← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 165

Sashe 26

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

har muryarta da idonta rawa yake duk sanyin falon sai da gumi ya kwankwasa mata kofa, tashin hankali yace baki ga komai ba sai a yanzu, gaba daya sai ta manta da tsoron fadin wanda ta bawa motar, furucin mahaifinta cewa an ga gawa ya fi komai daga mata hankali. Ameer na bawa motar Abiey gawar wa aka gani? Wane Ameer din? Sai a wannan karon Maleek ya saka bakinsa with confused. Ameer abokinka Ta amsa kai tsaye, a take Abiey ya sauke mata lafiyayyen mari sai da ta fadi kasa. Ta ina kika alakantu da shi? Miye hadinki da shi? Ina kika san shi har zaki dauki motarki ki bawa makiyin ana? Kin kyauta gashi yanzu an yi miki sakamako kuma zaki girbi abun da kika shuka Ummi ta yi saurin shiga tsakiyarsu hawaye na cika idonta, kafafuwanta suka fara juyawa kamar ba za su dauke ta. Ga.. Ga.. Ga...ga... So take ta tambaya gawar waye a motar amman ta kasa, saboda tsoro irin amsar da za a bata gashi maganar ma ta gagara fitowa. Mamaki ya hana Mahmood da Maleek cewa komai sai kallonta suke bama kamar Maleek. Abiey ya juya ya fice daga falon cikin wani irin fushi da bacin rai da ya dauki shekaru be ziyarce shi ba. Yana fita Ummi ta duka ta kama Nimra dake kuka. Ummi ban yi da wata manufa ba, ya fada min mahaifinshi ya koreshi kuma be san inda zai je ba, na bashi motata da kudi da ATM, amman ban san inda yaje ba, kuma ban aikata hakan da sanin cewar shi ne wanda suka yi fada da Ya Maleek ba, Allah ne shaidata ban sani ba Ummi Ummi ta rumgume ta tana kuka. Ummi ta amsa mata ta hayar daga mata kai alamar ta gamsu, sai dai zuciyarta ya samu rauni na rashin jin halin da Ameer yake ciki. Nimra ta dago ta kalli Maleek da ya kasa motsawa daga inda yake tsaye. Gawar waye a motar Ya Maleek? Kashe kansa yayi? Ko hadari yayi? Ina Ameer din yake? Sanin halin da Ameer yake shi yafi tsaya mata a rai sama da abun da aka zarginta da aikata, ji take idan aka samu gawar wani wanda ba shi ba abun zai zo mata da sauki, amman idan gawarsa shi ta wanne zata ji? Mutuwarsa ko zargin da ake mata? Gawar wata yarinya ce Maleek ya amsa mata, ita aka amsawa amman Ummi ce ta fi jin sanyi a ranta a take ta lumshe ido ta sauke ajiyar zuciya, kamin ta mike tsaye da sauri ta fice zuwa bangaren Abiey, ko da ta shiga ta same shi yana aikin saka sabon tufafi. Da gaske bari zaka yi police su tafi da ita? Abiey zaka iya kashe wutar nan daga nan gida ma ba sai an tafi da ita ba, Nimra macece be kamata a shigo har cikin gidan ubanta a kamata da laifin da bata aikata ba to miye amfanin dukiya da ikon Ubanta? Abiey ya juyo fuska a hade kamar garwashi ya kalli Ummi. To waya aikata? Miyasa kika goya mata baya ta aikata abun da ta aikata? Akan mi zaki shigar da yata a cikin lamarin rayuwar wani yaron can da bamu da alaka da shi? I warned you Zahra na fada miki ina son farinciki yayana fiye da nawa farinciki, sai dai na lura ke tashin hankali kike so, to ko hankali kowa zai tashi! Akan me zaki yarda ta bashi motarta da kudi saboda ya boya? A tunaninkin kin ni wayo? Na girgiza masa kai da sauri. Ba da sanina ta aikata ba? Idan zaki hade min Qur'ane ba zan yarda dake ba, kin fi kowa kusanci da Nimra kin san duk wani abu da take in and out. Enough is enough and lemme tell you something har abada ba zan taba amsar Ameeer a matsayin anki ba, ba zan taba son an makiyina ba, ba kuma zan taba son an da kika kaunar ubansa har yanzu ba, idan kika aikata kuskure rayuwar Ameer zaki jefa a hadari domin zai rasa gata ta ko'ina daga nan zaki gane kuskuren neman kusancin da kike da shi...! Tsaye ta yi a gurin kamar an dasata, duk wasu kalamai da zasu jefata a damuwa Abiey ya furta mata su akan rashin sani, kasa motsi ta yi har ya gama canja kayan ya saka babbar rigarsa ya fice daga dakin. Sai a lokacin ta samu juyowa tana tafiya kamar bata iya daga kafar, daker ta dawo bangarenta tana tafiya kalaman mijinta na zagaye duniyar tunaninta. Ba su dauka da gaske Abiey zai bar police su shigo har cikin gidansa cikin falonsa su kama yarsa ba sai da aka taba kofar ta yi kara ta sanar musu akwai baki a waje. Kowa ya kasa bude kofar daga Mahmood har Maleek balle kuma Ummi da Nimra ta tashi ta koma kusa da ita ta rike ta tana kuka. Da ido Maleek yayi ma Mahmood alama da yaje ya bude kofar, cikin karfin hali Mahmood ya isa kofar ya bude