Sashe 30
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
ki karba sai ya aje a saman gadon ya kai hannunsa jikin fuskarta ya share mata hawayen da suka zubo mata, nasa idon na cika da kwalla, da sauri ta kai hannunta zata dafa shi sai yayi saurin dauke hannun kamar ya san abun da take nufin aikatawa. Ba tare da yayi magana ba ya fice daga gurin Nurses din dake tsaye sai mamaki suke, ganin be fadi komai ba be kuma dubata yadda ya dace ba yayi tafiyarsa. Ganin ta ki magana sai kuka take ya saka suka tunanin bata iya magana, tunanin bata jin yarensu be zo musu a rai ba, domin wasu ma sun dora mata hauka ganin tufafin dake jikinta ga kuma tarin dattin daya boye ainahin kyaunta. Tun suna mata magana cikin dadi rai har suka gaji suka tafi suka kyaleta, daman irin Asibitin nan ce ta Gobnati ta marasa galihu da ba a ciki kula da mutum kamar babbar Asibiti ba, ko kuma Private Hospital, bata kallon ko'ina a yanzu sai kasa Tile din dake kasa take son tantance minene a gurin da yake sanyi dazun data taka, komai ya zame mata kamar mafarki, wacan rayuwar ta garinsu take jin tana marmari sai dai babu halin komawa a yanzu. Jin yan hanjinta na kukan sanar mata neman agajiya ya saka ta dauki Apple din da ya aje a gurin ta kai bakinta ta gutsura ta ci, tsoro baya bari ta tauna yadda ya kamata idan ta saka shi a bakinta ta raba shi biyu ko uku sai ta hade, da haka har ta cinye, sauka ta yi a hankali sai ta sake jin irin sanyi dazun hakan ya saka ta komawa saman gadon ba shiri, sai ta takure kanta ta fashe da kuka. Hankalinta be kara tashi ba sai da ta ga shigowar wasu mutanen na dabam ba na dazun ba, ba kuma wadanda ta taba gani ba, wadannan sanye suke da bakin kaya gaba daya jikinsu. A nan ta gane kowa ya banbanta, sai dai bata iya gane akida ko al'adar kowa balle ta iya fahimtar ko tufafin jikinsu suna walkiltarsu ne, wadanda suka zo yanzu kuma saka ta suka yi gaba da tambayoyi kala kala, suna rike da abun abun rubutunsu, kamin Likitoci uku su sake ziyarta ciki har da wanda ya zo dazun be mata magana ba, sai gashi shi ma yana mata tambayoyin da bata fahimcin yaren ba balle ta bada amsa. Ruwa a gorar dayan dan sanda dake sanye da bakin tufafi ya mika mata tare da abincin a takeway, ta sani tana bukatar ruwa sai dai tsoronsu da rashin sanin waye su mutanen ya saka ta kasa mika hannu ta karba, Apple din da likitan ya aje mata dazun ma bata taba ba, cikinsu kuma babu wanda ya damu ya tambaya waya bata apple din. A kokarinsa na burgeta ya bude abincin dake cikin robar takeaway, dafadukar shimkafa ce da cinyar kaza. Sam bata gane cewa shimkafa ce ba domin am sarrafa ta ba a babin da ta sani ko ta taba gani ba. Hawaye ke mata zuba kamar an bude karamin fonfo tsoron take gashi ta rasa gane yaren da suke magana da ita, ga mutanen sun kashi har kashi kashi kowa tufafinsa dabam, wani abun da ya bata tsoro kuma yadda suka tsareta wasu na kallonta wasu na damunta da magana wasu na rubutu, hankalinta be kara tashi ba sai da dayan likitan ya miko hannnunsa ya riko hannunta. Ahir hir Ahir verrr yat tour tour tor Ta fada da karfi ta fisge hannunta daga rikon da yayi mata, likitan nan ne dai na dazun da ya bata Apple, duk kirko kirko suka yi suna kallonta ba da farko kallon kurma suke mata ganin taki magana, a yanzu kuma da ta yi magana ta ba su mamaki, domin wani sabon yare suke ji a tare da ita. Kamar Fulatanci take Dr Shuraim Wanda aka kira da Dr ya juyo ya kalli dan'uwansa da mamaki. Ba fulatanci ne ba, fulatanci yarena ne da shi take yi da na ji Kasan ance fulatancin ko wane gari ya banbanta da sauran Yes, kalmomin suka banbanta amman muna gane yaren juna wannan ba fulatancin ba ne, wani yaren ne na dabam Ya sake juyawa ya kalleta da manyan idonsa masu matukar daukar hankali, cikin kwayar idonta yake kallo. Anene fulfulde? Ta rumgume kanta tana kara matsawa baya. Be sake ce mata komai ba sai ya dauki abincin ya matsar mata da shi hannu ta saka ta buge abincin ya zube kasa ta dauki Apple din kadai ta rike. Waya bata Apple Ya tambaya yana kallon Nurses din dake bayansa, suma kallon mamaki suke masa domin sun san shi ya bata apple din da kansa. Dazun kai ka bata da kanka With confused ya kalli wacce tayi maganar, baya son musu surutu ma bangarensa ba ne balle kuma musu, hakan ya saka be damu ya musa musu ba, all what he thought is wani likitan ne ya bata suka yi zaton shi ne. Matsawa yayi kusa