Sashe 97
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
buhun dake hannun matar saboda ta tabbatar masa bata iya kira ba, bata iya amfani da waya ba. Da da ne ba zai iya rike wayar ba saboda ta fito a hannun da be sani ba, gashi wayar karama ce da ta kusan mutuwa har aka daureta da roba saboda murfi ya tsaya. Wannan kaddara ta sauya masa rayuwa da mu'alama, cikin har da walwalarsa da farinciki da yake a kullum. Bangaren kiransa ya shiga ya duba numbers din da take yawan kira da kuma wadanda ake kiranta. Kin san yadda ta yi saving number wanda za a kira Rasa number da zai kira ya saka Ameer ya kalli matar ya tambayeta. Eh ranka ya dade, sunanta Aisha jikarta ce ita kadai take da waya a gidan ma, kuma ita take cewa a kira mata idan za ayi kira Ya maida hankalinsa gurin wayar ya duba number farko da aka rubutawa Aisha ya kira a wayar ya mikwa matar. Toh Toh Ta karba da hannu biyu ta kara a kunne. Hello Aisha Matsawa yayi ya bata guri jin an amsa kira sai yayi gaba kadan yana rumgume hannayensa. Ranka ya dade ya sunan wannan Asibitin? Ya juyo ya fada mata tare da kallon agogon hannunsa. Hikima hospital Ta fadawa yarinyar a waya sannan ta sauke wayar. Tace gata nan zuwa, Allah sarki hankalinta duk ya tashi sai kuka take Ameer ya busar da iskar bakinsa ya sake kallon agogonsa a karo na biyu. Akwai inda nake son tafiya, za 'ayi muku komai a nan, karku kashe ko naira ni zan biya komai, kuma ki tsaya a nan ki kula da ita kamin jikarta ta zo, zan dawo a anjima Toh ranka ya dade, Allah ya saka da alheri Ya kasa amsa mata da Ameen sai ya saka kai ya fice daga gurin. Daga asibitin kai tsaye ya nufi gurin wanki mota, shi ma da tambaya alexander ya isa gurin wankin motar da yafi kusa da asibitin domin be taba mai wanki mota ba, a gidansu ake wanke musu idan ma ya kama sai an kai toh ba shi yake kawai ba sai dai na bar motar a gida masu aikin gidansu, sai da isa gurin sai kuma wata zuciyar ta raya masa za su iya zargin wani abu, domin jinin mutum ne a motar ba kowa zai fahimta ba. Canja shawarar da yayi ne ya saka ya yi reverse sai ya canja hanya. Kamar ya san plan din da aka shirya isa makarantar a time din da suke daf da tashi. Waje ya tsaya ya aika mai gadin gate ya sanar da principal din yana neman Waira, har mai gadin ya ya tafi sai kuma ya dawo ya tambaya sunan babanta domin zai iya yiyu ba ita kadai cw Waira a school din ba. Ya sunana babanta? Ameer ya dan yi shiru yana nazari, be san sunan babanta ba kuma be san sunan da take amfani da shi a yanzu matsayin sunan uba ba. Waira Aliyu Ya fadi sunan mahaifin Maleek ba dan yana da tabbacin da sunan take amfani ba. Okay Ya juya ya shiga cikin makarantar. Be fadede ba ya dawo, sai aka bukaci Ameer ya shigo ciki domin tantance waye yake neman Waira. Yamutsa fuska yayi yana jin kamar yayi tafiyarsa, ya san idan ya shiga ciki za su tsare shi da tambaboyi ne da be san ma yadda zai amsa su ba. Ba dan kar tace ya karya mata alkawari ba da ba zai shiga ciki ba, haka dai ya daure ya fito daga motarsa ya shiga cikin makarantar, Security yana gaba Ameer na binsa a baya har suka shiga office din. Ameer ya mikawa mutumen hannu suka gaisa. Ka yi hakuri, dokoki ne na makaranta dole mu san wanda zai dauki dalibar mu, kuma dole mu san wanda ya kawo ta idan kawota aka yi, an kira mu daga gidansu an fada mana zaka zo, amman duk da haka ya kamata mu tantance waye kai, saboda hakkinmu ne kula da daliban mu matukar suna karanta Ameer yayi kamar yace musu shi ba daukarta zai yi ba ganinta kawai zai yi sai kuma yaji ba zai iya ba saboda gadarar ta tashi. Sun bashi littafi ya saka details dinsa, sannan aka kira Waira ta zo office din, ta shigo tana sanye da uniform, gashin kanta a fake a baya an sako shi ya sauko a bayanta, blue and black din uniform din ya mata kyau sosai. Tana ganin Ameer bata tsaya komai ta rumgume shi da murna. Da gaske zaka zo ashe I said i will Ya amsa fuska ba yabo ba fallasa. Motana yana waje muje can mu yi magana aa zaka jira mu tashi ne sai mu tafi tare, kai zaka kai ni gida zai mu yi magana a hanya Let's talk first Okay kaje ka jira ni a mota yanzu za a buga karaurawa Ya juya ya fice daga office din, sannan mutumen ya kalleta ya ce. Kin san shi? Sosai Okay ba wani matsala ko? Ta amsa masa