Sashe 102
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
lokacin Ya daga mata kai. You got lucky na canja if da yanzu na koreki Dariya Fiyya ta yi kamar yadda Humaira ma ta yi dariyar. Baka bukatar ka koreni ai, ni na kore kaina? Why? Ta daga kafadunta. Kawai dai Be sace cewa komai ba, ya kalli agogon hannunsa. Kuna bukatar wani abu? Aa bama bukatar komai a yanzu Shigowar da Dr yayi ne ya katse hanzarinsa daga yi musu sallama ya fice. Likitan dake cikin shiga ta kayan likitoci ya iso gurin ya mikawa Ameer hannu suka gaisa. An fada maka sakona Ameer ya kalli Humaira wadda ta dago tana kallon Likitan. Yanzu nake kokarin yi masa bayani Likitan yayi murmushi. Kin manta kenan? Aa na tuna yanzu da na ganka Ta fuskanci Ameer dake jiran abun da zata fada masa. Yace gobe za a kwance daurin da aka yi mata, a duba, idan yayi haka ake so, idan kuma be yi ba sai an sake wani Tana fadar idonta na cika da kwalla. Sarkin kuka daga magana sai hawaye, haka jiya kika min fa Likitan ya fada yana kallonta. Bana son tashin hankali, ba mu da yawa a dangi kusa, bana son na sake rasa kowa Ba saki rasata ba, aiki ne kawai kuma ni ba cinye ta zan yi ba, I'm not zombie Ta yi murmushi tana share hawayen idonta. Ni ban ce ba Da dai yafi Duk abun da ake Ameer be ce uffan ba, sai kallon tsohuwar dake cin ayarba hankali kwace yake kamar ba ita ake fadar za a sakewa aiki ba. Ita hankalinta a kwance ma yake naki ne a tashe Likitan ya fada yana kallon Humairah Toh abun da Allah ya kawo ba sai hakuri ba, gwagwarmaya wace kala ce ba mu gani ba? Ameer yayi murmushi yana kallonta, karfin halinta da imani ya burge shi. Allah ya kara lafiya Ya fada sannan yayi ma Fiyya alama da su tafi da ido, Fiyya ta yi musu sallama suka fice. Likitan ya juya ya kalli Ameer har sai da ya fice sannan ya maida dubansa gurin Humairah. Am ya sunanki ma? Humairah.. Haka ashe na rike sunan Ta yi murmushi tare da sauke kai kasa, sai ya dauki file din da ya shigo dashi bayan ya gama duba Tsohuwar ya fice. Zaunawa Humairah ta yi tana fadin. Yau Mama bata zo da wuri ba, gashi ina son na shiga makaranta kar na yi latti Ki zuba min abinci da aka kawo sai ki tafi, ai zata zo wata kila ta tsaya wanke tsumman da tafi da su jiya ne Maybe Ta dauki plate din ta bude coolar jalof din shimkafa ce da aka yi mata ado da doya ta sha kayan kamshi da vegetables ga kuma mai har yayi yawa. Rabin plate ta zuba mata ta dora mata a saman gadon ta matsa mata da ruwa kusa. Ba zaki ci abincin ba? Sai na dawo zan ci Toh Allah ya kiyaye hanya, yau ba su bada kudin da suka saba fadawa ba Yau da gobe ai sai Allah Hajiya, wata kila sun fara gajiya ne ko kuma sun manta Ba dai gajiya ba, sai dai ko mantuwa amman dan dan abun da suke ba mu ai be taka kara ya karya ba a dukiyarsu. Ni ba dan ba a son kaddara ba ai da na ce kara da aka yi haka, dubi ki ga kullum sai an kawo abinci, ga kudin nan, kuma sun dauke duk wata hidima ta asibitin nan, gaskiya suna da kirki, ko da can ke ce da masifar ki kike ganin kamar ba shi da kirki, kullum fa sai ya zo, mamansa ma kullum tana hanya Hmmm Hajiya, ke dai kin ganshi kawai amman da can ba haka yake ba, yanzu ne ya canja Ke ma ai na san halinki fitina ta miki yawa Ta yi dariya ta nufi gefen gadon Hajiya ta dauki jakarta ta goya, sannan ta yi mata sallama ta fice, tana tafiya harabar asibitin ta ji an kira sunanta. Humairah Ta dan juyo kadan sai ta yi arba da Likitan dazun, murmushi. Doctor Na'am fita zaki yi? Eh makaranta zan je Wace makaranta? Ina kike karatu Ya jera da ita suna tafiya. Sky King University Ah makarantar manyan mutane kenan, wane course? Microbiology Wow, ke babba ce Kune manya ai Kika ce ba, muje na sauke ki No akwai inda zan biya kamin na wuce Karki damu duk zan iya sama direbanki, kin ga wata rana zan yi alfahari na ce na taba daukar Humairah yar Microbiology a motata, zan ce ta yi min alfama ta shiga motata Murmushi ta sake yi ta girgiza kai. Bana son zolaya, Likita za'ayi ma alfama? Eh mana ke baki san babba ce ba? Bata son jan zancen da tsawo dan haka ta yi shiru bata sake cewa komai ba har suka isa gurin motae yar yayi mai matukar kyau, kana ganinta kasan sabuwar mota ce, sai da ya saka key sannan ta bude front seat ya shiga ta zauna. AMEER POV. A Area 2 ya sauke Fiyya gidan wata kawarta da zata yi birthday, sannan