Sashe 64
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
aje plate din kasa ta kama zomon da hannu biyu ta dora masa saman jiki ba tare da tambayarsa zai rike mata ko akasin haka ba, da sauri ya dago yana kallonta irin lafiya kike? Kar ya gudu rike sosai da kyau Ganin zomon zai sauka jikinsa ya saka yayi saurin rikewa kamar yadda ta bukata. Good Ta masa thumb up, bata san baya son mace ta taba jikinsa ko ta rabe shi ba, domin bata taba rumgumarsa ko taba shi ta ga abun da yake damunsa ba, a iya tunaninta bashi da halin kirki ne a farkon zuwanta gidan, daga baya kuma ta ya sauko har yakan zauna ayi hira da shi sai ta fahimci ya jefar da wacan halin nasa ne marar kyau, yanzu ya shirya mu'amala da kowa. Bata tare da tunanin komai ba ta juya ta koma kitchen ta dauko wuka da wani babban tray ta dawo inda yake zaune rike da zomon ta zauna a kasa ta fara yanka karass din tana yanka apple, shi dai kallonta kawai yake, he's feel something different about her, lokuta da dama tana masa abun da baya iya musa mata ko yi mata magana, not like other girls da zai iya kashewa ma idan suka masa haka, tun bayan marin da ya taba mata a karon farko da taba jikinsa be sake sha'awar kai hannunsa a jikinta da sunan duka ko hukuncin ba, a wacan karon ma da ta rika shi ya ji wani yanayi na dabam ba zai iya bayyana yadda yake ba, ba jindadi ba ne kuma ba na rashin dadin ba, wani abu ne da be taba jin irinsa ba a rayuwarsa yana aya daga cikin dalilin da ya haddasa masa daukewar numfashi na wucin gadi, wata kila saboda mace bata taba rumgumarsa ba ne, balle ya san ya dumin jikin mace yake idan ya gwaraya da na namiji duk da kasancewar a fusace ta hau stairs din a wacan lokacin bacin ran da be san na minene ba. There is something special about her, her unique skin colar da gashinta da ya banbanta na kannensa, the way she talk idan ta kama dole iya zaman da ta yi a gidan na shekara daya ua fahimci tana da kiyaye doka, domin duk wani abun da ta san za a mata fada idan ta aikata tana kokarin kiyayewa musamman a abun da ya shafe shi, bata cika magana ba hakan na matukar burgeshi da ita domin baya son yawan surutu tana da natsuwar da idan ba a kusa da Ummi ta zauna ba zata nemi bayan kujera ta boya. Yana fara kallon kyakkyawar hallitar da Allah yayi a fuskarta na dagon hanci da blue eyes ga karamin pink lips sai zuciyarsa ta buga da mugun karfi kamar zata fisgo ta fado kasa. This is first time da yake kallonta da wani irin kallo da be taba yi ma ya mace ba, kowane motsin da hannunta yake da na abun da take yankawa har zuwa zaman da ta yi da kuma daukar abun da ta yanka ta ci, even taunawar da take kallon yadda bakinta yake motsi yake. Waira... Ummi wanda ta fito daga kitchen ta yi tsaye cak tana kallon ikon Allah. Maleek da Waira suka kalli inda take, Maleek mamakin tsayuwarta a gurin yake ya manta da abun da yayi a yau sabon abu ne da be taba yi ba, Waira kuma jiran take ta ji abun da Ummi zata fada bayan kiran sunanta da ta yi. Ummi ta karaso gurin ta nuna zomon dake hannun Maleek, sai Maleek ya kalli zomon. Oh ta ba ni rikonsa ne waya taba zomo? Kuma ka rika? Ta kalli Waira ya kalli zomon ya daga kafadunsa he can't tell why ya rike mata zomon. Ummin ai baya ciwo So take tace cizo. Ummi ta yi murmushi dake tare da hawaye daman kukanta a kusa yake. Wow... Mikewa yayi tsaye ya taku daya ya kara matasawa inda Waira take zaune tana facing dinsa, ya dora mata zomon saman jiki ya kabe jikinsa ya nufi hnayar fita falon. Ummi ta duka a gurin tana kallon Waira. You're so special Waira, zuwanki gidan nan ya taimaka min sosai kin canja rayuwar ana, sanadinki na fahimci abun da ban fahimta ba akan Maleek, komai yana da sanadi, ke ce sanadin canjawa Maleek Bata kula da zancen da Ummi take ba saboda hankalinta yana kan sabon abokinta. Ummin ki rike Zilll zan yanka abinci Ki bashi wanda kika yanka idan na dawo sai na rike miki, zan duba bangaren Abiey ne Tohm okay Ta amsa har sau biyu sannan ta shiga bashi abincin. Ummi ta ja kumatunta tana kara jin kaunarta ta mike tsaye tana murmushi ta nufi hanyar da zata sadata da bangaren Abiey. Tana tafe tana tunanin abubuwa biyu da suka zo mata a lokaci daya, wato ganin Ameer da kuma abun da Maleek yayi a yau, da ane ko taba zomon ba zai yi ba saboda Waira ta taba shi, amman a yau