← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 165

Sashe 134

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai dan addinin musulunci da ta shiga ya kara mata kwarjini da farinciki a gurin kowa. Liyafa Mummy ta shirya mata, sai dai ita kasa cin komai ta yi saboda tunanin gaba da take. Bayan sun gama cin abincin Daddy ya aika yarsa ta dauko masa ajiyar da yayi a dakinsa, ya gabatarwa da Nuwaira, sarka zinari ce mai matukar ktau da tsada irin mai cika wuya wadda ke hade da abun hannu da agogo. Wannan duka na ki ne, ina fatar idan kin tafi ba zaki manta da mu ba, musamman ma ana Ameer, yana yawan maganarki kusan ya zama kamar wani soko akanki, ki rika tunawa da shi kina masa addu'a ko dan silar shigar da yayi miki a addinin Allah mai tsabta da natsuwa Ta saka hannu biyu ta karba, ba lallai ta fahimci minene ba saboda a garensu ba haka ake sarrafa zinariya a yi ado da shi a garinsu ba. Amman ta san abu ne mai kyau da tsada ganin yadda yake daukar ido. Zinari ne wannan, yana da kyau sosai Ta girgiza kai da sauri. Ba zan iya karbar wannan ba yayi yawa No ba a maida kyauta karki ce haka ki karba mana Mummy ta fada tana kallonsu da murmushi. Godiya sosai Nuwaira ta yi ma Daddy har ta rasa kalaman hadawa ta nuna masa farincikinta. Mummy ma ta yi mata kyautar turaruka da earring masu kyau na GL da lace mai kyau. Suka rakota har gurin mota ta shiga suna daga mata hannu. A tunaninta gida Ameer zai nufa da ita kai tsaye bayan ya bar gidan Daddy. Sai ganin ganin ya faka a gaban wani gate ya fita ta bude gate din ya shiga da motar ya sauya tuninaninta. Ina ne? Ta tambaya a lokacin da ya bude mata motar take kokarin fitowa. Kakata yau suka tare, na fada mata zan kawo ki, ki musu bankwana Kamin ya rufe motar Humaira ta fito rike da waya a kunnenta amman hakan be hanata yin welcoming din Nuwaira ba, cikin kyakkyawar tarba fuska a sake. Ameer ya wuce gaba Nuwaira ta bi bayansa har suka shiga cikin falon da ba a gama sakawa kaya ba, shi ya fara yi mata nuni da inda zata zauna sannan ya shiga dakin farko dake cikin falon. Humaira ta shigo after minutes da zaman Nuwaira a falon tana sake mata maraba da zuwa. Sannu da zuwa, Ameer yana yawan ba mu labarinki, kusan kowa ya san ki tun farko fara haduwarku ya fada kin yadda ya rikice akanki, bari na baki abun sha kar na cika ci da surutu Ta tashi ta shiga dakin da ke nuna madafa ce ta dauko mata ruwa da taliyar da ta girka, domin su ne kadai abubuwan da zata iya samu for now a gidan, kasancewar tarewar ta wuri ce kuma hankali Ameer ba kwance ba, be gabatar musu da komai ba, arzikinsu daya Daddy be manta da su ba, shi yayi musu komai a gidan. Nuwaira ta kai hannu ta dauki ruwan ta rike kamar wadda bata san abun da zata yi da shi ba. Can kuma ta daga kai tana kallon Ameer davya fito dakin Hajiya na bayansa tana takawa a hankali da sandar guragu, Bahijja na bayanta sai leken Nuwaira take kamar ba zata karaso kusa da ita ta kalleta ba. Sannu da zuwa yau bakuwar Ameer ce a gidan mu Nuwaira ta mike tsaye tana kallonsu, sai wani irin take ji, ta bakuncin mutanen da suka san da labarinta ita kuma bata san su ba. Hajiya ta karaso ta zauna tana kallon Nuwaira ita dai zuciyarta bata gamsu da yarinyar ba, ba dan tarbiyarta ko wani abun ba, sai dan ganin take ta fito daga bangaren Ummi ne, ganin take idan ya aureta Ummi zata sake dauke mata shi ne bayan duk abun da ta yi da farko, hakan na nufin ta ci nasara kenan. Cikin rashin natsuwa da sakin jiki Nuwaira ta gaisa da su, sannan ta yi musu sallama suka fito ita da Humaira ganin kamar Ameer ba zai fito yanzu ba. Da alama kin matsu ki bar gidan nan Ta kalli Humairah bata san me zata ce mata ba, domin ta san gaskiyar Hunairah ta fada, tabbas ta matsu ta fita saboda rashin sabon da bata yi da su ba. Karki damu, zamu taba da juna babu jimawa, domin na san Ameer yana sonki sosai irin son da ya wuce kwatance balle a kwatanta, ya wuce zane haka ma ya fi karfi fada, balle kuma ace alkalami ya rubuta, fatana dai ki share masa hawayensa ko san wahalar da ya sha Kallon Humaira kawai Nuwaira take kamar wadda bata fahimci abun da take fada ba. Fitowar Ameer ne ya saka Humairah ta dan matsa baya domin ba shi guri. How kika ji sabon gidan na ku? Na ji dabam saboda ban saba ba Zaki saba sannu, ki yi list din duk abubuwan da babu, idan ba zo sai ki ba ni a siyo, kuma ki gyara min daki daya zai zama ina da gida uku kenan gidan Daddy, Ummi, sai