yayi driving kansa zuwa gida, tun a harabar gidan yake kallon bakuwar motar da ke fake a compound din. Domin ba ta yi kama da motocin gidansu ba, yanayin yadda akai parking din ma ya fahimtar da ba direbobin gidansu ba ne. Yana wasa da key hannunsa ya shiga falon, sai ya samu Mummy da Ummi zaune, Daddynsa yana kan dayar kujerar fuskarsa dauke da murmushi. Ummi na ganinsa ta mike tsaye kamar karamin ma'aikaci ya ga boss dinsa. Ameer ka dawo Daddy ya fada, sai ya nufi inda Daddy yake ya zauna yana yi ma Ummi kallon tsanaki, ta yi rama sosai farinta ya wuce na ainahin fatarta wani fari ne mai she ar da fata, fatan idonta ta yi fari kana kallonta ka san lafiya bata isheta ba. Baka gaishe da Mamanka ba, tun fitarku take nan tana jiranka Mummy ta fada tana murmushi, still be ce komai ba, sai kallonta kawai yake. Hakan ya saka Ummi jin wani iri sai ta ji kamar ta tsargu, domin ganin take komai ta yi ma Ameer a yanzu ba zata burge shi ba. Na zo ne kawai na ganka, Daddyka ya fada min abin da ya faru, ina addu'a Allah ya tsare gaba, kuma idan ka ba ni dama ina son ni ma naje na dubata for the sake of you Ta karasa maganar muryarta na rawa kamar mai tsoron abun da zai fito daga bakinsa. Ya dauke kai sannan ya mike tsaye. Lemme drop her home Fadar sai sauke ta a gida, abun mamaki ne a gurin Mummy da kuma Mahaifinsa Daddy ya san da be son ganinta ba zai sauketa gida ba, ba ma zai zauna a falon ba, sai dai Daddy be san manufarsa ta yin haka ba, hakan ya saka shi mikewa tsaye tare da kai hannu ya dafa kafadarsa. Karka fada mata magana marar dadi please Cikin wata siga mai kamar rada ya fada masa haka, Ameer ya girgiza kai. Ba abun da kake tunani ba ne Yana bashi amsa ya wuce yayi gaba, Ummi ta dauki jakarta zuciyarta na raya mata maybe Ameer zai yi amfani da wannan damar ne ya fada mata karta sake zuwa gidan duba shi. Mummy ta rakota har gurin motar ta tuko kanta, hakan ya saka Ameer barin jikin motarsa ya iso gurinta ya mika mata hannunsa. Ta ciro key a jakarta ta mika masa, ya nufi motar ya bude mata backseat, ta ji kamar ya karramata yayi mata alfarma a cikin daruruwan mutane. Hajiya na gode sai anjima Toh Allah ya kiyaye hanya, ni ma zan shigo wani lokacin In Shaa Allah Allah ya nufa Ummi ta fada sannan ta nufi motar ta shiga, Ameer ya rufe motar ya zagaya ya shiga mazaunin direba yayi ma motar key. Yana tukin Ummi na hawaye ko da ace ba a cikin dadin rai Ameer zai tukata ya kaita gida ba, ita abun farinciki ne a gurinta. Karki sake zuwa duba ni, idan kina son ganina ki min waya zan zo Ya fada yana tukin a hankali. Ba lallai idan na ce ina son ganinka ka zo ba Saboda me? Saboda ban kyautata maka ba, a lokacin da kake bukatata, na san kana kallona da wannan abun a kullum Yayi shiru na tsawon lokaci kamin ya sake fadar. Me yasa to kika yi? Hannu ta saka ta share hawayen idonta. A lokacin ina tsoron rasa rayuwar mahaifinka ne, saboda likitoci sun tabbatar min, idan ba a yi masa aikin ba, zai iya mutuwa, mun siyar da gidan gadonmu da kayan dakin Yayata Maryam mun hada duk be wadatarwa na bi yan'uwana da abokan mahaifina, kowa be taimaka min ba, ina cikin wannan halin ne Dr Hamid ya kawo min mafitar cewar akwai wacce take son siyen ciki, idona a rufe na aminta aka siyar, sai bayan da aka yi aikin mahaifinka sai kuma rayuwa ta yi bankwana, babu yadda ban yi ba saboda na gudu da cikinka amman ban samu dama ba, saboda ina da talaka ba ni da ikon komai, a cikin yarjejeniyar da aka yi da Hajiya Jamila ance idan har na karya alkawari zan biya kudi mai yawa, kuma ba ni da su... Ta yi shiru saboda hawaye dake mata zuba suna son su ci karfinta su zame mata kuka. Su waye yan'uwa mahaifina? Ban san su ba Idan kana son sani, zan fada maka su, zan tafi da kai har Kano ka gansu Sun san abun da kika aikata? aa ba su sani ba, duniya tana kallon an da na haifa da Deen a matsayin mataccen Hawaye sun saukowa Ameer, sai ya kara rage gudun motar ya faka gefen titi ya jinginar da kansa jikin kujera. I'm sorry, na san baka kaunata na san a gareka ban cika uwa ba, na san ba zan taba kima a idonka ba, amman please don't leave me, i want you here with me, na san ba abu ne mai sauki ba, kuma ban cancanci ko wace kalar alfarma a gareka ba Idan kina bukatata a kusa da ke, you can make a room for me, sai na dawo gidanki na zauna, i