← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 165

Sashe 13

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

ne idan aka ce Ameer yaki zuwa gurin, kadan daga cikin halinsa ne, kuma mahaifinsa zai goya masa baya akan haka. Indai wanda nake tunani ne, ba zai je ba daman, kuma baka bukatar yin komai akai Abiey mahaifinsa yana da kudi sosai, zai iya yin komai ya kare dansa, wannan wasan a tsakaninmu ne, dan Allah ka hakuri ka kyale ni da shi kawai A tsakaninku? Wannan ya wuce a tsakaninku, komai Ubansa ya Mallaka sai na hukunta yaron nan, kuma kar na sake ganinka da abokan nan naka Ummi ta kalleshi kamar ta yi magana sai kuma ta yi shiru ta sauke ajiyar zuciya. Namra ta yi kwafa tace Wannan abun ya zama rainin hankali, danka ya aikata abu kuma ka kasa zuwa balle har ka tura shi ya bada hakuri, ta ina za ayi musu iyaka kenan? Kuma hakan ai zai bashi damar sake aikata wani abun a nan gaba Na fadawa CP shi idan ba zai yi ba, zan saka DSS su kama shi, kuma sai na hukunta shi ko dan ya zama izina ga wasu Sam ran Maleek baya son abun da mahaifinsa Abiey yake kokarin aikatawa, sai dai be isa ya hana shi ba, ya san idan ya nuna mahaifinsa hakan zai bude wani sabon shafin fadan ne a tsakaninsu, domin Abiey baya wasa da abun da ya shafi iyalinsa, musamman yayansa a yanzu. AMEER POV. Rabuwarsu da Nimra da uku ya bude motarsa ya shiga, ba mutum ne ma'abocin yawo ba, duk kuwa da kasancewarsa tantari gurin zuwansa uku ne idan baya gida yana tare da abokansa idan baya can yana tare da falkarsa sai kuma a yanzu da ya samu wannan gurin zuwa da yake haduwa da Nimra. Gurin da suka saba zama da abokansa ya nufa sai ya samu gurin a rufe, abun da ba a taba ba. Miya faru? Ya tambayi kansa, kamin wani gefe na kwalkwalwarsa ya tuna masa da abun da ya faru.. Oh... Ta tabe baki, ya juya motarsa ya ciro wayarsa number Tarig ya fara kira ta yi ringing har ta yanke be daga ba, a ka'ida baya kiran mutum sau biyu amman haka ya daure ya sake kiransa nan ma be daga ba, ya kira Dawood shi ma be daga ba, then Abdull ma yaki dagawa. Me yake faruwa? Ya tambayi kansa gabansa na faduwa, zuciyarsa na raya masa ba lafiya ba, domin be saba kiransu gaba daya ace kowa be daga ba, juya akalar motarsa yayi zuwa dayan gurin da suke hutawa, maybe zai samu wani a can, if not sai dai ya wuce gida domin a tsakaninsu babu mai iya zuwa gidan wasu neman wani. Ya isa a sa'a after faka motarsa da minti biyu ya fito ya shiga VIP din dake gurin, part din da suke zama ya nufa tun kamin ya karasa ya hango Abdull da Dawood zaune a gurin with serious face da alama wani abun suke tattaunawa. Kujera yaja ya zauna kamin ya ce komai Dawood ya fara mikewa tsaye Abdull ya bi masa baya suka fice daga gurin suka bar shi zaune da mamaki. What this mean? Ya tambaye kansa domin ransa be kawo masa komai ba, sai yanzu fushi suke da shi akan abun da ya faru? Or Maleek yayi masa wani sharin a gurinsu? It's because of.... Sai kuma yayi shiru, a ganinsa ko da saboda abun da yayi ma Maleek ne be kamata su shigar da kansu ba, domin a tsakaninsa da Maleek ne, idan ba haka ba miyasa ba su yi ma Maleek haka ba a lokacin da ya watsa masa yawu a fuska? Be tabbatar abun da friends dinsa suka masa ya masa zafi ba sai da ya shiga motarsa yayi mata key, da wani irin karfi ya daki sitiyarin motar yana jin kamar ba a taba bata masa rai irin haka ba, domin be taba samun matsala da friends dinsa da ta kai ya zauna su tashi ba sai a wannan karon and all because of Maleek, bayan fadan da Daddy yayi masa. Wayarsa ce ta yi ringing da gangan yaki kallon gefen da wayar take ma balle har ya duba ya ga mai kiran balle kuma ya amsa, har ya isa bakin gate din gidansu be bi ta kan wayar ba, kamar zai tashi gidan haka ya danne horn har sai da Masu gadin gidan suka bude masa gate. Har gaban kofar Momy ya faka motarsa ya fito va tare da ya dauki wayar ba ya karasa gurin kofar falon, yana ganin yadda kanwarsa ta bude masa kofar falon tana jiran shigowarsa ya san wani yakin zai tarar a gidansu. Kallo daya yayi mata ya dauke kai ya shiga ciki, sai ya samu mahaifinsa a tsaye yana jiran shigowarsa. Kamar ya san nemansa Daddy yake sai ya karasa gurinsa ya tsaya ya kasa ce masa komai kamar yadda be yi sallama a farkon shigowarsa falon ba, daman can kuma ba al'adarsa ba ce sai dai ya kan gwada yi wani lokacin idan Daddy na gurin saboda ganin fuskarsa. Tassss Daddy ya wanke masa fuska da mari mai kyau, har