Sashe 160
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
gani kin gani ba? Miye na kuka? Ummi i miss you I miss you too Baby Nuwaira, ya sabon gidanki Babu dadi saboda babu ke a ciki Ummi Zaki saba da sannu, mussamman idan kika gina naki iyalin A hankali Ummi take magana irin na masu ciwo yana shafa fuskar Nuwaira. Maleek ne ya shigo dakin ya aje basket din daga gefen gado Ummi ya zauna a kusa da matarsa yana kallon mahaifiyarsa zuciyarsa babu dadi. Maleek ya kake? Lafiya kalau Ummi ya jikinki? Alhamdulillah ina ta ibada Allah ya baki lafiya Ameen Ga abinci nan Nuwaira ta girka miki Ummi ta dan daga kai ya kalli basket din tana murmushi irin na masu karfin hali. Tare kuka girka? Kamin ya bata amsa Nuwaira ta ce Ni kadai na girka Ummi saboda ke na yi, dan Allah ki ci Zan ci mana dole na, Nuwaira ce yau ta girka abinci ta kawo min? Alhamdulillah Allah na gode maka da ka bani ikon ganin wannan ranar, Mahmood dauko plate da spoon na ci abincin yata Mahmood ya tashi ya fita tana murmushi, sai Ummi ta kama hannun Nuwaira ta kama na Maleek ta saka na Nuwaira ciki. Maleek ga Nuwaira na san an baka amanarta tun a ranar da aka daura muku aure, amman yau ina son na kara jadada maka Nuwaira bata da kowa a duniya sai ni da mahaifinka sai kuma kai da yan'uwanka, ita din amana ce a gurinmu, dan Allah karka cutar da ita, ka rike ta amana ka nuna mata soyayya da kauna kamar yadda ta nuna maka har burinka ya cika, karka yarda ta zubar da hawaye akan ka karka surfa mata bakinciki namiji, karka saka ta yi nadamar kasancewarta a cikin addinin nan karka saka ta ji kewata idan bana nan saboda wani mugun abu da zaka yi mata, ka je har garinsu ka ga gidansu da irin rayuwar da ta taso a cikin, yarinya ce da bata san gata ba, dan Allah Maleek ka zame mata gata rashin uwa da uba, karka yarda wani abu ya rabu sai mutuwa Maleek ya jinke hannun Nuwaira hawaye na sauko masa. Na miki alkawari matukar ina raye Nuwaira ba zata taba rashin wani abu ba, kuma ba zan taba cin amanarta ba, sannan na miki alkawari zan maye mata gurbin uwa da uba zan bata duk wani gata da ta rasa Ummi ta yi murmushi hawaye na sauka a idonta. Sannan ta dubi Nuwaira da tun da ta fara maganar take kuka. Nuwaira ki rike mijinki kinji? Karki yarda rudin shaidan ko duniya su saka ki juya masa baya, idan yace yana so ki fishi so, idan ya ce baya so ki fishi gujewa abun matukar ba sabon Allah ba ne, aljannar nan da kike jin ana yawan fada miki ta karkashin kafar mijinki ne, wannan hade hannun na ku da na yi ki rike shi har aljannah. Gobe zan koma asibiti kuma zamu tafi tare da Maleek da Namra da Ameer da Mahmood ban sani ba ko Allah zai amince min na dawo cikinku iyalina na sake wata rayuwar kuma ban sani ba ko mutuwata a kusa take, wannan dai wasiya ce nake bar miki ki rike addininki da kyau Cikin kuka Nuwaira ta ce. Ummi mi yasa ba za a tafi da ni ba? Abiey ne yace be yarda Maleek ko Ameer su tafi da matan su ba, amman kar hakan ya saka ki ji komai a ranki kinji? Nuwaira ta daga kai ta kwantar da kanta jikin Ummi tana kuka. Mahmood dake tsaye jikin kofar rike da plate ya kasa shigowa kuka yake. Sai da ya ji motsin fitowar Maleek sannan ya bar jikin kofar kuma ya kasa sauka gaba daya. Maleek ya fito hawaye na masa zuba suna hada ido da Mahmood sai suka fashe da kuka marar sauti, Maleek ya rike karfen stairs din da karfi yana zubar da hawaye. Mahmood kuma ya ba shi baya shi ma yana hawayen. Sun dauki lokaci a haka kamin ya saka rigarsa ya share hawayensa ya koma dakin rike da plate din da spoon, har lokacin Nuwaira na jikin Ummi tana kuka Ummi na shafa bayanta tana murmushi. Mahmood ya aje plate din zai fara zubawa sai ta hana shi. No Allah ya maka albarka ya baka mata ta gari, amman bari Nuwaira ta zuba min da kanta Nuwaira dago cikin kuka ta shiga zubawa Ummi shifar da miyar sannan ta zauna a inda ta zauna dazun ta yamutsa abincin ta fara bawa Ummi a baki tana ci a hankali idan ta bawa Ummi two spoon sai ta bawa kanta one spoon da haka har suka gama cin abinci, and this is one of the best moment da Nuwaira take jin ta yi spending tare da Ummi. Domin ita ta dafa abincin da kanta kuma ta yi feeding dinta, Nuwaira tana jin Ummi kamar uwar da ta haifeta, hakan ya saka zuwan da ta yi sai ta labe a jikin Ummi kamar wata mage, sam bata fito falo ba a dakin ma tana