← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 165

Sashe 42

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuma wanda ya mareta yayi yanayi da wannan. A take ta fashe da kuka jikinta na rawa sosai hakan ya saka Mahmood be karaso kusa da ita ba ya tsaya daga bakin kofar ya juya ya fadi cewar Tsorona take fa, wata kila ta dauka Maleek ne Ya juyo yana kallonta yayi mata murmushi, gaba daya sai ta kara rikicewa ta boye fuskarta, har sai da ta ji muryar Ummi sannan ta dago, Ummi na kai hannu ta tabata sai ta mike tsaye da sauri ta rumgume Ummi jikinta na bari sosai. Mahmood fita tsoronka take Mahmood ya juya ya fita, sai Ummi ta zaunar da ita a kasa ganin ta fi son zaman a nan ita ma ta zauna. Da a ce a fito dake falo ki zauna tare da mu ne, baki so? Bakin Ummi kawai take kallo tana son fahimtar abun da take fada mata, na kurame Ummi ta yi mata alamar mari ta a fuska ta sake yi mata alamar ba za a sake ba tana mata murmushi sannan ta kwantar da kanta a kafadarta ta dan kauce fuska saboda wari da bakin Waira yake. Gobe za a tafi dake asibiti a duba lafiyarki da hannunki, da kuma bakin nan da kika ji ciwo dazun, Allah yasa ki ba mu hadin kai Ummi ta fada, sai Waira ta lumshe ido ta ji wani yanayi da bata taba ji ba, domin ita ma bata san dadin uwa ba bata san dadin wani yayi mata haka ba, ita sam bata san dadin wani ya rabi jikinta ba sai Eid shi ma kuma iyakarsa rike hannunta ko daukarta idan ta kama, a rayu a inda take kwana ita kadai a dakin babu uwa ba uba babu yan'uwa sai beraye da zakaru... NIMRA POV. Tun da ta yi sallah Magariba bata fita dakinta ba har aka gama Isha'i sannan ta gabatar Sallah Isha'i ta yi shafa'i da wuturi, ta sauya tufafin jikinta zuwa na bachi, sannan ta fita dakin ta sauko downstairs, ta zuba abicin da ta san zata iya cinyewa ta dauki spoon da cup ta bar dinning. Daki zaki ci abinci? Namra ta tambaya ganin ta fara sabon halin da ba nata ba. Wai sai fushi kike da mu sai ka ce mu muka miki wani abu a gidan, ina ce Abiey ne kawai yake fushi da ke a gidan nan amman sai wani kebe kanki kike kamar kin ga makiyinki Dazun saboda ni yarinyar nan da aka kawo ta rumgume Ya Maleek me kike tsammani idan yayi arba da fuskata Namra ta tashi zaune fa kyau tana kallon Nimra da matukar mamaki, domin bata nan komai ya wakana a gidan, tana gurin aiki daga gurin aiki kuma ta wuce gurin Gwaggonsu bata dawo ba sai da Isha'i. Ta rumgume shi fa kika ce? Kamar ya? Ita yarinyar ta san shi ne No tsoro ta ji, na je ina nemanta ita kuma ta fito da gudu kamar mahaukaciya ta rumgume shi, kin ga marin da yayi mata sai da bakinta ya cika da jini Yana ina shi? Oho kila ya fita daga gidan Yarinyar fa? Tana dakin dake kusa na shi Tab... Nimra ta haye sama da abincin ta shige daki ta rufe ta aje tuwon akan carpet tare da ruwa, sannan ta zauna ta fara ci, ta dan ci da yawa domin rabon da ta ci abinci mai yawa haka tun da aka fara tashin hankalin nan ita ma ta shiga a damuwa abincin ma ba ya mata dadi sai abu mai ruwa. Brush ta yi bayan ta gama ta dauke plate din ta dora akan karamin tebur din dake dakin, ta hau gado ta kunna data. Misalin Sha daya na dare sakon Ameer ya shiga mata ta Instagram a take ta tashi zaune jiki na rawa ta fara amsa masa, a cikin kalaman da take aika masa har da wadanda take ganin be kamata ta tsaya tana masa magiya haka ba, amman ta kasa ganin illar hakan har sai bayan da ta riga da tura, tashi ta y zaune tana tunanin yadda zata yi ta bincike abun da yake cikin motar har ta sani idan akwai sarewar Ameer a ciki. Fitowa ta yi dakin ta nufo downstairs kamar zata sauko sai kuma ta fasa ganin Namra na zaune a falon a har lokacin sai ta nufi dakin Ummi, knocked ta fara yi sannan ta tura ta shiga babu kowa dakin, juyowa ta yi ta dawo ta nufi dakin Waira domin ta fi kyautata zaton Ummi tana can tare da ita, a nan ma sai da ta kwankwasa sannan ta tura ta shiga. Ummi kina nan har yanzu? Ta tambaya da mamaki, Ummi ta kalleta. Yarinyar nan bata son na daga da zarar na motsa sai ta tashi ta rike min hannu, wata kila tsoro take ji har yanzu ko kuma tana kewar mahaifiyarta ne Ummi sai ki biye mata, ki zauna tare da ita har tsawon wannan lokacin Ta sakw fada yayin da ta karasa kusa da ita ta duka. Sai Ummi ta kai hannu ta shafa fuskar Nimra. Zan tashi, nima na