wai shi ne ya rikewa Waira zomo ta zauna a kusa da shi tana kusantarshi tana yanka abu, kuma idonsa na kanta. Kamar yadda Zahra ta wanke shawara na yanke shawarar zan aurar da su duka a watan da zai kama, idan basa da wadanda suke so, akwai yayan yan'uwa da abokai za a hada su Shi ne abun da Ummi ta ji daga bakin Abiey kamin ta tura kofar falonsa ta shiga, Dr Zainab ta dago tana kallon Ummi da tausayi a fuskarta har tana zubar da hawaye. Zahra kin ga da inda yayi ikonsa? Ashe haka abu ya kasance, wani hukunci sai Ubangiji Ummi ta nemi guri ta zauna tana kallon Abiey. Ina ganin zamu daga musu kafa zuwa wani lokacin da Nimra zata samu natsuwa, ba mu sani ba ko Namra ma bata da wanda take so kamin lokacin na san ta samu idan kuma akwai sai ya fito, ita kuma Nimra zata samu sakewar zuciya da natsuwa kamin lokaci, domin ba abu ne mai sauki ka rabaka da wani kuma a aura maka wanda baka so ba Ba zan daga musu kafa ba, daman ai sun kai munzalin aure, duk su fito da mazaje ayi musu aure Amman dole a fahimtar da ita dalilin da ya saka ba za a barta ta auri Ameer ba? Ta ina kenan? Shiyasa nake na ce da laifinki a lamarin nan, idan ba haka ba ta ina za a ce Nimra ta kulla alakar soyayya da wani har ta kai ga haka baki sani ba? Saboda ba ni kadai Allah ya bawa ikon kula da ita ba, ni da ita duk a karkashin kiwonka muke Abiey Ummi ta amsa masa a gautsine. Abun da kike kokarin ki aikata na fahimtar da Nimra ba ni kadai zai shafa ba, ke da Ameer din za ku fi kowa cutuwa saboda rayuwarsa ce zaki rusa, ki haddasa masa bakinciki da ke kanki kuma ki butulcewa wanda yake dawainiya da shi tun yana karami har ya girma Ban ce dole sai ta hanyar fada mata ina da alaka da Ameer ne kadai za a fahimtarda ita ba, amman kai me kake tsoro ne Abiey? Ban ce ka dauki dawainiyarsa ba ban bukaci komai daga gareka ba ni dai kawai ina son ana a kusa da ni....! That's it, daman na sani ai, amman babu yadda ban yi da ke ba a wacan lokacin akan ki aje yaron nan a hannunki kika ki, sai yanzu yaro ya girma yana rayuwarsa dabam zaki ce ki rusa rayuwarsa kuma ki rusa rayuwar mutanen da suke rike shi a matsayin a? Damuwata ba akan Ameer ne kawai ba har da matsalar da zaki jefa kanki a ciki ina jin tausayinki Zahra da abun da zai biyo baya Dr Zainab ta kalli Abiey ta kalli Zahra ta dafe kanta. Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, yau Abiey da Zahra ne suke sa'insa? Abun da ban taba gani ba? Subhanallahi wannan abun yayi muni, Zahra ki yi shiru dan Allah karki sake magana Har zuwa yaushe zan yi ta yin shiru Aunty Zainab? Shekara nawa a tare da Abiey? Ina da mafarkai da buri amman na rufe su saboda na samu zaman lafiya da mijina, shim ba ku taba tunanin kewa da kaunar uwa ga anta ba? Kai da ya aikatawa yarka haka ka ji zafi balle ni da ya kwanta a cikina wata tara da kwanaki na rike ka shi a hannuna na shayar da shi? Ko ka so Ameer ko karka so shi idan aka tsaga jinin Ameer sai an ga nawa a ciki Abiey ya girgiza kai yana murmushi takaici. Ba zaki gane ba ne Zahra, yaron da kike ta kokarin ki dawo da shi kusa da ke, ba shi da kirki ba ta inda zai girmamamu ko ya tsaya ya fahimce, ina gudun kar bakincikin ya zama mana biyu, domin ba ke kadai zai shafa ba har da ni, duk abun da ya same ki a tare za mu raba either na dadi ne ko akasin haka, sannan yanzu ba abun kunya ba ne ki zaunar da shi ki fada masa yadda aka yi kika rabu da shi? Bayan kin katse masa jindadin da yake a can? Ummi ta mike tsaye. Ba abun kunya ba ne, kuskuren da na aikata nake kokarin na gyara, amman kai abun kunya ne a gareka yanyanka su ji cewar ka ki ka taimaka min a lokacin da naje neman taimakonka, da ban aikata abun da zan kwanta a gado ya hana ni bachi ba...! Abiey ya hade fuska kamar be taba dariya ba, Dr Zainab ta yi saurin runtse ido tana girgiza kai. WAIRA POV. A cikin abubuwan da ta yanka ta bawa zomon karas ne kawai ya ci, sauran idan ta ba shi baya karba tana ganin haka ta mike tsaye tana shafa shi, can kuma ta dorashi saman kanta jin sonsa take kamar ranta, kawo mata zomon da malamin yayi ya tuna da yawa daga rayuwarta na baya, hannu ta saka ta cire ribon din dake kanta ta birjita gashin kanta ta dora zoman a saman kanta tana dariya, sai ta fara zagaya falon tana tafiya, har ta isa gurin kofa ta bude ta fito Maleek dake tsaye jingine