kan gadon Ummi a jikin Ummi take kwantar da kanta, bata tashi sai idan lokacin Allah yayi, Mahmood ya saka wayarsa yayi ta daukarsu hoto. Sai da yamma Ameer ya shigo gidan, domin tun safe yana can gurin hada hadar tafiyar da za su yi gobe tare da Abiey. A nan ma sai da Ummi ta yi musu ta su wasiyar shi da Mahmood da Maleek, kusan sai da ta saka kowa kuka, daman Ameer be gama warkewa daga kukan wasiyar da ta yi musu a jiya ba shi da Humairah domin jiya din a nan wuka wuni, shiyasa a yau ya tashi da rashin lafiya. Ana gama sallah Magariba Maleek ya ce Nuwaira ta tashi su koma, a nan fa aka fara sabon yaki yana janta yana rike rigar Ummi tana kuka ita ba zata tafi ba. Ka barta ta kwana a nan mana in ya so gobe daga Airport sai ta koma gida Maleek ba musa shawarar Ameer ba ya yarda Nuwaira ta kwana a gidan, shi kuma ya koma saboda karasa shirye shirye. Aka bar Ummi daga ita sai Ameer da Nuwaira a dakin. Tashi ki debi abinci ki ci Ta sauka kan gadon tana share hawayenta ta fita. Sai Ummi ta kalli Ameer ta ce. Ku so junanku dan Allah Ameer, na san kai ne mai saurin fushi mai daukar zafi, dan Allah ka lallaba da kanenka musamman Namra bata da kowa a yanzu sai ku, kuma karka sake biyewa son zuciya da fushinta ka aikata wani ko bayan raina Ameer ya tashi daga inda yake zaune ya koma kusa da gadon Ummi ya zauna a kasa ya dora kansa a cinyarta ya lumshe ido. Nuwaira na tsaka da cin abinci Namra ta shigo dakin tare da Abiey da ya tarbota a airport domin jirginsu saukar dare yayi daga Katsina zuwa Abuja. Nuwaira bata san lokacin da ta bar dinning din ta isa gurinta da sauri suka rumgume juna. Ya Maleek be ce min zaki zo ba, i miss you Abiey yayi murmushi. Toh idan kun gama missing sai a gaishe ni ko? Nuwaira ta rufe ido sam bata lura da Abiey ba sai a lokacin. Be bi ta kansu ba ya haura sama ya shiga dakin matarsa, sai dai kukan da ya tarar tana yi ita da Ameer ya saka zuciyarsa tsinkewa. Jiki a sanyeye ya karasa cikin dakin ya zauna. A madadin ka zama mai karfin hali sai ks koma kai ma kana kuka kamar ita? Ameer ya dago ya dubi. Bar ni na yi kuka Abiey ba ni da kowa a duniyar sai Ummi, ba ni da sauran farinciki a yanzu bayan ita Namra ce ta shigo dakin rike da hannun Nuwaira, Namra ma kasa jurewa ta yi daman tun a waya Ummi ta yi mata nata wasiyar na ta rike Nuwaira domin ita kadai ce yar'uwarta a yanzu bayan mutuwar Nimra, ita ma kuma Nuwaira a yanzu bata kowa sai su. Sai kusan shan biyu na dare Ameer ya bar gidan zuwa gidansa Nuwaira kuma ta kwana a gadon Ummi ta shige jikinta kamar wata wadda ake shayarwa. Humairah na ganin fuskar mininta ta san be fita daga damuwar ciwon Mahaifiyarsa ba, domin tun da suka yi aure bata taba ganinsa a cikin wani yanayi marar dadi kamar a jiya da ya tafi da ita gurin Ummi ba kuma ta yi musu nasiha akan zaman aure da hakuri da juya, bayan ta gama fadawa Humairah cewar ga anta nan ya bata amana. Ruwa ta fara kawo masa ya karba ya sha sannan ta zauna kuss da shi sanin kanta ne tun kamin ya furta yana sonta idan yana cikin damuwa rumguma ce abun da yake so, dan haka ta matsar da jikinta ta rumgume mijinta, sai ya sauke ajiyar zuciya ya lumshe ido. Ameer ya kwana a cikin wani yanayi na damuwa da be taba samun kansa ba, sai dai Humairah ta yi iyakar kokarinta na ganin ta cire mijinta a damuwa ta hanyar kwantar masa da hankali da kalamai masu dadi da addu'a kamin babbar ibadar aure ta biyo bayan. Da wuri ta shirya masa abun karyawa sannan ta shiga ta tasheshi suka yi wanka tare cikin farinciki da kaunar juna, da farko kunyar wanka take da ta fahimci mijinta dan duniya mai son rayuwar wayewa da soyayya dole ta sake masa jiki. A tare suka karya kumallo ta ciyar da shi shi ma ya ciyar da ita sannan ya shiga ciki ya shirya ta taimaka masa da saka turare da talkama. Amman Dear ina jin tsoro kamar ba zan iya zama a gidan nan ni kadai ba Ya rumgomota yana shafa saman kirjinta. Yeah na manta ban fada miki ba, mun gama magana da Maleek zaki koma gidansa ki zauna tare da Nuwaira ne har mu dawo, dan haka ki shirya komai na ki da yamma direba zai zo ya dauke ki Okay, amman zan yi marmarinka sosai Me too Ya fada yana sumbantarta, kamin ya duka kasa ya kai hannunsa ya rike bayanta ya dora kansa saman cikinta. Hi Baby zan tafi sai na dawo ka ji Ta saka dariya tana ja da baya. Lafiya kake kuwa Sai ya mike