← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 165

Sashe 6

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

gurin motarsa tana lekensa, kamshin turaren da ya ji ya banbanta da na shi ne ya sanar masar akwai wani bakuwar hallita a kusa da shi, a take ya daina busar ya bude idonsa a hankali, wani karamin yaki ya murza da idonsa da zuciyarsa dake mugun bugawa da karfi kamin ya samu nasarar kawar da idonsa a cikin kwayar idonta. Ya aka yi? Busa muka ji kana yi mai dadi Ta fada tana kallonta with smile on her face, shi ma murmushi yayi kamar ba shi ba, ya dan daga kafada sannan na sauko saman motar, ba tare da ya sake cewa komai ba ya bude motarsa ya shiga ya bar ta a gurin tsaye. WAIRA POV. Al'adarta ce yin rawa ko babu kida hakan ya saka ta sauko tsaunin da ta hau tana taka rawar kamar yar makada. Eid ya karaso gurin ya mika mata hannunsa ta rika ta karasa saukowa. Abinci zan ci yanzu Ta fada da yarensu, ya gyada mata kai. Mu je gida mu ci Lambu zan je Ta sake hannunsa ta nufi hanyar da zata sadata da lambun da gudu tana gudu tana tsalle har ta isa, bata bi ta kan yayan itatuwan da suke take akan itacecen ba ta fara daukar wadanda suka fado kasa tana ci, wani ma tsuntsaye sun ci shi amman bata damu ba take ci haka nan, ba tare da ta wanke ba sai dai wanda ta tauna da ji da kasa sai da zubar. Da kin wanke dai Waira Ta juyo da sauri domin ta firgita bata san da mutum bayanta ba, ganin Eid ya saka ta lake kafada daya ta fara yin baya baya. Atud shie Be ma'ana ba zata wanke ba, shi ma dai ya san fada kawai yayi domin bata da kyama ko kadan, kuma bata da tsabta ita da kasanza kamar twins ne, da za a bashi neman wani abu da Waira ta wanke shi kamin ta ci am ba shi babban aiki, komai kazanta guri zata iya kwana kuma ta tashi ba tare da ta wanke jiki ba, wannan ya saka dakinta yake cike da beraye da jajayen zakaru da wani lokacin ma a tare take cin abinci da su, basa tsoronta har rufa take dasu idan zata kwanta, berayen kam ta sha saka su a aljihunta ko a rigarta tana yawo da su. Tun abun yana damun Eid yana mata magana har ya gaji ya fara saka mata ido, domin ba zai iya canjata daga yadda take ba, haka kuma ba zai iya rabuwa da ita ba, kuma yawan yi mata magana yana saka su yin fada. Sai da ta ci yayan itatuwan ta koshi sannan ta samu guri a bakin magudanar ruwan dake lambun da zauna tana kallon yadda ruwan suke tafiya, Eid ya tsaya kusa da ita yana kallon ruwan shi ma, kamin ya shafa kanta. Zan tafi gurin Sarki, sai na dawo Ta daga masa kai ba tare da ta kalleshi ba har ya bar gurin, kwantawa ta yi tana kallon saman da gira gizai ba su gama wawayewa ba. ABIEY's HOUSE. Ta aje dankunne data cire a kunnenta saman mirror sannan ta juyo tana gyara rigar bachinta, Abiey dake kokarin rufe kofar bathroom ya kalli matarsa, da fuskarta ke bayyana damuwarta karara. Lafiya? Zaunawa ta yi gefen gado, sai ya zo kusa da ita ya zauna, a kan kananan kitson dake kanta ya fara sauke ido sannan ya kalli fuskarta. Bana son gani damuwa a tare da ke, Zahra ko abu be taka kara ya karya ba sai ki dauke shi ki saka a rai, yanzu kuma me aka yi? A gurin ka wata kila ba wani abu ne ba, amman ni na san abun da nake ji, kullum cikin jarabawa nake Abiey, kamin na same ka na sha wahala na fuskanci bakinciki na yi kuka kala kala, bayan na aureka na dauka damuwata ta wuce na dauka zan dauwawa a farinciki ne, sai dai daga lokacin da Maleek ya fara girma ya tsane ni sai na gane damuwa ba zata kyale farinciki ya zauna shi kadai ba, ina ganin kamar kiyayyata ce ta saka Maleek ya tsani mata gaba daya To me kika masa da zai tsane ki? Wannan wace irin magana ce? Kin tana ganin a ya sani uwarsa? Ta juyo ta kalleshi hawaye na zirya a fuskarta. Wata kila saboda abun da na aikata ne, hakki ba zai bar ni ba Abiey, na ha'inci wasu kuma na cutar da kaina Ta fashe da kuka mai karfi, ajiyar zuciya Abiey ya sauke ya dafa kafadarta yana girgiza ta. Ki cire wannan a ranki, babu wanda kika ha'inta, Maleek ma zai daina komai yana da lokaci ai, dan Allah ki daina kukan nan Babu abin da ke da ke da bakinciki kamar an ka yana cikin damuwa ka fuskanci ka tambaye amman ya kasa fada maka, Abiey ni fa uwa ce ni kadai na san zafin da zuciyata take min Ta fada tana nuna kanta, mikewa yayi tsaye ya fito daga bangarensa ya shiga bangaren matarsa, sai ya samu Mahmud zaune tare da kanwarsa yar'uwarsa