babu da kai sannan ta juya ya fice. Ajinsu ta koma ta zauna a kujerar ta hada littafanta ta saka a jaka sannan ta kufa kanta a teburin da take karatun domin kowa da kujerarsa, haka take bata da sakewa a makaranta saboda suna mata kallon bare, gashi ita kuma ta kasa sakin jiki da saba da kowa, a kullum idan ta shigo makarantar tana maida hankali tayi abun da ya kawo ta ne, wannan ya saka take daga cikin students masu kwazo da saurin gane abu idan aka fada, ko aka yi musu bayani, secondly lessons din da ake mata a gida yana matukar taimaka mata sosai, sai dai sauran daliban da suka maida hankali kamar ita sun fita experience domin sun fara daga farko ne ita kuma ta hau abun ne daga sama. Tana jin na kada araurawa ta goya jakarta da sauri ta dauko cake din da Ummi ta yi mata dake karkashin table dinta ta fice cikin zumudi ta nufi gate, a ka'ida idan za a fita daga makarantar sai anyi signed daga mai daukar har dalibai idan kuma School bus ce zata kai su gida zai sun yi shi ma mai tukin yayi da nufin shi ya kai su gida. Ita ta fara saka hannu a inda ta saba, sannan security ya nufi inda motar Ameer take ya kai masa littafi ya karba yayi sign din. Sannan ta bude front seat ta shiga yana kallonta sai ta sakar masa murmushi. Ya karatu? Ba dadi Ya rage idonsa yana kallonta, he can't lie tana da kyau duk yadda zai misalta abun ya wuce tunaninsa, ba ma kamar yanzu da yake ganin nishadi da murna a fuskarta. Why? Bana son karatun ni ai, Ummi forced to do so If you don't want babu wanda zai saka ki dole, you can tell her Ko na fada mata ba zata bari na zauna a gida, kuma Ya Maleek zai yi fada he hate me so much Ta dan bata fuska ta turo baki, irin batawar da ya kara mata kyau domin a shagwabe ta yi maganar. This is the second time da ya ji abubuwa suna burgeshi akanta, far'arta da kuma bata fuska ko wanne kyau yake kara mata. Ba dan ya tabbatar ita din ce yarinyar da ya gani a can duniyar ba mai matukar kazanta da datti da ko za a hade kur'ane a rantse masa ba zai yarda ita ce aka gyara ta zama kyakkyawa haka ba, har wani abu nata yake burgeshi, yarinyar fa ganin bera a kanta ya saka shi amai, gashi a yanzu ko yar minister ba zata gwada mata kyau gashi ba, domin an gyara mata shi ya kwanta lum ya kara ba i sai sheki yake kamar ba nata ba. Ta bude dan box din cake din ta saka hannunta ta gutsira cake cin ta ci. Yanzu kuma bakinta yake kallon yadda take motsa shi a hankali tana cin cake din, ta dago ta kalleshi sai ta dauki karamin spoon dake gefen box din ta saka ta dibi cake din ta kai masa saitin bakinsa. Ya kalli cake din sannan ya kalli fuskarta. Akwai dadi ka ci, na aje ban ci ba saboda kai, ban yi break ba Ya bude baki ta saka masa ya fara taunawa, ta aje spoon din ta saka hannunta ta fara ci. Akwai dadi? Ya daga mata wani irin kallonta yake kamar ya hadeta. Ta sake daukar spoon ta diba ta kai masa a baki ya karba ya ci, sai ta aje ta saka hannu tana ci. Ni bana ci abinci da wannan Why? A garin mu da hannu muke cin komai, ya fi dadi Ta saka saka dauka ta kai masa a baki, wannan karon da hannunta ta kai masa. Sai ya dan tsaya kallonta sannan ya bude bakin ta saka masa. Ummi ce ta yi min yayi dadi sosai Cak ya tsaya da taunawar da yake, fuskarsa ta canja daga ba yabo ba fallasa to ba yabo, hannu ya kai ya dauki tissue ya zuba ragowar a ciki ya sauke glass ya jefar. Wani iri yake ji ace mahaifiyarsa tana raye amman be taba cin abincinta ba ko sau daya, be san yadda girkinta yake ba. Tambaye ni abun da kike so, zan tafi Kai zaka kai ni gida ai, na fadawa Ummi ba school bus zata maida ni ba Ya juyo ya kalleta kamar ya ce wani abu, sai kuma kwarjininta da ya cika masa ido ya hana shi kin cewa komai. Ya maida hankalinsa gaba ya jaya motar suka kama hanya, ko da wasa be sake kallon inda take ba. Ka yi fushi kuma? Saboda na baka cake din Ummi? Why do you hate her? Why don't you ask her why she hate me from first place? She didn't, tana sonka sosai Ameer Kuma ta bar ni? Ita tace ki zo ki ba ni cake? Ki siye ni da kalamai? Aa bana karya, bata ce tana son na baka cake ba, daman ni abincina daga cake sai biscuits ko fruits, tana yi min cake kullum Yayi shiru be ce mata komai ba, sai hawaye da suka cika idonsa. I'm sorry You shouldn't Ummi tana sonka sosai