← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 165

Sashe 68

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

damu, haka yake takurawa kowa a gidan nan kin san halinsa ai ko? Ta daga kai. Ina son na tafi gurin Sulem Yanzu ki bar shi ya huta tukuna, idan ya huta zamu tafi gaba daya har Ummi mu gaisa da shi sai ki sake ganinsa, yanzu zauna ki ba ni labarin i da kika san shi Ta zauna a kasa sai dai ta kasa labarta komai, sai tabin sarkar wuyanta take idan ta dago ta kalleshi sai ta yi murmushi kamar ba ita ce hawaye ya gama yi mata zuba ba. Toh shiga ki fadawa Ummi kin ga Sulem tun da ba zaki ba ni labari ba Ta mike tsaye da sauri daman abun da take nema kenan, da gudu ta hau stairs din kamar zata zame ta fado ta tura kofar dakin Ummi ta shiga sai ta samu bata cikin dakin, fitowa ta yi ta nufi dakin Nimra ta tura idan bata samu Ummi ba ai zata iya labarta Nimra sai dai tararda da ita da ta yi tana kuka ya saka jikinta yayi sanyi sai ta juyo ta fito ba tare da tace mata komai ba. Dakinta ta nufa tana shiga ta sami Ummi da Dr Zainab a dakin zaune Ummi tana hawaye. Take kwarin guiwar data shigo da shi ya mutu sai ta tsaya jikin kofar tana kallon Ummi. Waira kin san shi ne? Ummi ta tambaya cikin karfin hali domin bata manta dazun data fita daga dakinta tana fadin Sulem ba. Wannan ne karo na farko da Waira bata damu da tambayar ko son jin dalilin Ummi na kuka ba, ta karasa cikin zumudi ta fara fada mata abun da zata iya tunawa a game da Shuraim. Sannan ta nufi gurin data aje tsofin kayanta na fata na ainahin garinsu ta bude ta dauko takardar da yayi mata rubutu a jiki ta nunawa Ummi. Ya ba ni wannan da babaken mutane za su kawo ni Habuja Ummi ta karbi takardar ta bude. Ban san iya inda tafiya zata dauki be, ban san iya inda kaddara zata tsaya da ke ba, ban san yaushe Allah zai sake gadamu ba, a duk inda zaki karance ina fatar guri ne mai aminci da natsuwa. Ya kai wanda zai ci karo da wannan sakon ka ji tsoron Allah karka cutar da ita, fruits ne abun da ta fi ci, kuma ta tsoro da rashin sabo da mutane da wuri, Allah ya tsare ki Dr Shuraim... Ya rubuta daga karshe, Ummi ta mikawa Dr Zainab takardar ita ma ta karanta sannan Waira ta karba ta nade a hannunta ta tashi tsaye ta fito dakin, so take ta je ta nunawa Sulem bata jefar da takardar da ya bata ba, tana nufo Stairs ta fara saukowa dai ga Maleek ya fara haurowa sai ta juya da sauri ta koma. Mahmood dake zaune yana hangen abun da ke faruwa ya saka dariya yanayin yadda ta juya ta koma din da sauri ya nuna tsoron Maleek take. Bata shiga dakinta da Ummi take ciki ba sai ta shige bedroom din Ummi da babu kowa a ciki a zatonta Maleek zai yi magana da Ummi ne ko kuma dakinsa zai tafi. Tsayawa ta yi a dakin tana sauraren idan ya wuce sai ta fito, shi kuma hango Ummi da yayi a dakin Waira kasancewar kofar a bude take, sai yayi reverse ya dawo baya. Kamin ya tura kofar dakin Ummi sai Waira ta bude masa a zatonta ya wuce ita kuma ta fito, ita da shi duk suna rike da kofar ne, ita zata bude ta fita shi kuma zai tura ya shiga. Sakin kofar ta yi ta matsa baya shi kuma ya samu damar shigowa ya rufe kofar. Ba saboda ita ya shigo ba amman hakan be yana shi yi mata ishara data zauna da ido ba. Ta nufi gefen gadon Ummi ta zauna a kasa tana kallonsa da idanuwanta da ya fi tsana a yanzu domin haushi take ba shi, ta boye takardar hannunta a bayanta ta matse gadonta ta natsu sosai irin natsuwar nan ta tsoro. Yau wardrobe din Ummi ya nufa ya bude ya fara dubawa a hankali domin ita kadai ce be bincika na a kwana uku da ya kwashe yana bincikar akin a duk lokacin da ya samu sa'a Ummi bata ciki, yadda yake bin komai a sannu yana maida shi mazauninsa a yadda ya taba shi sai ka rantse da Allah criminal ne da ya kware a sata. Ita dai Waira kallonsa kawai take kamin ta mike tsaye ta nufi inda zomonta ya leko ta dauke abunta ta rike. A hankali ya rufe wardrobe din sannan ya juyo ya kalleta tana shafa zomon tana kallonsa. Ya bude dayan side din ya fara dubawa daga samna gaba daya akwati ne da Ummi ta saka a gurin. Hankali kwance ya bude akwatin yana saka yadda zai fadawa Ummi cewar Waira ce ta ce ya duba mata tufafinta a gurin, tufafi ne sabin da ba a dinka ba a ciki lace da atamfa kasan