Sashe 113
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
a jikinsa shi ma kuma jike yake kamar ita, wani irin kishi ne ya fisge shi. Wanka kuka yi? Ya furta kai tsaye, furucin da ya bawa Maleek haushi taya zai yi wanka da karamar yarinyar kamar Waira, ko ba ita ba shi sam ba zai iya rayuwar karya ko ta aure da mata ba, ya san zai iya zama a inuwa daya da su a yanzu da rayuwarsa ta sauya amman ba a irin inuwar aure ko ta zina ba. Ummi ta kalli Ameer da mamaki Mahmood ma haka kana kallonsa ka san da gayya yayi maganar fuskarsa ta munana alamar ganinsu haka be masa dadi ba. Ruwa na fada sai Ya Maleek ya cire ni Maleek ya kalleta da sauri never thought zata rufa masa asiri kamar yadda ya roka, wannan ne karo na farko da ta burgeshi, wani abu ya karu a zuciyarsa bayan tausayinta da yake. Ameer ya aje spoon din hannunsa ya mike tsaye yayi kanta, Maleek kuma ya kama hanyar stairs be ko kula da Ameer din ba. Taya zaki fada ruwa? Gurin da na aje wayata da da sarewata akwai tazara mai yawa a tsakani fada min yadda aka yi kika kai gurin ruwan? Ta yi shiru tana kallonsa a yanzu kuma bata san kalar karyar da zata yi tace shi ya kai ta gurin har ta fada ba. Ameer ya tsaya kanta. Idan ma ruwa kika fada ba zaki iya fitowa ba ne sai an dauko ki? Ni ban taba shiga ruwa ba Ta fada a shagwabe tana son yin kuka. Ina wayar take? Ina sarewar? Sai a lokacin ta tuna da wata waya da sarewa da ta saki a lokacin da ta ji ta a gabar mutuwa. Suna ruwa Kallonta yake so yake yayi mata fada kuma baya son ta yi fushi da shi, sai dai sam yanayin da ya ganta tufafin bachinta sun kama jikinta, ga kuma Maleek da yake ganin ya ganta ya bakanta masa rai matuka, wani irin kishi yake ji kuma wannan ne karon farko da yake jin haka, domin ya zauna da Nimra be taba jin wani abu na kishi akanta ba ko sau daya, haka ma yayi zama da Angel ita ma baya jin kishin komai akanta, kawai dai baya son ta hada tarayyarsa da wasu mazan ne saboda yana kyamarsu, kuma yana jin ya fi kowa, but Waira is different from them, komai da yake jin a kanta ya banbanta da yadda ya saba jinsa komai about ita is real da gaske son ta yake kuma baya son ganin kowa ya rabe ta. Waira shiga ciki ki canja ki sauko ki ci abinci, maybe bata iya ruwan ba ne, kuma kasan Maleek ba zai ga tana kokarin mutuwa ba ya kyaleta Ya juyo ya kalli Ummi cikin damuwardata kasa boyuwa fuskarsa. Ummi ta ya za'a ce bata iya ruwa ba? Ruwan ba mai yawa ba kamar na gidan nan? Kuma idan har taimaka mata zai yi ai hannu ya kamata ya mika mata ta riko ya fito da ita ba wai su shiga ruwan ba? Ummi ta mike tsaye ta nufo inda suke tsaye. Ameer Waira ba a gidan ta tashi ba, ba lallai ne ace ta iya kalar rayuwar da kuka ba, zuwanta gidan nan ma if i can remember ko ruwa bata son ya taba jikinta, maybe shi ya saka bata iya ruwa ba I hope so Ya fada sannan ya dauke kansa ya nufi stairs sai kuma ya juyo ya kalli Waira dake takowa a hankali. I'm sorry, let me go get my phone Kallonsa kawai ta yi ta sauke idonta kasa shi ya nufi kofar fita Waira kuma ta nufi stairs... *** *** *** Tun daga Ranar sai Ameer ya daukarwa kansa wani duty, kullum shi zai kai Waira School ya dawo da ita, hw use that opportunity yayi ta fada mata abubuwan da bata sani ba akan addinin musulumci, idan sun dawo kuma yayi ta dora mata da abubuwan da ya sani kasancewar mai yi mata lesson ya daina zuwa a yanzu, sai ya zamana da yamma bata aikin komai sai sauraren Ameer dake karantar da ita yana mata searching din wasu abubuwa, sannu sannu har ta kai Waira zata dauki remote da kanta ta kama peace tv ta zauna tana kallon program din da ake, idan kuma ta dauki wayar Ummi ko Ameer ta shiga ta tana kallon abubuwa, wani zubin kuma game take da wayar. A dan zaman da Ameer yayi a gidan na wata biyu da kwana goma sha uku shakuwa da kyakkyawar alaka mai karfi ta kara shiga tsakaninsa da Waira, idan bata cikin gidan har bata jindadi, ta kan dauke masa kai ne kawai idan Maleek yana zaune a inda suke zaune, kamar falo ko dinning, shi kan shi ya lura bata sakewa idan Maleek na gurin duk yadda yake mata magana ko ya tsokane ta iyakacinta murmushi. Duk tsawon lokacin nan babu daren da Maleek baya shigo dakinta Either ya rumgume ta ko kuma ta taba jikinta, tun abun na damuwarta har ta soma sabawa, some times zata jira