Namra. Daddy Nimra dake kofar kitchen rike da cup ta fada tana kallonsa, sai duk suka juya suka kalleshi domin ba su san da shigowarsa falon ba, gaishe shi suka yi, ya amsa da murmushi a fuskarsa. Ina Maleek? Yana akinsa, Daddy ai kasan idan mu nan falo ba zai zauna ba Be ce musu komai ba ya nufi upstairs, cikin natsuwa ya tura kofar dakin dansa ya shiga sai ya same shi zaune yana karatun kur'ane gaba daya ya cika dakin da muryarsa mai dadin sauraro. Abiey ya karasa ya zauna akan kujerar dake kusa da inda ansa yake zaune saman carpet, Maleek na ganin haka ya rufe qur'ane bayan ya kai ayar karshe. Abiey... Maleek karatu ake yi? Yayi murmushi ba tare da yace komai ba. Hakan yana da kyau ai, Allah ya kara basira, Umminku ta fada min kana da damuwa, sai kuma na zo na tararda kai rike da abun da ke kawar da damuwar, kusa da mai kawarda damuwar, sai dai duk da haka ba zan ki mu tattauna matsalar ba Maleek ya sake fadada fuskarsa da murmushi mai kyau ya gyara zamansa. Abiey gashi kai ma ka fadi, damuwa ai ta wuce saboda hada ta da mai iko da ita, kuma daman ba wani abun ba ne, fada ne kawai muka yi da wani friend dina shiyasa na dawo gida rai a bace, ita kuma sai ta dauka ko wata babbar matsala ce Ka tabbatar ba matsala ce ba? Babu wata matsala Abiey, kawai akan yayi min maganar mata ne ni kuma rai na ya bace na yi masa abun da be dace ba, wanda na ji ba dadi bayan yi masa haka, amman abun ya wuce Sai da na raya wannan a raina na san ba zai wuce akan wannan issues ba, amman a rika kiyayewa be kamata kana samun matsala da abokinka ba, su ma kuma ka fahimtar da su rayuwarka so that's kowa ya ya daina taba kowa In Shaa Allah Abiey ya shafa kan ansa sannan ya mike tsaye. Allah ya muku albarka Ameen Ya amsa yana kara jin kaunar mahaifinsa. ___________________ Wace kalar ramuwa kuke tunanin Ameer zai yi? Su Waira manya, team kazamai ku zo ku dauki yar'uwarku ...WANI GARI... _Na Khadeeja Candy_ Daga inda take kwance gindin ruwan ta hango yara suna hawan bishiya suna tsinkar yayan itatuwanta, kamar an cikareta haka ta tashi tsaye da sauri tana kallonsu, daman can babu abun da ta aje a ranta sai keta da son azabtarwa, itacen dake kusa da ita ta kama ta hau fir sai gata ta dale kan itacecen haka ta rika bin itacen tana sauka saman wannan ta hau wannan har ta isa gurin da yaransu, bata tsaya yi musu cewa su sauko ko su daina ba, saboda tana da hurumin hana su domin itacen ba na gidansu ba ne, ko da na gidansu ne bata da wannan damar balle na wajen gidan. Sai da ta kalli yaron da ta fi girma ta turashi da karfi ya fadi kasa, sai ta fara dariyar mugunta haikam, sauran yaran na ganin haka suka sauka daga kan itatuwan suka ranta a ana kare suka bar yaron daya fado kasa yana ta ihu da neman ceto. Mikewa ta yi tsaye saman itacen ta tsinki ganyensa da wani gafe na reshen itacen ta fado tun daga kan itacen zuwa kasa ta tsaye, ta nada itacen da ganyen ta dora a kanta sannan ta dauki fruit din daya fado ta fara ci tana yamutsa fuska saboda tsami, hango mutane tafe ya saka ta gudu ta boye a bayan wasu itatuwan tana leke har aka dauke yaron, sannan ta zauna a gurin tana ta dariya. Daga zama sai gata kwance ta daga kafafuwanta sama ta jingina su da itacen tana kallon sama, labarin da Eid ya bata take tunawa, akwai wasu mutane masu abun hawa da rayuwa da ba irin na su ba, abincinsu da yarensu da addininsu ba irin nata ba. Kuma suna jin dadi rayuwa? Ta tambayi kanta da yaren da shi aka haife ta kuma shi ta iya, zuciyarta ta raya mata babu wani jindadi ga wanda yake rayuwar da ba irin ta su ba, a gurinta hawan tsaunuka da itace da manyan duwatsu ya fi komai dadi, ka shiga lambu ka tsinki abun kake so ka ci ya fi komai saka nishadi. Outarrr Ta maimaita tana dariyar sunan da ya fada na abun hawansu Mota take kokarin iyawa. Kamar daga sama ta ji muryar Eid, da sauri ta tashi zaune tana kallonsa har ya karaso. Tada ita yayi tsaye ta cire mata ganyen data saka a kanta ta jefar ya rike kafadunta. Me kika aikata? Ban yi komai ba Ta bude hannayensa zata tafi ta dauko ganyen ya riketa. Sarki yace a zo da ke, kin jefar da yaro A take ta saka dariya, duk kuwa da kasancewar bata ga wasa a fuskarsa ba, sai dai ta san ba a yau ta saba irin wannan ba kuma kowa be tana ce mata komai ba, sai dai Eid yana yawan nuna mata abun da take yi ba shi da kyau, yana daga
Chapter 6 · 0% Book details