Sashe 127
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
saboda ke ba, domin ba zan jure ganinki da wani ba, Waira ina kashinki Kishi? Me yasa Sulem ba ya kishina ko Ya Maleek ko Mahmood sai kai? Saboda sonki nake yi, i love you Waira with all my heart Su ma suna sona ai Ba irin wannan son nake miki ba, nawa yana da banbanci da na su Irin son da kake yi ma Ya Nimra? Gabansa ya harba da karfi a lokacin da ta ambato Nimra kuma ta kwatanta da kanta. Ya kama hannunta ya rike. No Waira ina son ki ne tsakani da Allah irin son da zamu gina wata kalar duniya mai dadi mu rayu a cikinta, so na aure wanda zamu kafa zuri'a mu yi yaya kamar Ummi Ta janye hannunta tana girgiza kai. Ba irin wannan ba dai, ni bana yi ma kowa irin wannan soyayyar Amman kina so na ai Ina sonka ina son Maleek ina son Sulem ina son Mahmood ina son Jabir ina son Nimra ina son Ummi ina son duk wani mai kyautata min Ya hade yawu da karfi tana ta tunanin ta inda zai iya sarrafa halshensa ya karkato da tunaninta ta fahimci inda ya dosa. Ta mike tsaye tana jan kujera baya sai shi ma ya mike da sauri Waira dan Allah karki kalli abun da ya faru Nimra ki saka shi a ranki, kuskure wanda kowa yana iya yi haka ne? Amman kai ka shirya komai ai, kuma saboda kai Ummi ta mari Ya Maleek, ta yi fada da shi hakan yayi min ciwo duk saboda ni Waira please understand me ina sonki tun a lokacin da na fara ganinki a school bus Ba lokacin da ka fara ganina a daji ba? Kamar wanda ya firgita haka yake kallonta, sai kuma ya daga mata kai. Yeah tun a dajin Ba auren yarenmu, balle kuma ni ko cewa aka yi ana so na mutuwa ake, kuma ba ma auren wanda ba kabilar mu ba Ya matsa daga jikin kujerar ya rumgumeta. Waira ina sonki a haka zan iya aurenki ko da zan mutu ne, i love ban taba son wata mace ba sai ke, ba ki san yadda nake ji a zuciyata ba please ki daina min haka Ta fara kokarin raba jikinta da shi. Ya Maleek ya fada min Addinin musulunci ya hana taba jikin mace da bata ka ba, amman kai kana yi shi kuma ko hannuna baya rikewa saboda yana da tsananin biyayya da taka tsantsan ga addininsa Ya sake ta a dolensa yana kallonta idonsa cike da tsoro kamar yaro da ubangidansa. Amman ke ai wannan hukuncin be hau kanki ba, har sai kin musulunta Amman ai kai ka sani, kuma zaka samu zunubin haka ne? Ya daga mata kai kamar wani soko. Ameer kai ba mutumen kirki ba ne, mai cutar da wata har sai da ta rasa rayuwarta, mai fada da mahaifiyarsa, mai barin wata a daji har sai da ta kusa rasa rayuwarta, mai fada da dan'uwansa, mai aikata abun da addininsa ya hana, ni bana sonka, ni ba irin Ya Nimra ba ce, ba zaka min irin abun da ka yi mata ba Ta juya ta sauka daga dinning din, shi ma ya juyo yana kallonta jiki a mace kamar wanda aka zarewa kuzari. Hanne da bakuwarta suna satar kallonsa domin suna iya juyo wani abun da Waira take fada. Dakin Ummi ya nufa da tunani kala kala a ransa da kuma rudani na yadda Waira ta canja masa lokaci daya. Kamar wanda be san abun da yake ba haka ya tura kofar dakinta ya shiga idonsa cike da rauni, fuskarsa na bayyana karayarsa. Sai da ya isa gaf da gadon Ummi sannan ya tuna be yi sallama ba. Salamu alaikum Wa'alaikussalam Ummi ta amsa tana kallon cike da kulawa. Maleek dake tsaye jikin Mirror ya kalleshi sannan ya mike tsaye daidai da zimmar ficewa daga dakin, saboda shigowar da Ameer yayi. Maleek... Ya tsaya cak sakamakon kiransa da Ameer yayi, ya juyo ya kalli Ameer din dake kallon kasa cikin wani yanayi mai wuyar fassara. I know bana so na ko son wani abu nawa, na san ba zaka taba son abun da nake so ba, kuma ba zaka so na samu farinciki ba Ameer ya dago ya kalli Maleek. But Waira is different ita rayuwa ta ce, ina sonta irin son da kalamai sun yi kadan su bayyana alkali yayi kadan ya rubutu, ka bata a gurin kowa ka saka kowa ya tsane ne amman ban da Waira, kokarin bata alakarmu da nuna mata ni ba mutumen kirki ba ne, dan Allah ka bari, idan baka son zama a gidan nan zan iya tafiya na bar gidan, zan iya kaucewa duk wata hanya da zaka gan ni, amman please ka bar alaka ta da Waira, na san kana min kallon mutumen banza ko kuma makiyinka saboda abubuwa da suka faru, amman Waira da gaske nake, kai kasan idan ina son abu bana bashi baya, kuma idan na sakawa abu gaba ba zan saurara