Sashe 94
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
wasu abubuwan akanta a yanzu ya saka ta tunani. Me yasa baka zo jiya ba An yi mutuwa ai Waya fada maka? Na zo na tararda gidan a cike da mutane, na tambaya sai aka fada min mutuwa aka yi Ta saka littafanta a muhalinsu ta dauki jakarta ta juya ba tare da tace komai ba. Sai ya kirata Waira Ta juyo ta kalleshi. Karki da al'ummarki, karki yada al'adarki, karki manta da mutanen da suke ta fafuka akanki, memory ki na kurciya ya zauna a kanki, rayuwar da kike a garinku tana da dadi fiye da nan Kasa ce masa komai ta yi ban da ido data sakar masa har ya dauki jakarsa ta karatun ya nufi gate yana dingishi kamar gurgu. 9:23pm Ummi ta aje kofin shayi biyu a gaban Abiey, ma farkon ta fara dauka ta mikawa Abiey sannan ta dauki dayan ta mikawa Dr Zainab dake zaune a falonsa. Aa ku sha tea ai sai ku, ni idan kin ga na sha tea safiya ce zan yi breakfast Ummi ta zauna rike da kofin tana kallon Abiey da ke bata umarni babu wasa a maganarsa haka ma a fuskarsa. Wannan ya zama na karshe da zaki sake dafa min wani abu, na san aiki zai yi ma Hanne yawa dan haka na yanke shawarar zan karo wasu masu aiki Ciwona ba zai hana ni yin komai ba ranka ya dade, dan abun da nake dafa maka ai ba wani abun wahalar ba ne Ba shawararki nake nema ba, hukunci ne da na riga na yanke, kuma idan abubuwa sun dan laba zamu fita waje a duba ki a can hankali zai fi kwanciya kuma zan fi samun gamsuwa idan a can ne, saboda suna da kayan aiki masu kyau Dr Zainab ta tari numfashinsa. Yanzu ma yake min maganar rage wasu ayukan ma office, saboda ya samu time din zama a gida kuma na yaba da hakan, daman ina tunanin lokaci yayi da ya kamata ace ya sauwake kansa wasu abubuwa ya huta Duk saboda ni? Haba dan Allah karku sauya rayuwarku saboda wannan, ba abun mamaki ba ne Allah ya bani lafiya mai daurewa, wata kila ma sai duk kun rigani mutuwa Dr ta yi murmushi tana zolayar Ummi. Ban ji bakinki gashi ina son na tafi Kano jibi idan Allah ya kai mu Jibi kuma? Eh tun da na zo ina nan Abuja, ai ya kamata na leka gida na ga yan'uwa da iyaye, jibi idan Allah ya kai mu zan tafi Kano, Jabir ma na ji yana zancen tafiyar gobe ban sani ba ko ya fasa Zaku kara mana kewa Auntie Toh ya za'ayi abun da ya zama dole ai dole ayi shi, daman bayan taro sai raguwa, amman dai ina bada shawarar ku sake bincika yan'uwan yarinyar Waira take ko Wara? Saboda akwai rai akwai mutuwa Abiey ya kurba tea ya aje ya dauko wani zancen domin baya son maganar da Dr Zainab ta yi ta Waira. Sauban ma yace min gobe zai koma, amman kamin ya tafi zai sake dawowa Yayi kokari ai sosai Allah dai ya bar zumunci, kun zama yan'uwan kai da shi Cewar Dr Zainab kamin ta kalli Ummi dake fadin. Waira tana son zama da mu Auntie, kuma ta fada mana matsalarta, ko ba komai tana rage min kewar Nimra, idan aka dauketa zan yi kewa sosai kuma ita ma ba asan halin da zata fada ba Zamu yi wannan maganar daga baya, for now yarinyar tana tare da ke, karki saka damuwa a ranki Yadda Abiey ya mika hannu ya dafa kafadar Ummi yana bata magana ya matukar burge Dr Zainab, hakan ha tabbatar mata har yanzu kanenta yana bawa matarsa kulawa. Ummi ta mike tsaye rike da tea Bari na baku guri Okay Abiey ya amsa yana binta da kallo ransa na una,a yanzu ta fi zame masa tashi hankali fiye da mutuwar Nimra domin ita dai ya san ta tafi kenan, tsabanin Ummi da ciwo ke tare da ita. Waira na ganin Ummi ta mike tsaye ta nufi Ummi tana fadin. Ummi zaki kira min Sulem ko Ameer please? Ba ni da number Shuraim, Namra ce mai number sa, Ameer kuma idan na kira na san ba zai daga ba Zai daga Ummi please ki kirashi Toh kai wannan Kitchen sai ki dawo na kira shi Ta karbi tea ta nufi hanyar kitchen, tana shiga ta samu Maleek tsaye yana sakawa kansa kankara. Kallo daya ta yi masa ta dauke kai ta nufi kusa da inda hake ta aje ta dauki abu ya rufe sannan ta juyo. Samun kansa yayi da binta da kallo, ya sani da a da ne sai ta fada masa abun da ya kawo ta kitchen din sannan ta yi dakon jiran umarnisa kamin ta aje. Sai dai a yanzu bata yi ko aya ba, hakan kuma sai ya ji kamar dan dame shi, fushi take da shi? Or ranta ne a bace? Be raba ayan biyu ba aje kankarar ya fito daga kitchen din, yana daf da ficewa falon ya ji Ummi na fadin. Shiga akina ki dauko wayar sai a kira shi Yana rike da