Sashe 95
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba zai siye kudi ba, da na ce kudi matar nan ta baka har ka sauya nan take, wata kila ta siye ka da kalamai ne Dariya sosai Daddy yayi. Sai kuma gashi kudi baya siyen kudin, ashe wannan ya isa ya fahimtar da kai cewar tunani ne irin na babban mutum mai shekarun da ya isa ya haifeka, kalamai sun yi kadan su siye zuciyata Ameer, ni dai ina da saukin kai da saurin sauka idan na yi fushi ina bude zuciyata na fahimci ciwon wani ba ciwona ni kadai ba, zuwan Mahaifiyarka a gidan nan, ya fahimtar da wasu abubuwan da ada ban fahimta ba, akwai labarai masu matukar tausayi da sosa zuciya a bayan shafin faruwar komai, wata kila da bata ba ni kai ba, da yanzu ban san dadin zama uba ba, ban san zafin rabuwa da kai ba. Ameer bari na fada maka wani abu da ban taba fada maka ba, Mahaifiyarka ta taba ceton rayuwata a lokacin da babu kowa a kusa da ni, da ace bata ceto ni a lokacin ba, da yanzu duk wannan rayuwar ba mu yi ta ba, tana da tsohon cikinka ta gudu daga garin Kano ta tafi wani kauye da yake zaria saboda ta boye cikinka ta haihu a can so that idan ta haihu ba zata bawa Jamila kai ba, baka yi tunanin kauna ta saka ta yin haka ba irin ta uwa da a? Zan tafi gurin wani business trip jirgina ya fadi a cikin wani daji da ban san kowa ba, karfen jirgin ya danne ni, mahaifiyarka ita ta taimaka ta fito da ni, ni kadai na tsira a cikin jirgin nan da bata taimaka min ba da ni ma ban rayu ba (Masu makaratu kun tuna lokacin da Zahra ta ceto Mr Bashir a cikin littafin farko CIWON SO?) a lokacin ban samu taimakonta ba saboda ta bar garin tana zubar jini aka kaita asibiti jinina aka saka mata, sai dai tsoron kar ta rasaka ya saka ta sake guduwa daga nan ban san a inda ta koma ba, kudin na na bada a bata ma bata karba ba, ka ga dace kudi ne a gabanta, babu abun da zai hana ta tsaya ta karbi kudin, ban sake ganinta ba sai da Jamila ta aikata abun da ta aikata, sai ya zama nonon Jamila da madara da duk wani nono a duniyar nan baya baka lafiya a ciki, sai nonon Zahra, a dole ta gidan da zama saboda ta samu kusanci da kai Ameer ya aje spoon din ya kalli Daddy. Daddy abinci ka ce na zo mu ci ba hirar wata ba please Baka yarda da ni ba kenan? You can google it ai tarihi baya boyuwa zaka ga lokacin da hadarin ya faru, Ameer ba ina fada maka wannan ba ne kawai saboda ka sauko daga tudun daka hau, no ina fada gaskiya ne da kuma abun da na fahimta. Da zaka bawa mahaifiyarka dama ka tambaye ta wasu abubuwa wata kila da baka sake yin fushi da ita ba, ni dai na san baka dukan abun da zan iya domin samun farincikinka, shin baka tunanin lokaci yayi da ya kamata ka rama min abun da na yi maka? Ka saka ni cikin farincikin nima? Kai ai kana da sauran lokaci, amman ni na sha ruwa shekaru sun ja, ga kuma ciwo yana yawan kawo ziyara, kar sai bayan bana raye ka ce zaka nuna min kauna, lokacin nan is too late komai ya kare Ido Ameer ya kura masa yana kallonsa shi ma kallonsa yake da damuwa a fuskarsa. Ba wani abun nake son daga gareka ba, ni dai ina son ganin farinciki a fuskarka, ina son na ga kun shirya da mahaifiyarka, ina son na ga ka sadu da dangin mahaifinka da na mahaifiyarka a lokacin da nake raye da idona, domin mutuwa zata iya zuwa min anjima ko yanzu Me da me ta fada maka lokacin da ta zo gidan nan? Bata fada min komai ba, but i see the pain in her face, i read it in her eyes, i hear it in her voice, ta rasa yarta three days ago Ameer, but she still care for you, bayan kuma you're the reason behind her daughter's death, idan ba uwa ba wace mace ce zata so ka? Bayan mutuwar yarta? Kasan wani abun da ya ba ni mamaki? Zuwa ganinka da ta yi, babu wanda ya fada mata kana ciwo, sai alakar dake tsakanin uwa da a ita ta sanar mata. Ban ce dole ka yafe mata ba, ban ce dole ka sota ba, amman ina son na roki wannan amfanar a gurinka, dan Allah ka saurareta a duk lokacin da zata zo maka da wani uzuri ko da na magana ne, sannan ba ita kadai ba, Ameer na dade ina fada maka ka bude zuciyarka ka rika damuwa da damuwar wasu, idan wani ya shiga matsala ka rika jin kamar kai ne a ciki, wannan shi ne imani da soyayya ta musulunci. Daga karshe ina son na fada maka, iyaye komai suka aikata mana basa yin laifi, kashe ka kawai