← Book details Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 165

Sashe 28

Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read

sani ya zo ba. Ji yayi ba zai iya shiga ciki da motar ba sai ya bude ya sauko yana kallonta sai wani sham kamshi yake zuciyarsa na halbawa da mugun karfi, cikin wani irin taku na daukar hankali da gwarewa irin ta yan duniyar da take murza musu kambu yadda suke so, Angel ta je a gareshe tana tarbunsa with surprise. Don't touch me Tana isowa ya dakatar da ita, ta fi kowa sanin idan ya ce kar ta aikata abu he meant it tana aikatawa za su samu matsala. I miss you Ameer Waye ya fita da mota yanzu? Ya wani yi kamar bata fahimce ba, sai kuma ta yi dariya tana kokarin yi masa wasa da hankali. Oh... Kawata ce Nanita Really? Kina tunanin ni wawa ne? Ta mika hannu zata fara yaudararsa da kalamanta, ya daka mata tsawa. Na ce karki taba ni, kin fi kowa sanin abun da nake kyama shi ne sharing, and because of that na ware miki komai, na dauke miki komai ashe bayan idona kina iya cin amanata? Nono karka je da nisa Ameer wannan fa kawata ce ta kwana nan ne, yanzu nan ta fita kai kasan ba zan iya cin amanarka ba God Forbid ni zan aikata haka ba, yanzu dai shigo ciki mu yi magana Harara ya watsa mata tun daga saman kanta har kasa, sannan ya kara ja baya. Kin yi sa'a ina jin kyamarki a yanzu, idan ba haka ba, Wallahi sai na kusa kasheki a gurin nan, but matsalar ba zan iya taba ki da hannuna ba ne, ki hada duk wani abu da kika san naki ne ki bar gidan nan we done Ko bahaushiyace ba zata yarda ta rasa wannan gatan na Ameer ba balle kuma inyamura da suka fi kowa sanin zafin neman kudi, zubewa ta yi kasa ta fara rikonsa tana dukan kanta da ke a haske kamar na maza, ko kadan be saurareta ba ya juya ya shige motarsa motar ma da take kokarin tarewa sai da yayi cikinta da ita, da bata yi hanzarin kaucewa ba kadeta zai yi yayi tafiyarsa. Bacin ransa ya karu he never thought Angel zata iya cin amanarsa a bayan idonsa kamar haka, duk da be tabbatar ba amman yasan ta aikata domin akwai alamun rashin gaskiya a tare da ita, idan ba haka ba wace kawace zata zo ta kwana a gidan ta fita a irin wannan time da da sasafe kamar an koreta? Kamin bata taba fada masa kawarta ta zo ko zata zo ba, and shi da idonsa Namiji ya gani a motar ba mace ce, duk kudin da yake kashe mata yana yi ne saboda ta tsare masa mutunta ta hana kowa kanta sai shi, a tunaninsa matan hausawa su da rikon amana kamar na kafirai wannan ya saka be taba gwada yi da ba haushiya ba, sai ita da yake bata ko wane kalar umarni ta bi ciki har da aske gashin kanta da tayi saboda shi, domin tsabtarsa bata tsaya iya ga tufafi ba har da gashi baya so more Especially na wasu matan da yake ganin attachment ne ba ainahin na su ba. Rasa gurin zuwa ya saka shi zuwa gurinsa ba a time da ya saba zuwa ba, ba dan ya saba lati ba, sam baya lati a zuwa aiki kuma no matter how yana shiga office yayi duk abun da yake aikinsa ne, sai dai ya wulakanta mutane yadda yake so ko ya kori wasu, wannan halinsa ne da kowa ya sani. Shiyasa suke taka tsantsan da bin dokokisa gudun kar ya jefa su a matsala yayi musu sallamar dole. Ba halinsa bane yin Sallama balle kuma amsa gaisuwa, hakan ya saka be kula masu aikin tsabtacen muhallin dake ta gaisheshi ba, har ya isa gurin kofarsa Office dinsa ya saka code bude kofar ta bude masa ya shiga ciki ya zauna, nan kadai gurin da be yi marmarin zuwa ba, musamman a yanzu da ya shigo cikin damuwa. kujerarsa ya nufa ya zauna ya runtse ido kujerar ta fara juyawa da shi tana tunanin yadda abubuwa suke masa zafi a yan kwanakin nan. Zaman baya masa dadi haka ya saka shi mikewa tsaye ya nufi fridge ya dauko gorar ruwa ya kai bakinsa, sai da ya sha rabinta sannan ya aje saman fridge din ya nufi Window ya bude fararen Curtains din da suke gurin ya tsaya gaban glass din yana hango kasan begen da mutanen dake kokarin shigowa masu aikin gyara harabar kuma na ta yi. Hannunsa daya ya saka aljihu sannan ya juyo ya nufi gurin Telephone din dake gefen teburinsa kira yayi sannan ya kara a kunne. Idan Faruk ya zo ina nemansa Shine abun da ya fada ya aje telephone din, ya sake zaunawa wannan karon kofar shigowar yake kallon. Faruk be shigo office din ba sai takwas da rabi, ciki tsoro da fargaba ya shigo sanin waye Ameer zai iya cewa ya masa laifi, domin tun kamin ya shigo office dina ka fada masa Ameer na nemansa kuma shigowar