gabansa sai faduwa yake domin abun ne da basu saba ba, shigowa gidan ma police ba su isa su yi ba sai dan izinin da mahaifinsu ya ba su. Gaba tarda kansa police din yayi a matsayin jami'in tsaro sannan ya nuna masa arrest warrant. Maleek ya nufi kofar ya tsaya yana kallon police din ya ce. Motar ta ce kawai, amman abun da kuke zargi ba ita ta aikata ba, ni ma kuma ba da ganganci na aikata hakan ba, daga ita har ni zamu zo station yanzu nan, amman zaku ba mu police daya da zamu tafi tareda shi a motar gida Su sansu sun san inda suka shigo, hakan ya saka ba su masa musun abun da ya bukata ba suka amince, sai ya juyo ya dawo cikin falon ya kalli Nimra ya ce. Tafi ki dauko mayafinki, kuma duk tambayar da za ayi miki ki ce ni na karbi motarki Ta daga masa kai sannan ta tashi da sauri ta shiga ciki, fitowarta ya zama aiki domin gani take kamar idan taje ba zata dawo ba, na tsoron yan sanda take ba domin a masu gadin gidansu ma akwai police fushin mahaifinta take tsoro kar ya sa a yanke mata hukunci mai tsauri. Maleek ne yaja motar dayan police din yana front seat Nimra kuma na baya. Aka bar Ummi daga ita sai mai aikinta da ta gagara komai sai kallon ikon Allah take, da can bata san miya faru ba amman a yanzu ta fara fahimta akwai matsala a gidan. Wani dishe-dishe Ummi ta fara gani yana jin jikinta babu karfi ko'ina ya dauki ziza kamar jijiyarta ta yi majirya ga kanta dake sarawa, dafa kan ta yi tana wani tangadi kamar wanda ta sha kayan maye, Mahmood na ganin haka yayi saurin karaso ya riketa ya zaunar da ita mai aikinta ma ta karoso kusa da ita tana mata sannu, bata iya amsawa domin bata jin wani kuzari na magana ma balle motsi, sai dai hankalinta be gushe ba, wani kalar yanayi take ji a jikinta wanda ya banbanta da wanda ta saba ji, a duk lokacin da kalar rashin lafiyar ta ziyarceta. Mahmood kai ni daki zan kwanta Ya mike tsaye da taimakon mai aikinsu suka haura da ita sama suka kwantar da ita kan gadonta, Mahmood ya lullubeta da blanket sannan ya kashe Ac dakin ya fito ransa a jagule. Lumshe ido ta yiba dan bachi ba sai dan ta samu sa'ida, tana jin yawunta ya kafe sosai har ya haddasa mata bushewar baki, AMEER POV. Yana tsaka da wanke idonsa fuskar Waira ta yi masa gizo, be san lokacin da ya bude idon haka da kumfa ba, a take yaji ya shige masa a idon, a nan yaji wani sabon amai na taso masa yana ta jin kyankyami a jikinsa, tun da yake a rayuwar be taba wanka tara at the same time ba sai yau, ba wanka iya na sabulu ba har da na tsarki sai da yayi ba kuma dan yayi komai ba, sai dan ganin Waira da yayi da tabata da carpet din yake ji ba kamar ma har da wankan tsarki yana bukata saboda kazantar ta yi jawa wata kila idan be yi wankan tsarki ba zai iya jawa kansa matsala aki karbar sallah shi. Ya san yadda Hajiya Jamila take sakawa a tsabtace komai na dakinsa amman hakan be kwantar masa da hankali ya taba tawul din dake aje a bathroom din ba, haka ya fito ya nufi gurin da tufafinsa suke aje ya dauko sabbi fil ya saka sannan ya shafama jikinsa mai ya saka turare, talkami ya saka ya sauko fito daga dakinsa zuwa falon Hajiya Jamila tea ta fara tarbonsa da shi sannan ta zuba masa soyayyaen nama domin ya san yadda yake son naman da aka soya suya mai kyau, doya ta sarrafa masa da miyar kabeji wanda ta ji kaza, tun kan ta kawo masa abincin kamshi ya cika hancinsa. Lafiya lafiya ya fara cin abincin kamin ya tuna da kazantar Waira sai gashi ya tashi da sauri ya nufi bathroom din Hajiya Jamila cikin tashin hankali ta bi bayansa tana tambayar ko abincin ne be masa dadi ba ko kuma wani abun ya gani a ciki. Haka ta tsaya a bayansa tana kallonsa har ya gama aman ta kunna fanfo ta tara masa ruwa ya wanke bakinsa. Wani abu ka gani a cikin abincin ne? No inda na tafi ne na ga wata kazanta da ban taba gani a rayuwata ba Ina kaje Ameer? Wani daji ne, a KT Bedroom suka dawo, ya zauna ya labarta Hajiya Jamila duk abun da ya faru ciki har da motar da Nimra ta bashi and da reason din da yake ganin ya saka ta ba shi motar. A yanayin yadda ya bata labarin ta gama fahimtar bashi da gaskiya domin shi ya fara tsokanar abokin nasa amman tsoron bacin ransa ya saka ta kasa nuna masa sai tausarshi take kar ya aikata abun da zai zame masa matsala. Da ka yi hakuri ka kyaleshi Ameer idan ma ya ci amanarka zai gani a nan gaba, zalinci ba shi da kyau idan ka zalinci mutum komai
Chapter 26 · 0% Book details