Sashe 52
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
ita, za a kasheta Miyasa kika gudu? Baki da yan'uwa a can? Ke baiwa ce ko kuma me? Ta girgiza kai hawaye na sauko mata kamar ba gobe. Waira bata san kowa ba, ita kadai take zaune tana da.... So take tace bera da zakara kuma ba zata iya fadar hakan da hausa ba, ta suna sunan da aka fada mata na zaka da bera. Waira tana da Hens, Waira tana da Rat, Waira Waira zata mutu kusa Sarki ba zai kyale ba, zai kasheta Ta girgiza hancinta na zubar da majina kamar yadda idonta ke zubar da ruwan hawaye. Waira bata son ta mutu, Waira tana son ta ga Eid Waira bata son ta koma, ba zata gane hanya ba Da gaske take fada domin tana yawan tuna mutanen garin da rayuwar da take a garin amman ko kadan ta kasa tuna sunan garin ma balle kuma ta san hanyar da zata bi ta tafi, ita dai ta san ta rayu a wata duniyar kamin ta samu kanta a nan, kusan kullum sai ta kwanta da tunanin Eid da berayen da suke rage mata kewa. Ta kalli Jabir tana kuka sosai. Waira bata son ta mutu, Waira tana son Eid, Eid ba zai zo ba, Sulem ba zai zo ba... Waira tana Son Sulem.... Ya matso kusa da ita ta jingina kanta jikinsa yana jin tausayinta na kama shi. Har suka ci suka sude Maleek be dago ya kalleta ba tun bayan kallon da yayi mata da farko, sai dai kunnuwansa suna sauraren komai take fada and one by one ya fahimci ko wace kalma dake fita bakinta. Waira bata son makaranta, suna mata dariya idan ta yi magana, Waira bata da kawa a makaranta Kusan duk wani abu dake cinta a rai sai da ta fadawa Jabir, the way da yan makaranta suke tsokanarta yana mata ciwo sosai, idan aka tambayeta ta kasa bada amsa ko kuma ta yi bayani ba a yadda suke yi ba, suna mata dariya ita kuma tana jin zafin haka, idan an tashi cin abinci bata da abokin zama ta ci abinci, she's not that child da za a ce tana tsoron mutane domin ba small girl ba ce, but yanayin rayuwarta ya saka tana shakkar kusantar mutane, ga yanayin mu'amalarta da shigarta ya ya banbanta da na sauran yan makaranta domin bata son taka talkami har yanzu, tana isa makaranta sai take cirewa ta rike a hannu, ta inda Allah ta taimake ta rashin rufe kai ba ita kadai ce bata yi ba, domin akwai yara da yawa a makaranta da basa rufe kansu wasu ma ristoci ne wasu kuma musulmai ne da suka ari rayuwar turawa suka yafa. Ko baya ga wannan ma ita dai gani take an cilasta mata na cewa dole sai ta koyi rubutu da karatu, abun da bata iya ba tun farko, sai dai hakan ya taimaki rayuwarta domin tana jin yaren hausa da English a yanzu, sai idan an yi mata mai sarkakiya ne kawai ba zata gane ba. Rike hannunta aya a ciki ayan. Waira tana son Ummi.. Tana son Nimra.. Waira tana Son Mahmood... Ya nuna kansa. Waira tana son Jabir? Ta dago ta kalleshi idonta har sun sauya kala saboda kuka. Sai ta girgiza masa kai alamar aa. To Waira tana son Maleek? Nan ma ta girgiza kai. Waira tana Son Namra? Da Abiey? Ta girgiza kai a karo na uku cewar bata son su. Mun shiga uku har da Mai Gidan gaba daya? To shi mi yayi? Bata son Abiey da ansa Maleek saboda basa sakar mata fuska yadda Ummi da Nimra suke, kuma basa janta a jiki yadda ya kamata, Jabir kuma yau ta fara ganinshi taya zata san halinshi har tace tana son shi. Maleek ya mike tsaye ba tare da ya dauke plate din da ya ci abinci ba ya fice daga gurin ya koma cikin falo. Ita kuma sai ta saka gefen rigarta ta share fuskarta, Jabir ya yamutsa fuska alamar kazanta. Noooo bari na dauko miki tissue Ya tashi shi ma ya bi sahun dan'uwansa Maleek, sai ita ma ta tashi ta nufi hanyar Garden tana tunani kala kala, a cikin abubuwan da take tunanin babu mao mata ciwo kamar rashi ganin Eid tana son ta sake saka shi a idonta kamin ta mutu, domin ta san mutuwarta zata iya zuwa mata a ko wane lokaci, Sarki be taba alkawari ya saba ba, kuma ba zai fasa akanta ba. Abun ka da gwani, daga shiga dauko tissue Jabir ya shantake da bawa Ummi labarin abun da Waira ta fada masa, da kuma fahimtar manufarta da yayi. Tausayinta da kaunarta sai ta karu a zuciyar Ummi. Shiyasa bata da sakewa yarinyar nan kullum tana zaune kusa da ni, komai ake hira ba zata saka baki ba, shekararta aya a gidan nan amman taki ta sake jiki da kowa, wata kila shiyasa ta ki ta fada mana inda garinsu yake saboda bata son a maida ta garin, Allah kadai ya san abun da ta yi going through Tace bata son Abiey