wani littafi na turanci yana dubawa kanwarsa Fiyya ta turo kofar dakin a hankali ta shigo. Ya Ameer Favorite Ta fada ba tareda ya dago ya kalleta ba. Sai ta zauna kusa da shi tana leka abun da yake dubawa, a lokacin ya kalleta. Wani abu kike so? Ya Ameer duk ka canja, kusan three days kullum kana daki Fiyya baki san abun da ya faru ba ne? Na sani, amman faruwar wani abu zai canja alakata da kai ne? Zai tashi matsayinka na yayana ne? Ko kuma zai canja ka a matsayin an Daddy? Har abada kai yayana ne, fitowar wannan abun ke kara mana komai ba sai kaunarka, Mommy tace kar mu kuskura mu tattauna wannan maganar ko da yan'uwa balle kuma wani a waje ya ji, ta ce mu aje wannan maganar a cikinmu, dan Allah ka dawo da mu'alamarka yadda ka saba, wannan takura kanka da kake muma muna takura da shiga damuwa sosai Yayi murmushi. That's why you're my favorite Safiyya kin fi kowa fahimtata da kusantar inda nake Ta rike hannunsa. Ka yi min alkawari zaka canja Yayana? Sure for you only Taja hancinta sai ta yi dariya ta mike tsaye. Daddy yana kiranka zaku ci abincin dare Ya busar da iskar bakinsa. Oh... Okay ina zuwa Ta masa waving sannan ta fice. After like ten minutes da fitarta ya rufe littafi ya mike tsaye yana gyara rigarsa ya fito daga dakin. Ko da ya shiga bangaren Daddy ya same shi har ya fara cin abincinsa. Yunwa nake ji ba zan iya jiranka ba Ya kalli dinning din da aka cika da kuloli, ya kalli plate din Daddy dake cin tuwon shimkafa da miyar kubewa sannan yaja kujera ya zauna. Yau kam Mommy ta yi min favorite dina kai ma kuma ta yi maka na ka Daddy ya fada yana cin tuwo fuska sake kamar babu damuwa a tare da shi, tun a lokacin da abubuwan nan su faru Ameer ya daina ganin kwanciyar hankali da far'a a fuskar mahaifinsa sai yau. Daddy ya dauki plate ya mika masa. Ka zuba abun da kake so Ameer ya karba ya aje plate din a gabansa ya bude one of expensive warmers da suke gurin ya fara zuba White rice da aka sakawa green beans da carrots da green pepper da yellow, haka yake son a dafa masa farar shimkafa sai a hada masa da miyar hanta zallar hanta, a yankata kanana ta yadda kowane spoon sai ya ci da ita a ciki. Dazun mahaifiyarka ta zo, sai dai na hana ta ganinka saboda kar ta takuraka i know baka son ganinta a yanzu Daddy ya fada yana kai yankan nama a bakinsa. Sai Ameer ya tari numfashinsa. ZAHRA na ganta Daddy be damu da kiran sunanta da yayi kai tsaye ba, daman yasan indai Ameer ne komai ma zai iya faruwa. Oh really? Ka yi magana da ita? Yeah na fada mata karta sake zuwa gidan nan Saboda gidan nan gidanka ne? Ameer ya kalli Daddy. Daddy don't joke about this I'm not joking shiyasa da tace zata ganka na hana, amman idan zata zo gurina ko gurin Matata wannan ba huruminka ba ne? Ka fi kowa sanin bana son ana wulakanta mutane Daddy bana son ganin matar nan, da bata min duk wani tsari da tunani na rayuwa I know amman dukan dam'adam ajizi ne Ameer, tana da laifi tabbas kuma ta cancanci duk wani hukunci da zaka yanke mata, amman ni ma ina da nawa laifin, meyasa ban nuna maka haka tun farko ba? Wata kila da duk wannan rudanin be same ka ba Daddy ka yi hakan ne saboda tace ta yafe maka ni, domin ita tana da wasu yayan da suka fi soyuwa a ranta Ameer ko da babu zuwan wannan ranar da ita zata fada maka, ni na san wata rana idan bana raye za'a fada wannan, domin yana rubuce a cikin wasiyar da zan bari, saboda hakki ne da ba nawa ba dole kuma na sauke shi, saboda akwai yan'uwana da suka san da wannan maganar, na tabbatar idan bana raye za a dago maka da wannan maganar, a can ina tunanin kamar idan bana raye abun zai fi zame min kwanciyar hankali, sai dai halin da na ganka ciki a yanzu, ya saka na ji cewar ka san komai a lokacin da nake raye zai fi sauki fiye da bayan raina, domin zafin zai zame maka biyu, amman a yanzu zan iya kula da kai, zan ganka na yi farinciki, domin babu abun da zai canja daga matsayinka na ana da nake kallonka da shi Ya yayinda ya fara cin abincin kamar an masa dole. A lokacin ne Daddy ya aje spoon dinsa ya hade hannayensa yana kallon Ameer. Wallahi da za a iya shiga abun da yake zuciya, Ameer da ka kara gode Allah da wannan abun ya bayyana, domin ya kara maka kima da kauna da tausayi a idona, ina jin kaunarka a yanzu fiye da da Tsayar da cin abincin yayi ya kalli Daddy. Ba dan nasan kudi