ba na maka magana ne saboda ina son abu ya samu ta masalaha. Kana da Abiey a raye, ka rayu da Ummi tun tashinka har yanzu baka rasa komai ba, so please ka bar min wannan ni na na samu farinciki, domin a yanzu farincikina yana tare da Waira... Yana gama fadar haka ya mike tsaye ya fice daga dakin ba tare da ya ce da Ummi komai ba. Ummi ta bishi da kallo kamin ta kalli Maleek dake tsaye. Me ka yi? Yaushe zaku fara son junanku Maleek? Akan me zaku raba hankalinku kirkiri kiyayya saboda Mace? Ba kasan zaka iya rasa Waira ka samu wata ba, amman ba zaka rasa dan'uwa ka sake samun wani ba, kar soyayya ko kiyayya ta rufe maka ido ka nemi cin amanar dan'uwanka, na san kana son Waira amman kokarin bata dan'uwanka a gurinta ba abu ne mai kyau ba Yana son yayi magana zuciyarsa na raya masa ko da ya bude baki yayi magana Ummi ba zata fahimce shi ba. Saboda haka yayi shiru ya kuma tsaya a gurin ya kasa tafiya. Baka tashi nuna kana sonta ba, sai a lokacin da shi ma ya ce yana sonta? Kuma ba za ku iya bari ta zaba a tsakanin kai da ita ba, sai ka soke dan'uwanka a gurinta Ni ban soke shi a gurinta ba, ba zan hana ya sota ba, ba kuma za hana ita ma ta so shi ba, amman ba zan bari ya fitar da ita a gidan nan ba, bayan duk abun da yayi mata a baya Yayi mata ko kuma yayi ma Nimra? Ina zaton saboda haka ne kake rike da shi a ranka, idan har wani zai rike wani da laifi ba za a zauna lafiya ba, kai ka manta irin abubuwan da ka yi min kuma ka yi ma kanenka, ka manta yadda kake nuna min kiyayya, ba dama na yi magana da kai ko na zauna a kusa da kai? Yayi shiru yana jin wani iri Da ace ban yafe maka na manta ba, kana tunanin zan zauna da kai kamar haka? Kowa yana laifi Maleek kamar yadda ni ma na yi, amman aka daga kafa, domin Allah ma yana yafe mana idan muka yi kuskure Ya sauke kansa kasa tare da ajiyar zuciya sannan ya yi walking out slowly kamar mai abun kunya. Yana janyo kofar dakin ya rufe Waira ta iso gurin tana rike da hannayenta idonta yayi ja sosai alamar ta yi kuka, suna hada ya sauke idonsa daga barin kallonta ya sauka kasa, binsa ta yi da kallo har sai da ya kusa sauka sannan ta kira sunansa. Ya Maleek Ya tsaya sai dai be juyo ba, ta kawa ta yi ta sauka kasa ta tsaya gabansa. Zaka kai ni gida Please Ya kasa ce mata komai kuma ya kasa dauke idonsa daga barin kallonta. Ina son na tafi gida ne, zan gane hanya yanzu Be ce mata komai ba ya dauke kai ya sauka kasa ta bishi da kallo kamar ta san zai waigo ya kalleta, kallonta sosai irin na tausayi tunaninsa na bashi cewar saboda shi ne zata bar gidan. Yana kokarin juyawa ya cigaba da tafiyarsa idonta ya fara zubar da ruwan jini, ba tare da ta sani ba, da sauri ta hauro yana kallonta. Idonki Waira jini Ta kai hannu ta taba hawayen da suka zubo mata ta duba sai ta ga jini. Wani abun zai faru, wani abu marar dadi Kamar ya? A duk lokacin da na ga hawayen jini a idona to wani abu ne zai faru, wanda ba zai min dadi ba Ya kalli kofar dakin Ummi sai kuma ya kalli downstairs, baya son Ameer ko Ummi su ganshi tare da Waira, Ummi zata yi zaton yana fada mata abun da ya faru ne, Ameer kuma zai yi irin wannan zaton. Waira zaki shigo dakina mu yi magana Ina son na yi magana da Ummi ina son na fada mata cewar zan tafi gida Akan haka zamu magana please come Ya wuce gaba sai ta bishi a baya, rike mata kofar dakin yayi har sai ta shigo ciki sannan ya rufe yana kallon saman gadonsa da take kallo. Ya Maleek kana da aure? Ya girgiza kai. Ban taba tunanin yin aure ba, balle na yi me yasa kike tambaya? Idan ina da aure ai da kin sani tun farkon zuwanki gidan nan Ni ma abun ya ba ni mamaki, domin ban taba ganinta a downstairs tare da mu ba, amman ina ganinta idan na shigo dakinka, kuma ka fada min addininku ya rahamta taba jikin macen da bata tashi ba, amman ni ko wane dare kana zuwa min kana taba ni ko kuma kana zaton ban fahimta ba ne? Ya juya ya kalli gadon ya kalli Waira Wace mace dai tukuna? Sai a lokacin ta kalleshi, tun da take maganar matar dake kwance saman gadon kawai take kallo. Gata can Ta nuna saman gadon har lokacin jini zuba yake a idonta. Maleek ya juya cike da tsoro ya sake kallon gadon shi kam be ga komai akai ba, amman ita har lokacin saman gadonta take nunawa. A lokacin da na taba suma ma ita na gani, gata