← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 165

Sashe 59

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

maida kofar akin dakw bude ya rufe ya saka mata key. Khadeeja Candy Copyright 2023 Nimra i thought mun rufe babin Ameer tun a lokacin da kika bashi aron motarki Maleek ya fada bayan rufe motar da yayi. Kuka kawai take ta kasa cewa komai. Tun a lokacin Abiey da ni da Ummi mun nuna miki ba mason wata alaka tsakaninki da shi, ko dan mu ya kamata ki nisanta kanki da shi, kin manta bacin ran da kika saka mu a wacan lokacin ne? Ban manta ba, ban kuma fada soyayya da shi akaran kaina ba, ban yi soyayya da Ameer Saboda zuwan wannan ranar da zan bata muku rai ba, ban san miyasa kuka tsani Ameer da yawa ba, kamar wanda ya kashe muku wani Baki san waye Ameer ba ne Nimra, duk mai kaunarki zai so ki auri mutumen kirki, I'm not saying Ameer ba shi da kirki no, mutum ne da wani be isa ya saka shi ko ya hana shi aikata abun da yake so ba, and i don't think ma yana kaunarki da gaske saboda mun hada jini da ke, and i know ya fi tsanata da kowa a yanzu Ya karasa bakin gadon ya zauna. Zai fi kyau ki hakura ki cire shi a ranki, saboda iyayenki basa so, kalli abun da ya ja miki a yanzu, and kin manta yadda ya batawa iyayenki rai lokacin da kika ba shi motarki? Da ace Abiey be yi nasarar rufe case din nan ba, ko kuma ace yarinyar nan gawa ce aka samu a motar baki san iya abun da hakan zai haifar miki ba Ameer be ja min komai ba, shi kullum neman yake a bashi dama ya sanar da iyayena cewar yana kaunata, amman saboda tsoron abun da za ku fada ya saka na boye soyayyarmu, har hakan ya faru amman Ya Maleek ina son Ameer idan kuka raba ni da shi zan iya mutuwa... Indai har baki mutu kamin ki sanshi ba, to ba zaki mutu saboda kin rabu da shi a yanzu ba, Ummi kuka take saboda abun da kika aikata Nimra, ta samu rashin fahimta da Abiey duk saboda ke baki ji kunya ba? Har kike iya fadar zaki mutu idan kika rabu da shi, da shi ne na tabbatar zai iya rabuwa da ke a take Shi ma ba zai iya ba, yana so na tsakani da Allah ne, ya hade soyayyar masoyi da ta an'uwa da ya kasa nunawa yar'uwarsa shi ya nuna min, kana cewa na rabu da shi saboda baka taba so ba Ya Maleek wani digo be taba dirar maka a zuciya da sunan soyayya ko kauna ba, ba san miye a cikin shaukin son ba, saboda ka kasa rabar kanenka mata ma balle ka nuna musu so, baka taba yin budurwa ba, idonka be taba duba wata mace da rahma ko tausayi ba, balle kuma so! Wallahi Ya Maleek na shiryawa karbar ko wane kalar kalubale akan Ameer, idan ba har kuna da wani matsala da shi da dabam ba, be kamata fadanku ya taba soyayyar mu ba, idan har kasan zafin rabuwar uwa da a, to haka rabuwar masoya take, amman kai ba zaka gane ba saboda baka taba ana zakinta ba, da gaske nake Ya Maleek idan kuka Ameer mutuwa Ya ji wata yar iskar yarinya yaushe kika san Ameer din ma, da zaki fada min haka? Okay idan har Abiey zai yarda ki aureshi ko Ummi sai ki aureshi din, amman idan suka nuna basa so, ba zaki aureshi ba, ki rubuta wannan ki aje Ya mike tsaye ya juya. Saboda baka san me ye so ba Ya Maleek, aure zamu yi ba zaman banza ba A fusace ya juyo ya daka mata tsawa. Yanzu me kuke yi? Ke ce baki san waye Ameer ba Nimra amman ni na san Ameer in and out, na san abun da zai iya da wanda ba zai iya ba, da ace sonki yake da gaske, da ya sauke gabar da yake da ni dan shi ne ba shi da gaskiya, amman a halin yanzu Ameer ya bata da duka friends din mu saboda ni, idan na zauna a guri Ameer ba zai sake zamansa ba, idan na gaisa da wani Ameer ba zai sake magana da shi ba, taya zaki kalli idona ki fada min cewar Ameer da gaske yake son ki? idan ban soyayya ba ai na san hankali da tunani, don't you think yana amfani da ke ne kawai saboda ya bata min rai? Ameer baya yafiya, Ameer baya aje burinsa saboda wani, ba ya kashe kansa saboda wani ya rayu, ya sani duk ranar da na san yana soyayya da kanwata zan yi bakinciki wannan ma kadai abun farinciki a gurinsa, and i know one thing for sure Nimra, Ameer ba zai ajeki a gidansa for more than one year ba tare da ya taba ki ba, ko dan kasancewar ki kanwata zai aikata miki komai, and bari na fada miki wani abun da baki sani ba, Ameer yana da mistress ya ajeta a wani gidan na dabam you're not the only one wannan kadai be