Sashe 123
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya zagaya back seat ya bude ya shiga ya zauna ita dai sai kallonsa take. Cikin tausayinta ta kai hannunsa dake rike da tissue ya fara goge mata hawayenta. Dan Allah ku daina fada da juna, Ummi bata jindadi kuma ni abun zai shafa, ni burina kowa ya so ni na zauna da kowa lafiya, amman ba irin son da zai saka ku fada da juna ba, a yadda na saba da rayuwa a nan ko na koma can ba za su karbe ni ba, kuma zamana a nan ba zai saka su kyale ni ba Babu inda za a kaiki, mune familynki a yanzu, I'm sorry zamu gyara ni da Ameer ba zamu sake fada ba, Ummi kuma ba zata sake miki maganar garinku ba ki daina kuka Ta daga masa kai sannan ta mika hannu ta karbi tissue din ta kwanta jikin kujera, shi kuma ya bude motar ya fita zuciyarsa na sosuwa da hawayen da ya gani a idon Waira, ba taba jin damuwa da matsalarta irin yau ba. Kuma bata taba bashi tausayi irin yau ba. Har ya isa makarantar kallon fuskarta yake a madubi kamar zai yago naman fuskar ya cinye, damuwarta ta haifar masa da damuwa fiye wanda ya taba kasancewa a baya. Yana fakawa bakin gate din makarantar ta bude motar ta fita ba tare data sake kallonsa ba tun bayan da ta gama magana da shi a dazun, kasa tafiya yayi sai kallonta yake har ta shige cikin school ya daina hangota sannan ya sauke ajiyar zuciya. Kusan a takure ta wuni a makarantar duk wani darasi da ya kamata ta maida hankali ta rubuta ko ta fahimta sai ta kasa yin ko daya, gaba daya rayuwarta ta baya sai ta dawo mata, sai tunanin yadda ta rasa abubuwa take, farko garinsu da Eid, daga baya Shuraim ta sabu da Nimra ta rasata ta sabu da Ummi da Ameer gashi shakuwa na shiga tsakaninta da Maleek a yanzu, sai kuma ace Ummi ta maida ita garinsu? Garin da suke neman kasheta? Idan kuma ta cigaba da zama a gidan ta san zata cigaba da haifarwa da Ummi damuwa, bayan kuma bata cancanci haka daga gareta ba bayan duk abubuwan da ta yi mata na kyautatawa, kana a yanzu ta san Ummi ba zata aminta da ita ta zauna da ita kamar da ba, bayan ta gama bude mata sirrinta. A lokacin da aka kada karaurauwar break kowa ya fita gurin cin abincinsa masu kudi suka nufi gurin siyen abun da za su saka a cikinsu ita kuma sai ta kebe kanta can bayan karshen kujerar dake class dinsu ta zauna a gurin tana ta kuka, ta kasa fita daga ajin ma balle har ta ci wani abu, gashu bata ci komai da suka fito daga gida. Haka dai ta wuni cikin kuka da tunani da takura har aka tashi, ta yi zaman da yayi awa daya sannan direba ya zo daukarta ta shiga motar cikin wani irin yanayi na damuwa da bak'inciki, a can idan aka tashi daga makaranta tana daukin zuwa gida saboda tana jin kamar karatun da yan makarantar takura ne a gurinta a yau kuma sai ta samu kanta ta fargaba da tsoron komawa gida. Direban na fakawa ta bude ta fita ta tura kofar falon ta shiga, babu kowa a falon sai Ummi Hanne na zaune kasa tana matsa mata kafafuwanta. Ummi ta lura da damuwar sa Waira take ciki domin ta ga hakan a idonta da fuskarta, hancinta har yayi ja tsabar kukan da ta sha a yau. Dinning ta nufa ta aje lunch box dinta ta nufi stairs ba tare da ta yi ma Ummi abun da ta saba ba, wato hug da murnar dawowa daga makaranta. Ummi ta bita da ido har ta haye sama, sannan ta dauke kafafuwanta ta mike tsaye lunch box din ta nufa ta bude sai ta tararda abinci a yadda ta zuba mata shi. Ummi bata jidadin ganin Waira bata ci komai ba domin ta san kamin ta fita ban da kuka bata karya da komai ba, dan haka ta yi hanzarin nufar kitchen ta dauko cake din dake cikin fridge ta saka a oven ta dumama mata ta hada mata tea mai kauri ta dauki plate ta bude gurin da take ajiyar biscuits da chocolate ta zuba mata ta dauko dayan plate din ta zuba mata shimkafa da miyar da aka girka domin ta san zuwan Ameer tana kan gwada cin abincin da suke ci saboda ya koya mata, sai dai ba kasafai take ci ba. Karamin bowl ta dauko ta saka mata boiling eggs uku ta dauko babban tray ta jera komai a kai, sannan ta dauko ruwa ta dora sama ta dauki tray da kanta ta fito daga kitchen din, Hanne na ganinta ta yi saurin ta shi zata rika mata. Hajiya kawo a kai Aa ni zan kai mata da kaina Ummi ta nufi stairs ta isa har bakin kofar Waira ta murda kofar ta shiga, kasa ta aje mata tray domin bata cikin dakin, bayan ta aje ta nufi bandakin