sai da Ameer ya hade hakoransa na sama da kasa ya dantse ya yarfar da fuska gefe ya rufe ido. Kamin ya bude idanuwansa sun hada wani karamin yaki da ya haifar da sauyawar launin kalar idonsa daga fari fes zuwa ja. For What Dad? Ya tambaya wasu jijiyoyin bacin rai da takaici na bayyana a goshinsa, a take Daddy ya sake marinsa a barin da ya mare shi dazun yana masa wani mugun kallo irin na fadan Uba da a, wannan karon Ameer be rufe idon ba, sai dai ya sake yarfar da fuskar ya kalli kasa, da wani irin tashin hankali Momy ta hade yawun bakinta, idon kanwarsa Humy kamar zai fito tsabar mamakin Daddy ya mari Ameer har sau biyu a lokaci daya. Ameer ya dago yana yi ma mahaifinsa wani kallo da be taba yi masa irinsa ba, kallo ne mai kama da harara irin na an da suka gagari iyayensu, a take Daddy ya sake marinsa, cikin karfin hali Ameer ya sake dagowa nan ma Daddy ya sake sauke masa wani lafiyayyen marin, Momy na ganin hakan ta shiga tsakiyarsu ta tura Ameer baya tana kallon Daddy da tsananin mamaki, Humy kan tuni hawaye na wanke mata fuska domin ba Momy kadai ba ita kanta ta tsorata da halin da ta ga yayanta da mahaifinta a yau. Haba Alhaji me yake faruwa da kai yau? Ameer kake mari har haka? Daddy ya nuna Ameer cikin zafin zuciya naman fuskarsa na rawa kamar zai fado. Kudi da gata suka saka ka zama haka ko? Ka taka wani wanda ka ga dama ka mari wanda kake so, ka wulakanta kowa ka kade mutanen da ba su maka komai ba, ka kori ma'aikatan kamfani na akan karamin dalili, sannan na ce kayi ka tsallake layin da na shata maka ka yi tafiyarka inda ranka yake so, kuma na kira ka a waya ka kasa dagawa? And i slap you, you ask me for what? Sai na koya maka darasi, daga yau babu kai babu kamfanina, babu kai babu kudina, babu kai babu motocina, babu kai babu duk wani abun da kasan nawa ne, ko kuma zaka saka sunana ka samu, ka tattara duk abin da ka san nawa ne ka dawo min da abu na Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, Ameer ne fa Momy ta furta cikin tashin hankali da tsananin mamakin furucin Daddy. Daddy ya kalleta. Ameer Ubana ne? Ni na haife shi ba shi ya haife ni ba, idan kudin da nake sakar masa yake sakawa yana wannan halin daga yau na daina... Kamin Daddy ya kai aya Ameer ya tari numfashinsa. And Daddy kana tunanin ba zan iya rayuwa idan babu arzikinka a tare da ni ba? I had my own money too ina kudin da zasu isheni na gina kaina da rayuwa ta Ya karashe maganar cikin zafin rai gafen fuskarsa na dama na kara bayyana shatin marin da Daddy yayi masa, kasancewarsa farin mutun da jikinsa baya daukar wahala. Duk wani abu da kake takamar naka ne, ka samu ne a karkashina domin a kamfanina ka yi aiki, kamin kamfanina abinci da ruwana da suturata ka saka har kai a inda kake yanzu, nuna min naira biyar da ka samu ta karkashin wani wanda ba ni ba, idan har kana son ka burge ni, kuma ka nuna min ka isa ko kudin da yake account dinka karka yi amfani da shi, and already ma fadawa Bello duk wani abun da yake da sunana akai na ka, ya dakatar da shi Daddy ya fada cikin kakkausan lafazi. Ameer yayi wani shu'umin murmushi ya girgiza kai, takawa yayi a hankali ya karasa kusa da kujerar da Daddy yake tsaye ya aje masa keys din motar dake hannunsa ya kalleshi ba tare da ya sake cewa komai ba ya juya ya fice fuuuu kamar walkiya. Momy ya bi bayansa da gudu tana rikosa. Baka da hankali ne Ameer wannan fa mahaifinka ne, be kamata ka yi masa haka ba, domin kai kake da laifi, ka koma ka bashi hakuri Ameer karka yarda ka yi fushi da mahaifinka, karka yarda shaidan ya shiga tsakaninku... Juyowa Ameer yayi ya kalleta. Da hadin kanki aka yi komai, ke kika shirya masa duk abun da yayi karki zo kina min wani wasan, gida ne zan tafi na bar muku abun ku Ya juya ya cigaba da tafiyarsa, sai kuma ya juyo ya dawo cikin falon har lokacin Daddy na tsaye a inda ya bar shi, Momy kuma ta biyo bayansa suka dawo falon tare, Upstairs ya nufa ya shiga dakinsa tsayawa yayi ya karewa dakin kallo, sannan ya shiga boutique dinsa dake dakin, tulin kayan da suka kawata dakin ya bi da kallo be ji zai iya daukar ko daya ba saboda ya same su ne duk ta hanyar mahaifinsa, kuma shi a yanzu ya shirya nuna masa he can live without him, gurin da ya saba aje sarewar ta busa ya nufa ya bude gurin ya dauki box din sarewar gaba daya domin ita ba da kudin mahaifinsa ya same ta ba. Fitowarsa ta fi shigarsa tashin hankaki, domin ya fito a yanayin
Chapter 13 · 0% Book details