da Maleek amman tana son da Nimra da Mahmood Ummi ta yi murmushi tare da mikewa tsaye tare da mika hannu ta karbi tissue dake hannun Jabir. Ba ni tissue Jabir ya mika mata ta zara ta share hawayenta daman abu kadan yana saka ta kuka a yanzu saboda zuciyarta a raunace take. Jabir har ya mike tsaye zai bita sai mahaifiyarshi sai dakatar da shi. Yanzu kuma ai sai ka ba ta damar magana da ita tun da ka yi mai yuyuwar, sanadinka ta fadi abun da ta boye kar kaje yanzu zata ce ka tona mata asiri wata kila yardar da kai ta yi shiyasa ta fada maka Gaskiya yarda ce kam tun da bata fadawa kowa ba sai ni Nimra ta kwantar da kanta jikin Dr zainab. Ta ba ni tausayi Darasi ne agareku ku da kuke da iyayen a raye, kuma suka dage suka ba ku gata da tarbiya daidai gwargwado, sai ku bisu da addu'a kuma ku cigaba da yi ma Allah godiya kuna musu biyayya Maganar da Dr Zainab ta yi ta soki Nimra, sai ta yi shiru kamar ruwa ya ci tana kallon wani gurin na dabam har sai da Jabir ya fice sannan ta tashi zaune tace. Mommy akwai maganar da nake son na yi da ke, amman ba yanzu ba sai mum kebe saboda magana ce mai girma, but ke kadai zaki iya taimako a nan saboda Abiey yana jin maganarki kuma zaki iya tankwara Ummi ta aminta ma Dr Zainab ta kalleta da duba da babu wasa a cikinsa. Wace magana ce? Akan wani ne, kusan dai zan iya cewa maganar aurena ne, amman dai sai kin kara hutawa zuwa gobe ko jibi zai mu yi maganar, amman for now karki fadawa kowa mun yi maganar wannan sirrinmu ne Dr Zainab ta gyada mata kai cike da jindadi daman kullum burinta ta ga sukana dan'uwanta, kusan ta fi kowa damuwa da rashin auren da kowa be yi ba a cikinsu tun daga kan Maleek da be son zancen aure har zuwa Nimra da Namra da suke mata, a take ta ji duk ta matsu goben ta yi fada mata ko minene. *** *** *** Waira na tsaye tana kallon barewar dake ta kiwo ita kadai Ummi ta iso gurin rike da tissue ta dafa Waira, sai Waira ta juyo ta kalleta. Kin ce kina so na, amman baki taba hira da ni kin fada min damuwarki ba miyasa? Ina yawan tambayar ina iyayenki suke baki fada min ba Waira ta sauke ido kasa. Waira bata da kowa, Waira bata san Iyayenta ba, Waira bata san waya haife ta ba, Waira bata ga Babanta ba, bata ga Mamanta ba Ta fashe da kuka, sai Ummi ta riketa. Wani lokacin barin damuwa a cikin rai ba ya maganin komai, ko da yake fitarwa ma bashi magani, sai dai idan ka fada kana jin sanyi, we all have story to tell, kowa yana da damuwa da burin da yake boyewa a zuciyarsa, Waira na miki alkawari, matukar abun da kika fada gaskiya ne, zan rike ki kamar ata wata kila saboda haka Allah ya dubi zuciyata ya yafe min son zuciyar da na aikata a baya, ni ma na rasa farinciki kamar dai, ina da damuwa wacce na boyeta a raina na kasa fadawa kowa, sai dai na san hakki ba zai daina bibiyata ba, tarin dukiya da kayan more rayuwa sun yi kadan su manta da ni kuskuren da na aikata a baya, farinciki a zuci yake na rasa nawa Hawaye take sosai tana jin kamar ta samu damar fashe urjin da ya nuna yayi mata tuwa a zuciya. Wata kila shaidan ne yake ribantata, amman ina jin son ana a raina, fiye da sauran ina kewarsa sai kace na taba rayuwa mai tsawo da shi, ina son na hada su guri aya matsayin yan'uwa, gabar dake tsakaninsa da Maleek ina son ta wuce na rumgume su biyu a lokaci aya, ina son kamin na mutu na roki yafiyarsa kamin ranar da Allah zai tsayar da ni ya tambaye miyasa na aikata son zuciya da abun da nake ganin kamar hanya ce mai bullewa, na manta shi ke kashewa ya raya, soyayya ta rufe min ido a wacan lokaci, ni kawai yarinya ce mai wauta da sakarci a wacan lokacin, hakkin Deen da na iyayensa yana kaina, hakkin Ameer yana kai na, ina son na gyara komai kamin an lokacin da ya rage min ya kare, ina son na kyautatawa ana na fada masa irin kaunar da uwarsa take masa, na roki yafiyarsa, so nake na yi masa gata kamin na mutu amman taya.....? Ta rumgume Waira tana kuka, Waira ma kukan take duk kuwa da kasancewar bata fahimta takamaiman dalilin daya saka Ummi take kuka sosai haka ba, kuma take kalaman da bata gane manufarsu ba. Rumtse ido ta yi ta dafa hannun Ummi a kokarinta na fahimta abun da Ummi take fada. Duk abun da suke Maleek na tsaye jikin gilashin windows din akinsa yana hangesu, sai dai ko za'a kashe shi ba zai iya fadar abun da suke cewa ba, ko kadam be jidadin hango mahaifiyarsa tana