kayan kuma wata karamar jaka ce irin ta saka takaradu, sai da ya cire kayan sannan ya dauko jakar dake lake da karamin makulli, aje jakar yayi ya maida akwatin da ya rufe sannan ya rufe wardrobe din yana ta mamakin me ke ciki fatansa dai ace abun da yake nema ne, domin ya duba gun da Ummi ke aje takardunta be samu komai a gurin ba. Sai da ya gama ya dauki jakar ya nufi kofa sai kuma ya juyo ya kalli Waira. Sauran na ji kin ce na dauki wani abu, na cire miki ido Yana maganar yana zare mata ido, ita dai idon kawai ta sakar masa har ya fice, sai da ta ba shi mintunan da take kyautata zaton ya isa ya boya sannan ta nufi kofar ta bude ta fito tana sanda ta sauko kasa, sau daya ta kalli gurin da Mahmood yake zaune ta dauke kai bata ce masa komai ba, shi ma kuma be ce mata ba har ta fice. Harabar gidan ta fara kallo tana rabon ido bata san inda ya shiga ba balle ta bi shi, sai dai ta ga motar da ya shigo dan haka ta nufi gurin motar ta tsaya tana leka ciki ganin babu kowa ya saka ta zauna a gurin ta jingina da motar, a wayonta duk inda suka a cikin gidan dole idan suka fito za su tafi zata gansu ai idan tana gurin. NAMRA POV. Namra ta yi musu tarba irin wacce ta dace da mosoyi ita da Yesmin da Hanne suka jera musu abubuwan da aka shirya musu. Zaman minti talatin da ta yi a falon sai da ya fara bata labarin haduwarsa da Waira, a iyakar gaskiyarsa ya jidadin ganinta kuma ya kasa boye hakan, ita dai bata ce masa uffan ba akan Waira ba har ta fita ta ba su guri domin cin abinci. Dr zaka kufular da yarinyar nan fa, taya zaka rumgume wata budurwa a gabanta kuma ka zo kana ta bata labarin haduwarku? Dr Shuraim ya aje kofin lemun dake hannunsa. Haba karka min kuskuren fahimta mana, Namra ba yarinya ba ce ai tasan kanta ba zata ce kishi take akan haka ba, kuma ni ba son wannan yarinyar nake ba, kawai dai ta shiga raina ne sosai dan zaman da muka yi na kwana biyu daga asibiti zuwa gidanmu Allah ya sanya shakuwa a tsakaninmu, baka lura ita ta yi tsalle ta rumgume ni ba? Eh amman mace bata son ko kwalliyar wata macen ka yaba a gaban wata fa, kai baka lura yanayinta ya canja ba, kuma ka zo kana ta son dole sai ka fada mata yadda kuka shaku Shuraim yayi murmushi. Kamal kana nufin kishi take? Ai dalili ake ma kishi da ace ganin ta yi nace jna sonta shi ne zata yi kishi Ka dai kiyaye kar garin neman gira a rasa ido, kuma karka manta abun da ya kawo ka a gidan nan Ba zan manta ba, ni da na dade ina jiran zuwan wannan ranar, kuma zan manta a yau? Kaima tunaninka ne ya baka wani abu amman babu abun da kake tunani a zuciyata Be sake cewa komai ba, ya bude fruit salad. Shuraim be ci komai ba bayan lemun da Namra ta zuba masa ya sha, Kamal ne kawai ya ci abinci shi ma kuma ba sosai ba. *Littafin WANI GARI na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660* AMEER POV. Tun da ya shigo gurin Humaira ta lura da yanayinsa, yau ya dan fi sakewa fiye da jiya da shekaranjiya. Gorar ruwa ta dauka ta nufi inda yake, sai da ta fara aje masa ruwan sannan ta ciro biro da dan karamin littafi. Me za a kawo? Ya daga kai ya kalleta be jin zai iya amsa mata dan haka ya sauke kansa ya saka hannu aljihu ya ciro wayarsa ya fara latsawa. Me zaa a kawo maka? Ya mata banza, ta daure ta sake tambaya a karo na uku. Me za a kawo? Idan na bar gurin nan baka fada min ba, ko na kira ni ba zan dawo ba, me yasa kai a rayuwarka kake son untatawa mutane ne? Kai baka san dan adam yana da daraja ba? Ya dago ya kalleta a hankade. Nuna min inda taki darajar take, kina mace kin so kina aikin siyar da abinci a karkashin mahaifina, kina daukar order ko wane shege da dan'iskan, sannan ki tsaya a gabana kina min zancen daraja, be kamata kalmar ta fito daga bakinki ba ai, domin ke baki da ita, kudi su ne daraja, daraja shi ne ka cire talkami wani ya zo da gudu ya dauka ya wanke maka, ka zo restaurant wata ta zo ta tsaya a gabanka da abun rubutu tana jiran ka fada mata abun ka kake son ci ta kawo maka, daraja ka shiga mota idan ka tsaya mutane ta nufoka suna son ka ba su kudi, daraja ka zama mai ikonka kanka ba a karkashin ikon wani ba Ta kalleshi da kyau zuciyarta cike da bakincikin kalaman da ya fada mata. Dan'adam ba shi da zabin rayuwa kamin a haife
Chapter 68 · 0% Book details