← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 165

Sashe 23

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 3 min read

one is for you Nimra ina fatar yarinyar ta mutu Har wani daga gira daya yake, ko kadan baya jin komai a jikinsa sai ketar da yake ta sakawa, jefar da rigar hannunsa yayi ya bude motar ya shiga be saka kafafuwansa ba sai da ya cire talkamin kafarsa ya shiga motar haka, daga shi sai wando jean jikinsa ba riga sai farar fatar jikinsa da kuma mazanta dake kara fitar da zatin fuskarsa. Kunna motar yayi at first sai ta tashi sai da ya yunkura zai yi reverse sai ta tsaya, ya sake kunna ta mutu ya sake kunna ta sake mutuwa har sau hudu, jimmm yayi yana tunanin yadda rayuwa zata kasance masa idan motar nan bata tashi ba, ba zai yi mamaki ba idan ta ki tashi domin ya ci uban motar, yadda ya rika buga motar da icen dake gurin sai da gabanta ya lankwashe, abun da be saba ba sai gashi yana addu'a da fatan Allah yasa ta tashi. And he got lucky motar ta tashi abun yayi hamdala ga Allah sai gashi yana fito ya juya kanta da karfi ya koma hanyar da shigo da motar yana gudu sosai kamar an biyo shi. Babu inda ya nufa sai hanyar da zata sada shi da Abuja, tunanin yadda zai yi idan police ko sojoji suka tare shi a hanya be zo masa ba sai yanzu. EID POV. Yana tsaye bakin kofar dakin da Waira take yana kallon cikin dakinta dake hargitse, he felt very bad domin shi ne silar guduwarta a garin, guduwar da bashi da tabbacin Sarki zai yafe mata ko kuma ya kasheta kamar yadda ya alkawaranta. Waira duk saboda kar ki yi kewa babu ranar da bana kasancewa tare da ke, miyasa zaki tsorata har haka? Akan me zaki karya dokar dake nufin rayuwarki? Ya kai hannu ya taba kofar dakin, kamin ya sulale kasa ya zauna a hankali, tun da ta tafi kullum a gurin yake zama, idan baya dakinta to yana a gurin da ta saba zama ta ci yayan itatuwa, ko kadan baya son yayi tsafi ya ga halin da take ciki domin zuciya zata iya debarsa ya bi bayanta bayan kuma Sarki ya kafa masa doka tun a ranar da ta gudu cewar kar ya bi bayanta. Ya daurewa zuciyarsa ya bi Umarni Sarki na iya yanzu da zuciyarsa zata iya dauka, kamin ya shawo kan Sarki ya sassauta hukuncin da zartarwa Waira tun gabanin ya san zata gudu. Wani irin azaba ya ji hannunsa na yi kamar an jefa shi a ruwan zafi, an cire na kara a wuta, da sauri ya saka dayan hannunsa ya rike dayan da yayi masa mugun nauyi dafin na shiga har wuce iya inda zugin yake. Iyakar juriya yayi amman sai da ya kai kwance yana dafe da hannu tsabar azabar da ya ji hannun na masa, yanayin yadda gurin ke masa zafi dafin na masa yawo ya gane cewar maciji ne ya cizi Waira, mikewa yayi tsaye rike da hannu ya daga kansa sama ya lumtse ido. Sai ga wahala masu zafi sun sauko masa, ba Hawaye ne na kukan zafin da yake ji ba na cizon maciji ba, hawayen tausayin Waira yake a wane hali take ciki? Ta ina maciji ya cijeta? Daman tun da ta gudu babu ranar da ba ya tunanin halin da take ciki da kuma abun da zata ci, ko a ina ta boya, duk be sani ba kuma bashi bukatar ya sani a yanzu. Waira Ya fada yana jin azabar tana karuwa, har yawun bakinsa sun soma canjawa, gumin azaba da wahala na karyo masa a goshi har ya rasa inda zai saka kanshi. Lokaci daya kuma sai ya ji azabar ta dauke masa. KhadeejaCandy
Chapter 23 · 0% Book details