Sashe 61
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
kai aya Ummi bata ce masa komai ba, sai sauraren muryarsa take wani bakinciki na bude mata sabon feji, hannu ta mika ta taba ginin dake bayanta ta jingina a hankali ta lumshe ido. Can kuma ta bude idon tana ta kallon number da ta yi appearing a truecaller da sunan Ameer. A yau anta ya kirata, amman ba kira na sanin cewa ita mahaifiyarsa bace, ba kira nw irin an a da uwa ba. Sakon address inda suke ne ya biyo bayan kiran da yayi mata, ta mike tsaye har lokacin hawaye take, ta kasa tsayar da kuka kuma ta kasa saka hannunta ta share, saukowa ta yi downstairs ta nufi gurin mijinta, tana shiga falon sai ta samu Maleek da Abiey zaune da alama wani abun suke tattaunawa, sai dai shigowarta ya saka sun maida hankalinsu a gurinta. Nimra bata gidan nan Kuma..? Maleek ya fada da mamakin wani irin hali yar'uwarsa ta daukarwa kanta. Ta gudu ta tafi gurin Ameer, ya kira ni a yanzu ya fada min inda zan same ta Abiey ya hade wani kwalolon bakincikin da ya tsaya masa a makoshi. Ina daf da yafe yarinyar nan... Ba zaka iya ba Abiey, ka fi kowa sanin yadda ake ji idan iyaye suka juya baya, ko ka manta abun da ya faru tsakaninka da Mai Martaba? Ba zaka aikata hakan ga marainiyar da uwarta ta tafi ta bar mana amanarta ba, da ace ta saba aikata maka hakan sai ka ce ka gaji amman bata saba ba, kuskure aka samu ya kamata ka duba mata Abiey, ni bazan iya juyawa yata baya ba Ta juya ta fice daga dakin, da gudu ta iso bangarenta tana kuka ta shiga ta dauki hijan dinta ta saka ta dauki makullin motarta ta fito da saurinta ta sauko kasa. Tana fitowa waje sai ta samu Abiey Maleek sun data mota ita kawai suke jira. AMEER POV. Ameer ya aje wayar yana matukar jin tausayin halin da ya jefa Nimra, be taba sanin abun da yake aikatawa be kyautu ba sai a yanzu da ya firgita yar mutane ta fita daga hayyacinta. Bama kamar data fito daga bandakin yana kallon fuskarta ya san samun damar kebe kanta ta yi kuka ne kawai ta yi amaimakon wanke fuskar da yace ta yi, yana ta kallonta har Humaira ta zaunar da ita a kujerar da take zaune a dazun, wannan karon tausayine a fuskar Humaira ba kamar dazun ba, bata san abun da ya faru ba, amman yadda ta ga jikin Nimra da kuma kukan da take ya saka jikinta yayi sanyi tana jin tausayinta. Zaki iya cin wani abu na kawo miki? Humaira ta tambaya, sai Nimra ta girgiza mata kai alamar aa. Humaira ta kalli Ameer dake kallon Nimra. Ban san miya faru ba, ban san damuwarta ba, amman ka sani idan kai ka cutar da ita Allah ba zai barka ba Ta fada idonta na cika da hawaye, kallonta Ameer yayi yadda take iya fada masa magana ba tare tsoro ko fargabar abun da zai mata ba abun har mamaki yake ba shi, shi kam a rayuwarsa be taba haduwa da tsagera ba irin wannan yarinyar, ba dan ta samu damarsa ba har yaushe zata kalli tsabar idonsa ta fada masa cewar idan shi ya cutar da yarinyar da bata da alaka da ita Allah ba zai barshi ba, sai dai ta ayan bangaren kalaminta ya sanyaya masa jiki domin duk wani mai imani da tausayi idan ya ga yadda Nimra take zubar da hawaye dole ya tausaya mata, musamman ma shi da ya san silar kukanta da kuma halin da ya jefarta. To yar iya na gode sai ki koma gurin aikinki Ta watsa matsa harara kasa kasa, tana zaginsa a ranta dan dai ba zata iya fada a fili ba. Bakin Azzalumi macuci, shaidane mai karyar arziki, Allah kadai ya san abun da ya kullawa yarinyar ya yaudare, ita kuma ta fi kyau da kudi ta cutar da kanka, waya sani ma ko ciki yayi mata, dan iska dan kasan wuta... Da wani shegen hanci na shi kamar tattasai, kai kamar ganwon albasa Tana tafiya tana zaginsa a ranta, tana ayyana da ace ita ya cuta sai ta karya masa kafa ya zama gurgu. Ameer mu tafi yanzu Okay amman akwai wanda nake jiran ya kawo min sako zan dan jira shi minti kadan Sai a lokacin ta fara jin ta tsargu sboda babu mayafi a jikinta kuma babu talkami. A da idan zata shigo gurin sai ta saka mask da glass saboda kar wanda ya santa ya ganeta. Dan karamin veil Humairah ta kawo mata tare da gorar ruwa mai sanyi. Karbi wannan ki rufe kanki Ta kalli Humaira sannan ta mika hannu ta karba, ta lulluba, Humaira ta mika mata gorar ruwa. Ba zan iya sha ba, bakina ciwo yake Ta nuna mata bakinta dake kumbure. Wayyo sannu Allah ya isar miki Ameer ya kalli Humaira da sauri ganin tana zakalkalewa. Ga wa? Ga wanda ya cuceta mana, daman mace rauni ne da ita wasu mazan suna amfani da haka