ma har sai ya shigo ya fita sannan ta kwanta, domin bata jin ta jindadin sai ta yi bachi ya tasheta, a tsawon lokacin da yake shigo dakinta be taba ce mata komai ba, sai dai kamin ta saba ta gwada buge masa hannu da fada masa bata so, sai dai ganin ba zai daina ba ya saka dole ta hakura. A tsawon lokacin ta kame baki bata fadawa kowa ba, no matter how ta yi unkurin fadar sai ta kasa, some times tana tunanin Maleek yana mata haka ne saboda ya hurar da ita saboda biyewa Ameer da take shi kuma baya son haka domin kullum cikin yi mata gargadi yake, ta hanyar fada mata da baki ko kuma da ido. Today is Sunday Waira na zaune gefen Ummi rumgume da baby Rabbit dinta sai shafa shi take tana wasa da kunnensa, Ummi kuma hankalinta yana gurin wayar da take da yar'uwarta Maryam. Ni dai ina tunanin kamar bata hakuri ba ne, shiyasa ta ce bata bukatar komai, ko abinci aka kai mata na lura indai daga gurina aka tafi da shi haka za a dawo da shi bata taba ba, idan kuma naje dubata da zarar mun gaisa na yi mata ya jiki ta amsa ba zata sake cewa komai ba, amsawar ma kamar an mata dole haka zata ta yi, sannan duk lokacin da Ameer ya dawo indai ya fara zuwa gidanta sannan ya dawo gidan nan ina ganin canji a fuskarsa Zahra kin fi kowa san wacece Hajiya, tun kamin ki auri Deen har kika aure bayan rasuwar da auren da kika yi babu abun da baki gani ba na halinta. Dan haka ki saka mata ido a yanzu ki bita a yadda take son tafiya Ummi ta mike tsaye tana sauke ajiyar zuciya. Ina burin kyautatawa kowa Ya Maryam, ina son na kyautata mata, na san shi Baba ba zan iya samun yafiyarsa ba, amman ita ai tana raye yafiyarta nake son na nema a yanzu, ba zan iya da hakkin mutane da yawa ba Idan kina son neman yafiyarta sai ki bi ta hanyar anki Ameer mana, tun da shi kun samu kyakkyawar fahimta da shi Bana son na saka shi cikin matsala ta ne, burina kawai na kyautata mata irin kyautatawar da zata mantar da ita abun da na yi mata har ta furta cewar ta yafe min, amman ta ki ba ni wannan damar, yanzu kin ga sallamarta za ayi a asibiti na ce zan ba su gurin da za su zauna mai kyau, saboda Ameer ya fada min inda suke zaune ba shi da kyau kuma akwai mutane da yawa a gidan amman ta tsaya kai da fata ita bata bukatar komai daga gareni, dauren min fuska da take ma abun yana damuna sosai Daman ba zai yiyu ta saurareki cikin kankanen lokaci kuma ya fahimce ki ba, dole na sai kin bata lokaci kuma kin yi hakuri, ki kwantar da hankalinki Zahra ke dai kina aikata hakan ne da zuciya daya, dan haka ki yi hakuri kuma kar hakan ya saka ki fasa kyautata musu, ai ita ma idan zata yi adalci kin yi musu duk yadda ake yi, kuma girma ya kama yanzu, ta san kuma karfi ba daya ba, ba zata iya ja dake ba idan ma ta ce zata yi shari'a ne, kuma silar wannan abun ba gashi Mr Bashir ya dauke mata nauyin komai ba? Wannan ma kawai jindadinta ne, dan Allah karki saka damuwa a ranki kin san dai yadda jikinki yake Ummi ta sauke ajiyar zuciya, zata sake maganar Waira ta mike tsaye tana fadin. Ummi assignment din ba'ayi min ba, kuma gobe school za su min fada idan ba ayi ba Ummi ta rage murya. Dauki assignment din ki tafi falo duk wanda kika tarar ki ce yayi miki assignment din Ta amsa sannan ta nufi kofar fita ta bar Ummi tana ta wayarta, tana fita dakin Namra ta shigo rike da waya a hannunta, can one seater ta zauna tana kallon Ummi dake waya. Waira dakinta ta shiga ta dauko jakarta ta bude ta dauko littafin da aka bata assignment din ta dauki pen ta sauko kasa. Maleek ta tarar zaune a kasan carpet, ya rufe ko ina na jikinsa da jacket, kafarsa ma sanye da safa kansa ma na sanye da jar hular sanyi. Tea mai zafi na gabansa da kananan cincin a plate ya maida hankalinsa gurin Plasma dake kunne yana kallon wani documentary da ake a Al Jazeera. Zuwa ta yi ta tsaya kansa sai kuma ta ga kamar hakan be dace ba, a kokarin na yi tarbiyar da Ummi take dorata ta zauna gefensa tana kallon yadda dress din yayi masa kyau. Ya Maleek ga assignment da aka bani a school sun ce gobe za a kawo Juyowa yayi ya watsa mata wani banza kallo ya dauke kai. Bata damu ba ta fara bude littafin tana nuna masa. Ni kika maida kafiri kenan? Idan karatun Allah ne sai dai ki samu Ameer, yanzu kuma da yake na boko sai kika kawo min ga dan iska da duniya ko? Salon magana da yayi