motarsa tsakiyar titi he just got lucky titi babu manya motoci a lokacin, ko da ma akwaisu ya shirya yin haka domin jin yake kamar rayuwarsa bata da amfani a yanzu. Sai da ya kusa isa gidan then ya sake jin bana bukatar shiga cikin gidan ba dan an masa laifi ba, rauni zuciya yake kusantoshi a duk lokacin da rai ya rasa masa ganin fuskar Mr Bashir. Faka yayi nesa da gidan ya fito waje ya tsaya yana kallon motar kamar mai tunanin abun yi? Jin kamar numfashi zai gagareshi ya saka shi bude motar ya dauko ruwan gora ya daga kansa sama ya kafa gorar a bakinsa ya fara shan ruwa kamar rakumi, ragowar kuma ya daga gorar sama suka zubar masa a fuska suka jika jikinsa musammansa ma kirjinsa dake masa zafi kar an watsa masa tafasasshen talge a ciki. As Simple as that you just look in to my eyes kika fada min cewar ke ce mahaifiyata? Akan me? Me yasa ba zata bar wannan ya cigaba da zama a sirrin ba? Ya tambaye kansa wasu hawayen ya cika idonsa? Ina take son na rayu? So take na tsani duniya? Me jindadin rayuwata ya tsare mata? Ya sake tambayar kansa a karo na biyu, yana jifa da empty gorar ruwan dake hannunsa. Saboda ka taba Malee ne, kuma ka taba Nimra su ai yayanta ne da take matukar kauna Zuciyarsa ta amsa masa tambayarsa da amsar da zata fi gamsar da shi. A take ya girgiza kai yana kara gamsuwa da hakan, domin a lokacin da duk wannan be faru ba, bata nuna cewar shi danta ba ne, a yanzu ya yarda da maganar Hajiya Jamila cewar bata sonsa, kalli yadda wanda ba ubansa yake nuna masa kauna fiye da iyayensa, kalli Hajiya Jamila ma yadda take sonsa. Tabbas da ace Ummi ma tana sonsa ko da tabin haka ne da bata barshi ya tashi a hannun wani yana masa kallon ubansa ba. Yanzu ya duniya zata kalleshi? Taya zai fuskanci mutane? Alfarmar da yake samu ta mahaifinsa zai rasa a yanzu, korar wanda yake so da bawa wanda yake so aiko ko mukami ya fita a hannunsa a yanzu, mutanen da ya wulakanta saboda yana jin cewar shi dan Mr Bashir ne ya za su kalleshi idan suka ji? Mutuwa ce kawai be yi ba a lokacin amman komai na duniya ya taru ya tsaya masa cak a lokacin. Yana kallon wayarsa na kara ya kasa dagawa kuma ya kasa kashewa. Yana tsaye a gurim har aka kira sallah Magariba, that's what he can't afford to miss, sallah in time, wannan ne a abun da ya saka shi shiga motarsa duk kuwa da kasancewar ba kiran sallah ya ji ba, domin unguwarsu tafiya ce mai nisa tsakaninsu da massallaci that's why kowa yake yin masa masallacin a gida, for masu kula da addini kenan, wasu kuma babu ruwansu da gina Masallaci, though he's muslim App ya gane Magariba ta yi saboda kiran sallah da app da ya fara. Yana fara tukin wayarsa ta kara ringing sai ya kalli inda wayar take aje, number Hajiya Jamila ce take kiransa da sunan da yayi saving number ta wato Ammy with heart emojis. Ya amsa kiran and put the phone on speaker. Ameer kana ina? Ka daga min hankali, na kira mahaifinka yace min baka gida, shi ma yana ta kiranka baka daga wayarsa ba? Please Ameer ka san muna matukar kaunarka, mu ba kamar Zahra ba ne, idan ka shiga wani hali ko ka illata kanka zamu shiga uku ba, ba zamu iya bearing rashinka ko shiga damuwarka, dan Allah karka jefa kanka a matsala please we love you kuma ka sani, sanin gaskiya ba zan saka mu canja maka komai ba, ba zai canja cewar kai an mu ba ne, sai ma kaunarka da tausayinka da suka karu a zuciyarmu Cikin kuka take fada masa hakan, shi ma hawayen yake yana jin tausayinta da kuma na Mr Bashir da kansa a lokaci daya. I promise you ba zan jefa kaina a halin da hankalinku zai tashi ba, i will control my temper, i will take care of myself Thank you, please pick up your phone call your dad ka yi magana da shi Does he know kin fada min gaskiya? No kawai na kira wayarsa a saboda na kiraka baka daga ba, sai ya fada min shi ma ya kira baka dauka ba kuma na san ya damu I already reach home bye Ya yanke kiran ya jingina jikin motarsa, this is the first time da ya taba tsayawa haka a gate din gidansu peacefully ya danna horn yana jiran a bude masa. Yaja motar kamar marar lafiya ya shiga yana ta kallon bangaren da mahaifinsa yake. Calmly ya faka motar ya bude ya fito ya bar wayarsa da takardar da Zahra da bashi tare da hoton ya nufi Garden. Tun da yake a rayuwarsa be tana kunna fonfon Garden yayi alwala na sai yau, saboda yana matukar kyamar gurin, kasancewar ma'aikatan gidan suna yawan zuwa gurin diban ruwa idan babu a fanfon masallaci. Damuwa ta mantar da shi dokokinsa na ware kansa da yake a masallaci yana sallah a one place ba tare da hada kafada da sauran mamu ba, sai gashi a sahun gaba, wani direban Daddy yayi ikama, mai bawa fulawowayin gidan ruwa yaja Sallah, kamin su sallame mamaki ya cika kowa. Ya sallame kamar yadda ake sallame ko wace sallah magarib, ya karanta addu'o'in sallah as usual ya daga hannunsa zai yi ma mahaifiyarsa da be taba manta ta mutu ba addu'ar samun rahma a kabarinta, sai ya tuna she's alive and healthy, hawaye suka zubo masa, saurin rumtse ido yayi ya hade yawu, ya mike tsaye sannan ya bude idon ya fice daga masallacin. Fitowarsa ta yi daidai da shigowar Motar Daddy, saboda kauna irin ta uba da a sai Daddy ya kasa tuka motar ya wuce ansa sai sauke gilashin motar yayi yana tukin daidai tafiyar Ameer da ya ki yarda ya kalleshi, but murmushi yake saboda ya boyewa Daddy damuwar da ta bayyana kanta a fuskarsa. Yau na yi latti ka riga ni samun jam'i Mu ma yanzu muka gama sallah Yanayin yadda ya amsa masa da kuma muryarsa da kallonshi da Ameer ya kasa yi ya kuma damuwar da ya gani a fuskar dansa, ya saka yayi saurin isa inda yake aje mota ya faka, domin shi yake tuka kansa da alama fitar ba mai nisa ba ce, domin jallabiyar dake jikinsa ama ta nuna haka. Kamin Ameer ya iso Daddy ya fito motar yana kallonsa. Sai Ameer ya kasa karasawa inda yake ya yanki hanya ya shige bangaren Mommy. Daddy na ganin haka ya ciro wayarsa dake pocket ya kira Hajiya Jamila. Kamar tana jiran kiransa domin ringing daya ta fara ta yi picking. Kin kira ni dazun, kina tambaya ta Ameer na fada mikin nima na kira shi be daga ba, and now yarona ya dawo gida, baya son kallon idona, na ga damuwa da ban taba ganin irinta ba a fuskar ana, ya kasa karasowa kusa da
Chapter 83 · 0% Book details