su cutar da ita, kuma idan mutum ya san be yi cuta ba miye ruwansa da Allah ya isa Wata uwar harara Ameer ya watsa mata, ba dan yana a yanayin da baya son biye mata ba, da sai ya gaura mata mari a gurin ko ta shiga hankalinta, domin ya kura bata tsoronsa sam kuma bata kunyar fada masa magana, sai dai baya a cikin yanayin da zai biye m ata su siyar da hali a gurin, dan haka ya dauke idonsa yana kai zuciyarsa nesa ya tattara hankalinsa ya maida gurin Nimra. Ganin hakan ya saka Humaira ta juya rike da gorar ruwanta ta koma a iyakar gaskiyarta take neman Allah y isarwa yarinyar da zuciyarta ke raya mata Ameer cutar da ita yayi, ko da yake ta ayan bangaren tana ganin kamar har da laifinta taya za'ace duk wakar nan da take mata idan suka zo gurin bata dauki haske ta gane Ameer yaudararta zai yi ba, saboda yawan taba ta yake ta kyale shi yana shiga jikinta gashi yanzu har ta kai yayi mata duka kuma ya dauko sun ta zo gurin babu ko mayafi a jikinta babu talkami. Ameer na ganin kiran number da ya kira ta Ummi dazun ya fahimci sun iso gurin, sai ya yanke kiran ya aika mata da sako daidai inda zata tsaya ta jira shi. Sannan ya kalleta ya ce. Tashi mu tafi Gudun kar ya rikata su fita tare mahaifiyarta ta gani ranta ya bace sai ya nemi Humaira ta rika masa ita suka fito yana gaba Nimra dake dafe da Humaira tana bayansa, sai da suka iso gurin motarsa da yayi parking sannan Ummi ta bude motar da facing din ta su ta fito tana kallonsa kamanin da ta gani a fuskarsa da jikinsa sun matukar daga mata hankali zuciyarta sai rawa, ita kadai take masa kallon tausayi da kauna, Abiey da Maleek kuma suna matsa kallon tsana daga cikin motar kamin su bude su fito. Nimra na ganin iyayenta sai hankalinta ya tashi ta fashe da kuka. Ameer kaika kira su? Ya juyo ya kalleta. Ba zan iya bari ki aikata kuskure nan ba Nimra Ba kai ka fada min zaka iya mutuwa a kaina ba? Hakan baya nufin na cutar da ke a yanzu, ba ki san abun da yake kasa ba Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Ta fada tana runtse ido. Maleek da Abiey suka iso gurin da suke tsaye Ummi kuma ta kasa karaso sao kallon Ameer take. Abiey ya kai hannu ya fisgo Nimra daga hannun Humaira ya tsinka mata mari sai da wutar kanta ta yi daukewar wucin gadi. Sannan ya kalli Ameer cikin bakar fuska ya ce. Babu kai babu jinina, babu kai babu zuri'ata, babu kai babu iyalina... Ya juya ya nufi motarsa yana jan hannun Nimra da karfi, ita kuma da yake bata da kunya sai kiran sunan Ameer take, har mutane suka fara lura da abun da ke faruwa. Allah ne kadai ya tsare Ameer be fadawa Abiey bakar magana ba, domin babu mai fada masa magana marar dadi be rama ba, sai dai tausayin Nimra da son nema mata sassauci ya saka be furta ma Abiey komai ba, sai kallon Ummi dake tsaye tana hawaye yayi daga inda yake yake fadar. Wata kila kin taba yin so a lokacin da kike da kurciya, ban sani ba ko kin san yadda yake da zafi da rikita zuciya, CIWON SO yana da wahala da dimauta mai yinsa, mutum kan fita hayyacinsa ya aikata abun da be dace ba, dan Allah ki dubi Nimra da idon rahma, wanda be taba so ba idan ya samu ba zai fita akin son da sauki ba, karki bari mijinki ya cutarta da ita dan Allah. Bata watsar da tarbiyar da kuka mata ba, duk abun da ya faru ba laifinta ba ne laifina ne... Each and every words da ya furtawa Ummi sai ta ji kamar magana yake jefa mata, gaba daya duniyar ta juye mata upside down. Maleek ya tabe baki yana kallon Ameer da tsarki. Nice one Ameer kai kake furtawa Ummi wannan maganar saboda da baka da kunya kuma baka da mutumci? Ameer ya matsa kusa da Maleek yana furzar masa da numfashi da karfi tare da saka hannayensa aljihu yana kallon cikin idonsa. Saboda bana da uwa a raye ba shi yake nufin van san darajar uwa ba, kai kuma baka san miye soyayya ba, baka san CIWON SO ba, saboda haka be kamata ka tsoma rubabben bakinka ba, baka san komai akan masoya ba dan haka karka sake karanbanin shiga a abun da ka zahilta, zan raga maka ne kawai saboda Uwa... Ameer ya daga hannunsa ya nuna Ummi dake tsaye, suna kallon kallo akuya kallon kura shi da Maleek. Maleek yayi kamar ya fada masa magana sai kuma wata zuciyar ta hana shi ya juya yana huci da jin acin maganar da Ameer ya fada masa ya nufi motarsu. Wayyo Allah zuciyata... Ummi ta fada tana kai hannu ta dafe zuciyarta, Maleek ya rikata da sauri ya saka a back seat inda Nimra take zaune ya rufe motar sannan ya bude front seat ya