safiya yayi. Da katinsa yayi amfani ya bude kofar sannan ya shigo Office din dake dauke da kyamarorin tsaro, kamar yadda ko wane Office yake. Da ido Ameer ya fara tsare shi sannan ya mike tsaye ya dauki pen din dake gurin ya yagi diary ya rubuta masa numbers dinsa duka biyu ya mika masa, da kamar tsoro Faruk din ya karasa ya karba. Ka karbi kudi gurin Cashier ka yi welcome back din layukan Okay Sir Amsa da sauri yana jin sanyi sanyi a ransa ya juya da sauri ya fice, fridge Ameer ya sake budewa ya dauki gorar ruwa ya fice daga office. MALEEK POV. Sun samu Abiey a Station din yana jiran isowarsu, da gangan ya bari aka kama Nimra saboda ta san ransa ya bace kuma ta kiyaye sake aikata irin kuskure a gaba, ta wani bangaren kuma yana ganin kamar bata da laifi domin gani yake Ummi ce ta shirya mata haka saboda ta samawa Ameer mafita. Office din CP din aka shiga da su, yadda aka kawata dakin ba dan tarin hotuna da awards da kuma littafai da suke gurin ba sai ka rabtse ba Office ba ne, sanyin Ac ta ko'ina ga wani madaidaicin tv da aka saka a gafe bayan na'urar sanyaya ruwan sanyi da zafi a suke gefe daya. Kusan kamar hira Maleek ya samu mahaifinsa na yi da CP din da suke ganinsa kamar dan'uwan Abiey saboda shakuwa da suka yi tun kamin a kawo shi Abuja a matsayin CP sun san juna shi da Abiey. Nimra ta kasa kallon inda mahaifinta yake ma balle ta karasa ta zauna a inda CP yake nuna mata. Ka kyaleta a nan ai duk ita ta jawa mutane matsala CP yayi murmushi yana kallon yarinyar da zai iya kiranta da yarsa daman bata wuce sa'ar yarsa ba. Yaran ne sai hakuri, kullum cikin janyo magana suke, zauna... Wannan... Nimra tambaya zan miki Ta zauna daker har lokacin kuka take marar sauti, kamin CP ya fara magana Abiey ya kalli Maleek ya ce. Ummi ce ta maka umarnin amsa cewar kai ka karbi motarta? Maleek ya girgiza kai. Aa saboda ni din ne dai Abiey ya kalli CP daman tun kan a iso da su aka fada ma CP abun da Maleek yayi shi kuma ya fadawa Mahaifinsa. Shashanci ne, ba shi ya aikata abun nan, kawai yana kokarin kare yar'uwarsa ne, Maleek ba shi da matsalar shiga sha'anin da babu ruwansa ko kuma janyo magana, ita ma kuma yanzu ne ta zama haka da can ba haka take ba From A to Z Nimra ta bada labarin abun da ya faru ciki har da haduwarsu, da adadin kudin data ba shi da kuma Alert din da ta gani na kudin da aka cire. CP ya girgiza kai Abiey kuma ya tabe baki. This is serious issues to shi yaron yana ina yanzu Ban san inda yake ba Wallahi Ta amsa tana kuka, sai ya mika mata takardar da biro. Rubuta mana number da kika ba shi a nan zamu binciko inda yake, idan kuma kin san inda zamu ganshi ki fada mana Idan ma an fada muku ai ba kamashi zaka yi CP sai dai ka bugawa Mahaifinsa ka fada masa ya boye dansa Cewar Abiey CP ya kyalkyale da dariya. Alhaji Aliyu kenan, to ai rayuwar duk haka take tafiya dole kowa ya ci Alfarmar, kasan shi arziki ba karyar ba ne ko da baka mutuncin da mutum balle kuma ana yi, kai ma yanzu da aka turo min case din nan Abuja da bayanin yarka ai kiranka na yi a waya na fada maka, kuma da baka aminta ba da Police ba su shiga sun kamata ba, so abun ya zama na gida ne gaba daya, sa'arku daya daga kai har shi Mr Bashir din yarinyar bata mutu ba, kuma babu wani abu da aka gani a tare da ita idan ba cizon maciji ba kuma Alhamdulillah tana asibitin a yanzu haka karkashin kulawar likitoci Abiey ya sauke ajiyar zuciya. Ina ya dauko yarinyar kuma? To wannan kuma shi kadai zai iya amsa mana, amman dai yarinyar wata kala ce tun daga yanayin hoton da na nuna maka idan ka kalleta zaka ga yadda tufafin jikinta ma suka banbanta da mu Ka kira mahaifinsa ka fada masa abun da ansa ya sake aikatawa Kana hanyar zuwa na kira wayarsa ban samu ba, amman anjima zan sake gwadawa ko kuma na aika masa da sako Abiey ya mike tsaye sannan ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudin aljihunsa mai dan dama ya dora saman teburin CP. Zan tafi da ita gida idan ya dawo ya fadi inda ya dauko yarinyar zan dawo CP ma tsaye yayi da katon cikinsa. Kwana biyu kana ta zirya CID kuma be kamata ana ganinka a nan ba, indai ba abun ya fi karfin yadda nake tunani ba, to ba sai ka dawo ba zan iya rufe case din na san shi ma Mr Bashir haka zai bukata, kuma hakan zai fi tun da abun ya zama duk gida ne, idan ya fada mana inda yarinyar take zamu maida ita gurin iyayenta then case closed Abiey ya
Chapter 28 · 0% Book details