Sashe 34
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
take a cikin motar tana mamakin a ina ya kawo ta? Kuma me zai mata? Ta san ba gurin dazun ba ne da take jin jama'a da yawa, duk kuwa da bata bude ido ba amman ta ji alama hakan kuma ta ji anyi motsi da abun da take ciki kamin a kawota nan. Jin kamar ta aminta da shi ya saka ta fara kai hannunta ta taba interlock din dake gidan so take ta ji idan bashi da sanyi kamar na asibitin da suka baro, sai ta samu wannan ta dumi sosai saboda zafin ranar da ake a Katsina, ganin haka ya mika hannunsa ya fito da kafarta waje, sannan ya riko hannunta ta fito a hankali tana kallon gidan da yake da girma sai dai ba irin matsiyacin girman nan ba, sai dai an kawata shi da shuke shuken itace kala kala a jikin ginar gidan har zuwa gate haka ta rika bin itacen ta kallo kamin ta maida ga harabar gidan, ba mamakin yadda aka zagaye gidan take ba, domin ko a duniyarsu akan zagaye gida da wadanda suke iyawa ko kuma suke da Sarautar a garin, wani da kasa za ayi wani da itatuwa, fenti da ginin bulu suke abun da bata taba gani ba, yanayin ginin gurin yayi kama da na inda aka fito da ita wato asibitin sai dai kamshin nan ya banbanta da can, kamar wacce ta yi arba da abun tsoro haka ta rike shi da sauri da kuma karfi tana raya cewar idan ma ya kawota a irin gurin da aka fito da ita ne ba zata yarda ta sake shi ba, haka kuma ba zata yarda ya cutar da ita ba. Sanin zata bashi wahala gurin shiga gidan saboda rikon da ta yi masa ya saka ya duka ya dauketa cak kamar yar baby, sai ta saka hannayenta ta zagaye wuyanta tana murmushi idonta a rufe, tana matukar son a dauke ta a haka sai dai bata samu domin Eid baya mata haka saboda gudun fushin Sarki ko fadansa, kusan tun da take a rayuwarta sau biyu ko uku kadai ya taba yi mata irin wannan daukar. Yayi mamakin ganin murmushi a fuskarta domin be tsammanci haka da wuri ba, gashi murmushi ya kara mata kyau dattin dake jikinta yayi kadan ya boye kyauta gaba daya. Sai a yanzu yake jin karnin da take na datti har wani tsami tsami take irin na Shugaban kazaman garinsu, kai kana jin warin kasan ta dade bata ga ruwa ba kuma ruwa be ganta ba, sai dai ba kawowa kansa cewar bata son wanka ba a tunaninsa bata samun wankan ne wata kila a inda aka boyeta ko aka fito da ita a rufe take ba a barinta fita. Ba karamin jihadi ta yi ba na amincewa ya shiga da ita har cikin gidan, tana jin karar bude kofa sai ta bude ido domin bata saba jin irin sautin ba, a nan fa ta zama na daji a makka idonta kamar za su fado tsabar kallon labulayen falon da kujeru ba ka kamar lokacin da idonta ya sauka a gurin TV dake kashe ta kalli guluf da fankar dake aiki sai ta kankameshi ta rufe ido. A tunaninsa ta fi bukatar wanka da komai a halin yanzu hakan ya saka be direta ko'ina ba sai bathroom din kanwarsa. Tana jin sanyi tile din sai ta dage kafafuwanta tana son ya dauke ta. Nooo a nan zaki tsaya Maimoon zata taimaka miki ki yi wanka Ta bude idon kamar ta san abun da yake fada, a nan ma ta shiga bawa idonta abinci, tun daga kan kofar bathroom din take kallo har zuwa tube da karamin madubin da yake lake, kamin ta daga kanta sama, sakinta yayi a hankali ganin su biyu ne kawai a gurin babu wani ya saka bata yi yunkurin yin ihu ba ko roke shi, ya nufi durum ya bude ya zuba ruwa a bokiti sannan ya dauko soso da soap ya aje a gurin, ya bude gurin da kanwarsa take aje kayan amfaninta ya dauko sabon brush ya dauko brush and toothpaste ya zuba a kai ya mika mata, ta dade tana kallon abun sannan ta karba sai ta saka yatsanta ya kwashe toothpaste din da yake kai ta saka a baki ta lashe abun ta, ta hade sannan ta saka halshe ta lashe dan zaki zakin da take ji ya hana ta ji makakin da yake tare da toothpaste din, sai ta mika mata tana tande baki, abubuwa biyu suka zo masa a lokaci daya mamaki da kuma tausayinta a lokaci daya, ya mika hannu ya karbi brush din ya saka zuba mata wani sannan ya zuba wani a hannunsa yana nuna mata yadda zata yi, a maimakon ta saka brush din a bakinta sai ita ma ta saka yatsanta ya lakaci man ta saka a baki tana gogawa kamin ya goga yadda ya kamata har ya nuna mata ta zubar ita kan har ta hade nata, yana zubarwa sai ta tofar da yawu. Oh Allah Ya fada yana furzar da iskar bakinsa ya daga kansa sama, sai ita ma