kuma nan Humairah ta yi dariya. Ka zauna a nan kuma? Kai da zaka yi aure? Aure? Yeah.. Ta furta tana kallon Nuwaira, sai yayi murmushi ya girgiza mata kai, a take murmushin dake fuskarta ya gushe. How? Ta tambaya without saying it with sound. Sai ya daga mata kafadunsa. Ba kin min baki ba? Addu'ar da kika yi ma dan'uwanki ce Allah ya karba so get ready for your annoying brother Ya kalli Nuwaira. Let's go A tare suka sauka ya bude mata mota ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya bude bangarensa ya shiga, suka bar Humairah da mamaki da kuma tunani kala kala. Tun da suka hau hanya Nuwaira take kallon Ameer har suka kusa isa, shi kam ko da wasa be kalli inda take ba. Ameer ya kake ji a yanzu da kake da iyaye har uku? Sai ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba. Ba dadi, ina ji mn rayuwa ta juye min upside down amman zan saba, kowa da kaddararsa Ta dan ji babu dadi ganin yanayinsa ya sauya sakamakon tambayar da ta yi masa, ta kai hannu ta taba shi. I'm sorry Ya kalli hannunta sannan ya kalli fuskarta sai kuma yayi murmushi. Yanzu ba kin musulunta ba, kin san halal da haram dole ki kiyaye wannan idan kin koma garinku Ta yi saurin dauke hannunta domin gaba daya ta manta da wannan haramcin. Bata sake cewa komai ba har suka isa, ya fara a daidai balcony din kofar Ummi. All her thoughts is zai kashe motar ya fita ya zagayo ya bude mata, sai ta ga ya kalleta yana murmushin da ya zame masa dole ne kawai. Finally kin ga Daddy daman kin taba ganinsa ai, amman dai yau kun gaisa kun san juna sani na musamman, kuma kin ga third parents din na, na san baki bukatar komai a yanzu right? Ta daga masa kai sai kallonsa take kamar yau dai jin kallonsa ya fi mata dadi. Ba zan shiga ciki ba, a nan zan sauke ki kuma ina miki addu'ar Allah ya sauke ki lafiya, ya tabbatar da ke akan addinin nan kuma ya kareki ya saukar miki da natsuwa da kwanciyar hankali a duk halin da zaki samu kanki, na gode sosai da kika ba ni danar saninki, kasancewa da ke ya janyo hankali zuwa ga alakata da Ummi, ido ya bude na fahimci rayuwa a daidai fiye da baya da nayi mata fahimta baibai, na kasance da ke a yanayi na nishadi da jindadi, sanadinki na san kishi, sanadinki na san so kuma sanadinki na san zafin rabuwa thank you so much for the experience, ina miki fatan nasara a duk rayuwar da zaki samu kanki a gaba, and i hope zaki bar kyautar da na baki saboda kin rika tunawa cewa kin taba kasancewa da wani Ameer Shi yake magana ita take hawaye har ya gama, ya dauke idonsa daga barin kallonta. Idan kin fita ki bude baya ki dauki kayanki Ta bude motar ta fita tana jin zuciyarta na narkewa, cikin rashin kuzari ta rufe masa motar ta bude baya ta shiga ta kwaso kayan da Daddy ya bata da Mommy tana kallonsa ko zai juyo ya kalleta amman yaki ya kalleta har ta kwashe ta fita ta rufe masa motar. Sai da ta fara tafiya sannan ya juyo da fuskarsa ya kalleta shi ma dan ya san ba zata iya ganinsa ba kasancewar bakin gilashi ne kallonta kawai yake tana tafiya hawaye ya sauko masa, kamar ta san son ganin fuskarta yake sai ta juyo tana kallon motar hawaye na sauko mata har wani jan numfashi take kamar zata shide, jin take kamar ya bude motar ya fito yace mata da shi za a tafi har garinsu. Amman har ta gaji da tsayuwa ta juya ta shiga ciki be fito daga motar ba, sai da ta yi minti biyar da shiga ciki sannan ya bude motar ya fito ya jingina da motar yana kallon kofar falon, ya shafa kansa ya sauke ajiyar zuciya, can kuma ya daga kansa sama yana kallon saman, kamin ya juyo ya bugu motarsa da karfi, ya sake shurinta motar. Ya dauki lokaci a haka sannan ya bude motar ya shiga ya dauki hanyar gidansu, da hannu daya yake tuki hannu daya ya shafa kansa gaba daya zafi yake ji a jikinsa ya rasa me ke masa dadi, kamar ya haukace haka yake ji sanin cewar bankwana ne yayi da Nuwaira bankwana na har abada, domin ya san ba zata taba dawowa ba. MALEEK POV. A hankali ya saki curtains din dakinsa ya sauke ajiyar zuciya, slowly ya fito daga dakin ya sauko kasa sai ya ci karo da abun da be yi zato ba. Nuwaira ce kwance akan kujera sai rusar kuka take kamar wadda aka yi ma mutuwa. Sai da ya waiga ya kalli stairs sannan ya zauna a hannun kujerar yana kallon kayan da ta watsar. Me kike yi ma kuka? Kamar jira take sai ta dago tana fada masa abun da ke cikinta. Ameer ne, wai bankwana yayi min tun a yanzu ba zai bari sai gobe ba,
Chapter 134 · 0% Book details