jidadin zaman ne, ina ta jin kewarku kuma lokacin da kuke da kurciya kamar ita haka kuke yawan rabar jikina Har yanzu ma ai ba mu daina ba, kuma ba za mu taba girma da hakan ba Ummi ta yi murmushi sannan ta cire hannun Waira a hankali ta aje kasa ta mike tsaye, da sanda suka fice daga dakin ita da Nimra saboda kar ta farka. A bakin kofar dakin Nimra ta fara yi Ummi tambayoyi. Ummi an bincike motar kuwa? Ina tunanin police din sun yi bincike ai, ba su koma ba ma sai gobe za su kama hanya tun da sassafe Kuma ba su ga komai a motar ba? Da sun gani da sun fada ai, mi yasa kika tambaya? Ta dan hade yawu tana tunanin irin amsar da zata bawa Ummi. Akwai a motar wanda na siya few days before abun ya faru kuma akwai ATM dina da waya a motar ina tunanin ko Ameer ya bar su a ciki Sarewa kuma? Ki yi me da sarewa ke ba namiji ba? Zan tambaya Abieyun ku na ji idan akwai a motar Idan kuma babu Ummi ki karba min key din na duba da kaina Okay Ya juya ta nufi hanyar dakinta, Ummi ta bita da ido tana karantarta, domin ta ninka a kiriniya lokacin da take da kurciya, tunanin Ummi dole sai dara nata saboda ita uwa ce kuma ta bata shekaru masu yawa, a take zuciyarta ta raya mata sarewar ba ta ta ba ce, sai dai bata nuna mata hakan ba kuma bata ce mata komai ba har ta shige dakinta. Ajiyar zuciya ta sauke ta taka zuwa kofar dakin Maleek ta tura ta shiga, hango shi kwance saman gado ya daga mata hankali cikin kulawa ta shiga dakin ta karasa har gurin gadonsa ta kai hannu ta bude blanket din da ya rufa da shi ta taba jikinsa ta jishi da zafi sosai kamar an kara a wuta. Subhanallahi Ya bude ido da sauri ya kalleta, sai yayi hanzarin tashi zaune yana kallon agogon bangon dake dakin, tun da ya kwanta bayan gama Sallah Magariba be sake farkawa sai a yanzu da hannu Ummi ta taba jikinsa. Baka da lafiya ne? Ummi ta tambaya, sai ya kai hannu ya taba jikinsa. Ba sosai ba Ya mike tsaye ya nufi bathroom, Ummi na zaune har yayi alwala ya fito ya nufi inda carpet yake shimfide ya tada ikama ya fara Sallah. HUMAIRA POV. Sai da ta taso daga makaranta sannan ta wuce gurin aikinta, daman ta kan yi hakan shiyasa ta fi kaunar duty dare, idan kuma har tana da duty rana kuma ga karatu wani lokacin suka yin canjen aiki ita da abokan aikinta, wani yayi amfani da lokacinta ita kuma idan ta dawo sai ta dauki lokacinsa, a haka dai take ta kai da kawo na ganin sun yi survive ita da iyayenta, ba abu ne mai sauki a gareta ta hada abu biyu a lokaci daya ba, kamar aikin Restaurant da kuma karatu da yake bukatar lokaci sosai, sai dai rashi da neman abun dogaro da kai ya saka a dole ta sabawa kanta da wannan wahalar har ya kan zama idan bata je aikin ba bata jindadi, kuma bata isa ta jefar da karatun da makomarta da na iyayenta yake ciki ba. Washe garin data dawo kowa sai tambayar ya fuskarta yake, wadanda suka samu labarin abun da ya faru daga baya kuma suka jajanta mata, ba sosai suke ake baki suna zaginsa ba, saboda akwai Security Camera tsoron suke kar su zure da yawa a duba Camera a gani su ja kansu matsala. Ita kanta da fargaba ta yi aikin na yau tana ta tsammanin ganin takardar kora daga mai gurin ko kuma ansa dan gadara bata ga ko daya ba har ta gama duty ta direban gurin ya kaita gida. Khadeeja Candy Copyright 2023 *W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660* Washe gari bayan gama Sallah Asuba Ummi ta shiga dakin Waira ta same ta zaune ta kasa ta takure guri daya. Kin farka? Ni ban san sunanki ba, ban kuma taba jin maganar ki ba, balle na fahimci yarenki ma Waira dai kallonta kawai har ta karaso kusa da ita ta zauna saman gado ta kama hannunta a hankali ta duba. Sannan ta rika ta ta mikar tsaye tana mata alama da ta tashi su shiga bandaki, bata yi musu ba, domin ita ma kanta fitsari ya cika mata mara kuma bata son shiga bandakin da take masa kallon ya fi dakinta ma ta yi fitsari, yadda kofar za ta yi kara idan aka tura ko rufe take tunani, Ummi ce ta bude mata ta shiga kamin Ummi ta yi mata alamar komai ta risina kasa ta juya baya ta saki fitsari a nan, ganin hakan ya saka Ummi ta yi saurin juyawa ta fice daga bandakin. Ba ta saba yin tsarki bayan fitsari ba hakan ya saka bata yi tsarki ba ta mike tsaye taja wandonta sama ta juyo ta fito. Duk yadda Ummi ta yi juyim duniya
Chapter 42 · 0% Book details