ta kwaikwayeshi sai dai ita bata ita furta abun da ya fada da kyau saboda ba yarenta ba ne. Oww Allah Ta furzar da iskan ta daga nata kan sama, zatonta yana nuna mata komai ne, be san lokacin da dariya ta subuce masa ba, sai ita ma ta yi murmushi, karbar brush din yayi ya aje sannan ya nuna mata ruwan dake cikin bokiti tana ganin ruwan sai ta bata fuska ta lake kafada domin ta yi arba da makiyinta. Sai ta matsa can baya ta rakube ta bata rai sosai. Ganin haka ya saka shi nufar kofar ya bude ya fito, a falo ya samu mahaifiyarsa a tsaye tana jiran fotowarsa. Ni kam ina cewa Allah yasa dai ba wanka zaka mata ba Yayi murmushi. Aa Maimoon zata taimaka mata ta yi wanka Maimoon ta nuna kanta cikin rashin jindadi. Ni kuma? Haba ki tausaya mata mana, bakonka Annabinka kuma iya yau ne kawai tun da gobe wucewa za'ayi da ita Ba dan ranta ya so ba ta mike tsaye sai daj Mamanta ta saka baki kuma yayanta ya hade fuska. Ki wanke mata kanta sosai, kuma ki kula da ciwon dake hannunta Yaya kamar wannan yarinyar za'ace ba zata iya yi ma kanta wanka ba? Wanka na ce ki mata? Ki taimaka mata ta yi nake nufi, idan kin wanke mata kanta sai ki fito ki barta ta yi wankan, kina ganin yanayin yarinyar nan kin san bata saba irin rayuwarmu ba, yanzu ba Brush na bata da man wanke baki sai ta lashe man Cikin Mamaki Hajiya Hajara ta ce. Ni ai tun da ka fada min cewar tana tsoron mutane na san akwai matsala, anya ba memory kanta ya samu matsala ba Bata yi yanayin da irin wadan nan mutanen ba, kuma ba su barta a asibitin ba balle a abincika kwakwalwarta ba, sai son tafiya suke da ita Abuja, ni tsorona daya idan ba tsafi za'ayi da ita ba, wata kila an ajeta a wani gurin ne aka koya mata rayuwar ta dabam, ko kuma an satota daga wani gurin ne, a yadda na fahimta su police din suna kokarin rufe maganar ne kawai, wata kila akwai manya a ciki, in ba haka ba mi zai saka a dauke ta a kaita can ba tare da ta ji sauki ba, idan har nema mata yan'uwa za'ayi ai sai a nema mata a inda yan'uwanta suke a nan ba tufafin jikinta ma irin na fata ne da aka ce a can da arna suna sakawa... Kamin Hajiya Hajara ta sake magana Maimoon ta fito tana fadin. Ihu take min kuma bata bari na taba kanta kuma Wallahi yayi datti da yawa sai an saka mata Clean Dr Shuraim ya juyo yana mata wani kallo mai kama da harara. Ina kika taba ganin an sakawa kan mutun clean? Sai kace kayan wanki Hajiya ta yi murmushi. Kar a taba mata kayana ko sai ka ce ke kike siya? Je bathroom dina ki dauko min shampoo and conditioner sai na rika miki mu wanke mata Ba musu ta juya ta koma sai Hajiya ta bi ta a baya, kamin ta kawo har Hajiya ta shiga Bathroom din ta tsaya tana mata kallon tausayi a kalaman Dr Shuraim cewar wata kila tsafi za'ayi da ita ya fi komai tsaya mata a rai, Maimoon ta kawo kayan sai Hajiya ta rikata ta yi mata irin na babba da yaro ta saka kanta a tsakankanin kafafuwanta Maimoon na zuba shampoo tana murza mata gashin dake a damke ana wankewa sau daya ta yi amfani da shampoo amman duk yawansa sai daya kare akan Waira, saboda dattin da kanta yake dauke da shi da kuma yawansa domin ya sauko har yama taba tile, duk yadda ta so ta kwaci kanta kasawa ta yi har sai da Hajiya Hajara ta wanke mata kan tass. Bata tsaya jiran komai ba ta kama rigar dake jikimta ta cire a nan suka tsaya kallon tufafin fatar dake a matsayin skirt dinta da kuma wanda ta yi riga da shi wacce ta tsaya mata iya kirji, da taimakon Hajiya Hajara Maimoon ta yi mata wanka wanka bana wasa ba, ba kuma daya ko biyu ba sau hudu suna murza mata jikinta soson yayin baki jikinta kuma yayi fari tass, hannunta mao ciwo ne kawai ba a wanke ba, shi ma iya bakin inda aka daure mata, kafafuwanta kuma Hajiya Hajara ce da kanta ta rike kafafuwan ta wankesu, ta saka abun gogewa ta goge mata dan abun da ba za'a rasa ba saboda rashin saka talkamin da take. Maimoon ta dauko tawul ta daura mata sannan ta janyo hannunta ta fito da ita, idonta yayi ja sosai saboda kukan da ci, ta yi ihu har ta gaji ta yi shiru dan kanta. Maimoon ta zaunar da ita saman gadonta a hankali sannan ta dauko baby oil din da take shafawa ta fara shafa mata a kafufuwa, babu yadda ta iya bayan mika wuya haka ta zauna kamar gumki Maimoon ta shafe mata jikinta ko'ina, sannan ta dauko hand dryer ta jona ta kunna, Waira