isheki abun kunya...? Ameer ba shi da kowa sai ni, kuma ni Ameer ba taba min komai ba, saboda so na yake da aure, baka fahimce ba ne Ya Maleek, ka bude zuciyarka ka zuba mata tausayi da soyayya, ka zahilci so... Da mugun mamaki Maleek yake kallon. Ina fada miki gabas kina fada min yamma? Saboda an kyale ki? Baya son saka hannunsa dan haka ya nufi gurin Laptop dinta take ya fisgo carjar ya nufi Nimra da ita ya fara dukanta kamar an aiko shi, tun yana dukanta tana ihu har ta kai muryarta bata iya fita Ummi kuma ta saka fitowa ta ceceta sai nata kukam take a dakinta tana sauraren muryar Nimra. Waira ce ta hau sama ta tsaya bakin kofar akin Nimra tana buga kofar da karfi, ba dan ta san abun da yake faruwa ba, domin shigowar kenan bayan ta ga ji da zama a motar da Maleek ya barta. Kamar wanda aka cewa ka yi ta dukanta har sai bacin ranka ya fita haka Maleek ya rika zunawa Nimra wayar carjar laptop din a jiki ido a rufe har kafarsa ya saka ya shureta, abun da be taba ba, ya kan doke su amman acan baya lokacin da suke shige masa hanci da kududdufi sai dai ba kamar irin dukan da yayi mata a yau ba. Do you know what? Da ina tunanin idan Abiey da Ummi suka amince zan goya miki baya ki aureshi, but yanzu na yanke hukunci ba zaki aureshi ba, sai kuma na ga yadda zaki yi, ki mutum na gani Ya karashe tare da kwafa sannan ya juya ya nufi kofar akin ya bude, sai yayi arba da Waira, ita ma ta yi arba da shi da bulalar wayar dake hannunsa, hannunsa dake rike da bulalar ta fara kallo sannan ta kalli fuskarsa dake hade kamar bakin hadari, a zatonta ya gama dukan Nimra ne ya fito ita ma yayi mata nata, sai ta kwala kara iya karfinta har sai da ya dafe kunnensa ya kauce daga gurin ya sauka kasa da sauri zuwa ya nufi bangaren mahaifinsa yana jin kansa na mugun sarawa, domin tana da yar muryar irin wannan mai shiga har can cikin amon kunne. Ummi ta fito da sauri tana share hawayenta ganin Waira tsaye a kofar akin Nimra ya saka ta karaso da sauri, ganin Ummi ya saka Waira ta yi shiru domin a yanzu ta gama fahimtar babu lafiya a gidan, ganin Ummi ma tana kuka. Lafiya? Waya taba ki? Ya Maleek ya dauki bulala zai daki Waira Ummi ta rika hannunta taja ta suka nufi akinta, hakan ya bata damar rumgume Ummi ta sauraren dalilinta na kuka. NIMRA POV. Maleek na fita daga dakin ta ji ihun Waira da kuma Isowar Ummi taja hannunta suka bar gurin ta san, Ummi ta ajeta a gefe kenan, ba dan haka ba da yanzu ta iso da gudunta a lokacin fa Maleek yake dukanta ta tare mata dukan har ma ta yi fada da Maleek din, amman gashi bata zo ba, sai da Waira ta yi ihu, furucin da Maleek yayi mata da kuma bacin ran da ta gani a fuskar mahaifinta, ya matukar daga hankalinta ya kuma tabbatar mata da cewar ba za su taba yarda ta auri Ameer ba, ita kuma a yanzu tana jin ta shiryawa mutuwa akansa, bata taba so ba sai akan Ameer wani namiji be taba shiga zuciyarta ta juyawa yadda yake so ba sai Ameer, dabam wanda be saba ba idan ya samu ba shi ma so da sauki, iyakar gaskiyarta tana nufin mutuwa idan har aka rabata da love of her life, bata ta inda zata rayu ba idan har iyayenta suka zabi raba soyayyar da Ameer. Daker ta tashi ta tsaye ta nufi inda ta nefar da key din mota da wayarta ta dauka idonta daya a rufe saboda dukan da Maleek yayi mata ya same ta a dayar idonta ne, bakinta na a kumbure yake har lokacin yana jinin naushin da Abiey ya kai mata a baki, bata ko iya taka kafarta da kyau sai dingishi take, ko'ina na jikinta tsami yake duk inda Maleek ya same ta da bulalar ya kumbura mata jiki, yayi mata ja. Idonta har ya canja kala saboda kuka har wani jiri take gani. Sai da ta fara lekowa ta ga babu kowa a saman sannan ta sauko nufo downstairs tana tafiya dake tana sauri ta sauka, kanta babu ankwali balle ayi maganar mayafi, haka ta sauko falon ta nufi kofa ta fita babu talkami da faduwar gaba ta fito falon ta nufi gurin motar da Ummi ta bar mata tana hawa tun bayan da Ameer ya ci uban tata motar. Ta bude ta shiga ta yi mata key kamin ta yi reverse kamar zuciyarta zata fado ta ji, masu gadi na ganin ta kunna mota sai suka fara kokarin bude mata gate, kamin ta iso har sun gama budewar ta nan ta samu sa'ar ficewa da sauri tana wani irin gudu. Fita ta yi daga unguwar amman hankalinta be kwanta ba har sai
Chapter 59 · 0% Book details