inda take jin motsin ruwa tana dan jin tsoron Waira ta tsaya bakin kofar. Na ga baki ci abincinki ba, ga wani nan na kawo miki ina son kamin na dawo ki cinye, idan ba haka ba zan maida ke garinku, idan kina son zama a tare da ni to ki ci abinci karki haifar da kanki matsala Ta juya ta fice daga dakin tana sauke ajiyar zuciya, ita kanta bata son rabuwa da Waira domin ta shaku da ita, a zuwa yanzu kuma bata gama yanke hukunci akan ta bar Waira ko ta kaita wani gurin ba, ko kuma ta maida ita garinsu. Hajiya wai mai darasin Waira ne ya iso Maganar da Hanne ta yi ne ya dago hankali Ummi dake tunani ta kalli Hanne da baro jikin kofar falon ta nufo Ummi dake saukowa tana fadin haka. Mai darasin ta kuma? Ai ya dade be zo ba, kuma yanzu ta dawo daga makaranta ba lokacin zuwansa ba ne sai La'asar Toh shi ne dai ya zo yace a kirata Bari na yi magana da shi Ummi ta fada sannan ta juya ta koma sama dakinta ta shiga ta dauko mayafi ta saka ta fito ta nufi kofar, tana budewa sai ta yi arba da shi yana tsaye. Sannu Malam Yauwa sannu Hajiya, ya gida Lafiya kalau, kwana biyu ka daina zuwa lafiya? Ba ni da lafiya ne shiyasa Subhanallahi amman irin haka idan ta samu kamata yayi ka rika kira, saboda a san halin da ake ciki, a dauki tsawon lokaci babu labarinka, kaga idan da halin mu taimaka sai mu taimaka maka ma Zamu kiyaye gaba, Waira tana ciki? Eh amman yau ba zata samu yin darasi ba ita ma bata jindadi Ayya ni ma ba darasin na zo ba, na zo na yi magana da ita ne kawai dan Allah Hajiya ki kira ta mu gaisa sai na mata ya jiki Ummi har ta yi kamar tace masa ba zata samu fitowa sai kuma ta amsa masa da Okay, ka dan jirata tana fitowa Toh na gode Ya juya ya nufi gurin da suke darasi Ummi kuma ta juyo ta dawo cikin falon, kai tsaye ta nufi dakin Waira wannan karon zaune ta same ta gaban tray da ta aje mata sai cin abincin take da sauri tana hawaye hakan ya tabbatarwa da Ummu bata son komawa garinsu ko kadan. Ummi ta dauki lokaci tana kallonta da tausayi sannan ta yi mata magana. Idan kin kare ki fito mai miki lessons yana son ku gaisa Ta juyo da sauri ta kalli Ummi bakinta na cike da abinci idonta kuma na cike da hawaye. Ummi ta juya ta fice sai ta aje cin abinci ta shiga bedroom ta wanke hannunta ta fito ta sauko falon da babu kowa daga Ummi har Hanne, ta isa gurin kofar ta bude ta fita waje ta gangara gurin da suka saba zama suna yin darasin. Tsaye ta same shi ya bata baya nesa da shi ta tsaya sai ya juyo ya kalleta doguwar rigar abaya ce a jikinta ta baza bakin gashinta dake jike da ruwa ya warwada har bayanta. Takowa yayi ya iso har inda take ta kai hannu ta taba fuskarta ya shafa kumatunta yana kallon idonta, a take ya fara rikida daga mai mata darasin da ta sani zuwa wani dabam, bude ido ta yi ta mugun mamaki tana kallonsa jikinta na rawa. Lokaci yayi da ya kamata ki koma gida Ta matsa baya tana girgiza masa kai zata yi magana ta ji wani abu ya fisgeta sai ta tafi suuuu zata fadi kasa, yayi hanzarin riketa ta fado jikinsa, sai ya sumbanci goshinta ya rumgumeta ya rufe ido, yana kusa fuskarsa cikin gashin kanta... Yana lumshe idonsa dake cike da yake jin kamar hawaye su zubo masa. Deep down abun da Namra ta masa guri ya masa zafi, irin zafin da yake jin da ma ace komai be faru ba tun farko. Are you okay Ameer Ya bude ido ya kalli Humairah wacce isowarta kenan tana tsaye a gefensa, kallonsa take da kulawa ganin damuwa a idonsa. Sai ya sauko saman motar yayi tsaye. Can i hug you Kamin ta ce masa komai ya rumgumeta, sai ta ware hannayenta tana yin baya a hankali, so take ta raba jikinta da nashi shi kuma ya rike ta gam. It's public place Ameer ana kallonmu I don't care i just need i hug Shiru ta yi kunya ta kamata saboda daidaikun mutanen da ke wucewa suna kallonsu some people ma may think ko su masoya ne, ba dan halin da ta ganshi a cikin yanzu ba, ba zata yarda yayi mata wannan rumgumar a guri kamar wannan ba. Sai da ya sake ta sannan ta kalleshi Me ya yaru? Shi ma kallonta yayi yana sauke ajiyar zuciya. Abu daya ne, wanda ya saka nake nadamar haihuwa ta da aka yi a yau? Ta matsa ta jingine jikin motarsa ita da shi suna kallon karamin gate din shigowa asibitin. Fada min damuwarka maybe i could help Ta fada muryarta na bayyana damuwarta, irin damuwar da ita ma kanta bata san me yake damunta ba.