za su yi su yi laifi a gurin Allah, bayan Allah da Annabinsa, babu na biyu sai iyaye, da ace na wulakanta iyayena da ban samu kaina a halin da nake ciki a yanzu ba, da rayuwata bata yi albarka kamar haka ba, ni dai kam ina matukar alfaharin da iyaye, ko da kuwa za su siyar da ni a kangin bauta... Daddy na kaiwa nan ya mike tsaye yaja kujera baya, ya zagayo ta inda Ameer yake zaune ya dafa shi. Shin baka marmarin sanin waye mahaifinka? Su waye yan'uwan mahaifinka? Miye mahaifinka ya yi kamin ya rasu? Miye ma silar mutuwarsa? Baka son saduwa da yan'uwa da danginsa? This is right time da zaka kyautatawa iyayenka ka samu aljannarka cikin sauki, duk wanda zai fada maka wani abu bayan wannan ba masoyinka ba ne, ai yanzu ne lokacin da ya kamata ka yi hanzarin kwace muhallin duka yayan da Zahra take da su a zuciyarta, kai da ka zama an gata mai gida biyu iyaye hudu? Baya fika Ameer? Ka ci abinci lafiya... Daddy ya karasa yana bubbuga kafadarsa tare da murmushi sannan ya fice daga dinning din. Ameer ya juya yana kallon mahaifinsa sai kuma ya juyo ya kurawa abincin da yake ci ido, kalaman Daddy nata masa yawo a madafar tunanin da nazari, har ya fara tace su yana sakawa a babin lura. Kasa cin abincin yayi tun bayan four spoon da yayi a dazun duk kuwa da irin dadin da abincin yayi da kuma kasancewarsa favorite food dinsa. Tashi yayi ya fito daga bangaren Daddy ya fito waje ya tsaya yana kallon yadda Allah ya kawata saman da tausarari masu kyau da gaske. Ya dauki tsawon lokaci a gurin sannan ya shiga parlour ya zauna for few minutes, ya tashi ya shiga dakinsa. Miss calls ya tarar kusan 9 daga number Ummi, daman kai ko da ta kira wayar na hannunsa ba zai yi picking ba balle kuma har yayi calling back. Shi be ga reason din da zai saka ta dame shi a yanzu ba, bayan ta kasa bashi kulawa a lokacin da ya fi bukata. Daddy was right idan zai bukaci wani abu a yanzu to tahirin mahaifinsa ne, not her or her family, ba zai son jin haka daga bakinta ba sai dai abu ya zame masa cilas shi ne tambayarta a ina yan'uwan mahaifinsa suke, a gurinsu yake son samun labarin komai ba a bakinta ba. Yana kokarin jifa da wayar akan gado wani kiran ya sake shigowa a take ya danna rejected. Kamin ya aje wayar sako ya shigo masa. Waira ce take son magana da kai, ta takura tana son ta tambaye ka wani abu Ya karanta sakon, kamin yayi decided zai dauka ko ba zai dauka ba, kiran ya sake shigowa, sai da ta kusa yankewa sannan ya daga ya saka wayar a hands-free, kuma yaki yayi magana har sai da Waira ta fara magana. Allo Ammir A dayan bangaren sai Ummi ta matso kusa ta karbi wayar ta saka hands-free saboda ta ji muryar anta. Ya aka yi? Ina ta kira baka daga ba Yanzu na daga ai Baka son magana da ni? Me yasa na daga wayar to? Gashi nan kana bata fuska Ta fada ba dan ta ganshi ba, sai dan ta karanci hakan a muryarsa da yadda yake amsa mata. Ya nufi boutique dinsa ya tsaya gaban madubi yana kallon kansa, da gaske fuskarsa a hade take. Zan aje waya sai ka yi far'a sai na sake kira Ta fada. Jin haka sai ya saka ya sassauta fuskar yayi ya sauke numfashi. Wayar tana kusa da ke ko? Ita tace na ki fada min haka? Ummi ta yi saurin girgiza ma Waira kai. Aa Ummi tana dakinta Ni na sauko ina falo Ya jimmm for some seconds sannan ya ce. Me mike son ki tambaye ni? Abubuwa da yawa, na ce Ya Maleek ya kawo ni, sai yayi min ihu wai ba za a sake zuwa ba, kuma idan na sake yin maganarka ma sai ya min duka Saboda shi ubanki ne? Aa shi Ya Maleek ne Baki da alaka da shi ai, ba shi da hujja Shi yaron Ummi ne ai Baki da alaka da Ummi baki da alaka da kowa a gidan nan, so babu wanda zai saka ki dole ko hana ki abun da kike so, idan ma akwai wannan to ni ne, domin ni na dauko ki daga daji, ni ne sikar zuwanki garin nan and that stupid house, remember? Ta kalli Ummi sannan ta daga masa kai. Good so no one has power over you, tambaye ni abun da kike son ki sani Ummi ta yi saurin rada mata a kunne. Zaka zo sai na tambaye ka? Please Abubuwa da yawa ne, ina son na sani zaka zo saboda ni? Baka damuwa da matsalar kowa kai? Yayi shiru, ya saka hannunsa ya taba hancinsa ya runtse ido ya bude. Dole sai na zo wai? Zaki iya tambayata a waya Bana so a waya, kai baka da tausayi Ameer ko? Shiyasa ka tafi ka bar ni a