da ita sai ta matsa baya kamar zata shige jikin ginin tana masa kallon tsoro, hannunsa ya kai ya rika kanta yana kokarin duba idonta dake kama da nashi tsabar farin idon, sai dai nata gwaiduwar ciki blue ce tsabanin tashi da take baka wulik, kallo daya zaka mata ka fahimcin kyaunta ya banbanta da na sauran mata sa'aninta duk kuwa da kasancewar dattin dake jikinta. Tana da masifar kyau ga kirjinta a cike daidai har ya fi na sa'arta domin rigar sa in dake jikinta ta fata tana fito da ainahin zatin kyaunta ne. Be ankaro ba ta dantsara masa cizo a hannu da mugun karfi, abun ka da wanda ya dade be ci nama ba hausawa suka ce masa maye wai idan yayi cizo ba a warkewa da wuri, idan kuma yayi magana sai ta kama Mutun lol, tana dota hakoranta a hannunsa kamar reza haka hakoran suka yaga rigar hannunsa suka shiga har cikin naman hannunsa sai wani zafi yaji kamar an yanke shi da wuka a take jini ya fito sai dai ba mai yawa ba, cikin zafin nama ya fisge hannunsa yana zaro ido Easy Girl... Da sauri Police din da suka zo daukar report dinta suka jo kanta da gudu suka riketa dayan ya juyarda hannunta da karfi zan lankwasa sai Likitan yayi saurin dakatar da shi ganin yana kokarin yi mata illa kamar ya samu katon namiji. Nonono she's just a girl karka ji mata mana Ai kara ayi mata haka, what is akwai dafi a bakinta fa? Ba mu san waye ita ba Ya fada yana kara matseta. Saketa dan Allah ta tsorata ne tana zaton zan mata wani abun ne Ya saketa kamar yadda Dr Shuraim ya bukata, sai ta rumgume hannayen nata m har da mai ciwon. Dr Shuraim ya fice gurin rike da hannunsa har lokacin ciwo yake ji a sosai, kamin ya karasa Office dinsu na Likito ya cire safar hannun ya jafa a gurin da aka tana da domin zuba shara, bathroom 2(8 ya fara shiga ya wanke hannunsa sannan ya fito ya dauki audiga ya saka a gurin ya goge, sannan ya cire labcoat din dake jikinsa ya aje ya ciro wayarsa dake ringing ganin mai kiran ya saka shi murmushi. Hey Baby Girl Ruhul Kal ya kake ya aiki? Ina lafiya fatar ke ma haka kike? Nima haka, ya Katsina Katsina na nan sai zafin kamar za a kama da wuta Mu kuwa ruwa ake mana yanzu, wani guri na samu na fake ma Daman ku yan Abuja kun fi kowa zama yan gayu, fatar dai ruwan be taba min ke ba Ya jika ni kadan Da ace zan ga ruwan an kuwa da na masa duka Ta kyalkyale da dariya, shi kuma yayi murmushin da ya bayyana fararen hakoransa da suka haska bakar fatar jikinsa mai kyau da sheki. Take care of yourself zan kiraki idan na bar gurin aiki Toh I love you I love more and more and more Baby girl Ya sauke wayar, sannan ya fice daga gurin, dakin da ake aje majiyanta ya sake komawa sai ya samu har lokacin suna nan tsaye akan yarinyar yanzu ma har an samu karin wasu mutane dake kallonta a cikin masu jinya. Wannan ai zaku tsoratata ne, please kowa ya koma gurinsa Kowa ya wuce ban da police din da suke zon tirsasa ta tayi magana. Ba zata iya magana a yanzu ba, a yadda na fahimta ko tayi magana ba zai amfanar ku komai ba, domin ba ta jin yarenku inda ba ta yi hakan da gangan ba, kai kana duba jikinta da yanayin tufafinta kasan ba ta jin yarenmu Amman Doctor zai dauke ta lokaci kamin ta warke? Eh ya danganta da kalar majicin daya cije ta, zata iya sati ko sama da haka a ka'ida dai ana son ta samu kulawa mai kyau na wata daya idan abun yana da karfi wata shida shi ne zata warke gaba daya Okay mun gode, dan sandanmu daya zai tsaya tare da ita saboda bada tsaro da kuma kula da ita, ni kuma zan je na sanar da halin da take ciki Da kai ya amsa masa, sannan ya mika masa hannun suka gaisa su biyu suka fice dayan ma da aka bari domin bata tsaro fita yayi saboda ganin Likitan ya zauna a saman gadon da take zaune. Kallonta Dr Shuraim yake yana son fahimtar wasu abubuwa a tattare da ita. Baby Girl... Ya kirata da irin sunan da yake kiran Babensa, domin be san sunanta balle ya kirata da shi. Ya leka kasan fuskarta sai ta boye kanta. Akwai bukatar ki tsabtace jikinki ki ci abinci a baki magani Kamar wacce ta san abun da yake fada sai ta lake kafada daga boyen da take ta fashe da kuka. Da kamar mamaki ya ke kallonta. Kina jin yarena? Nan ma ta lake kafadar. Wane yare kike ji? Nan ma ta sake yin abun da ta yi dazu, sai ya fahimci bata son yayi mata magana ne. Okay Baby Girl zan barki ki huta Ya mike tsaye sai ta dago kanta ta kai apple din hannunta a baki ta fara ci, still tana kuka kamar wata shagwababbiya.