Sashe 11
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
kuma tace bata jin marmarin wani da ta rasa ba. Baki marmarin zama da iyaye? Ta kyalkyale da dariya irin dariyar nan ta yaran da ba su gama sanin ciwon kansu ba. Mi zai saka na yi marmarinsu? Bayan ban rayu da su ba? Abun da ka taba kasancewa da shi shi kake marmari ai Zaman da kike ke kadai be taba sakawa kin ji marmarin iyaye da yan'uwa a kusa da ke ba? Ina da yan'uwa ai Su waye? Ta saka hannunta cikin gashin kanta ta ciro karamin beranta ta dora a hannu ta nuna masa. Gashi tare da zakaru, ina jindadin rayuwata ni Ya kawar da kansa. Wannan ba jindadin rayuwa ba ne, Waira kin tashi babu iyaye kin ware kanki dabam kina rayuwa tare da abubuwan da ake kebewa, a haka kuma jiran ake ki shekara ashirin a baki sarautar da idan kika haihu zaki mutu ki bar abun da kika haifa, to ina jindadin rayuwa a nan? Hannu ta saka ta raba gashin kanta biyu ta saka beran a tsakiya sannan ta mike tsaye ta doshin gurin iccen abaya, Eid na kallonta har ta haye sama tana tsinko ayabar tana jefowa kasa sai da ta gama sannan ta kwanta a saman itacen tana cin wata. Eid na ganin haka ya tashi ya karasa gurin ya daga kansa sama yana kallonta. Zo mu tafi gida Ta girgiza masa kai alamar aa, yana jin haka ya san ba yanzu zata tafi gidan ba, sai ya juya yayi tafiyarsa, tashi ta yi zaune sai da ta daina hangoshi sannan ta share hawayen da suka cika mata ido. A yau kam Eid ya saka ta marmarin da tunanin abun da bata taba ba, su waye iyayenta wace kalar kulawa za su bata duk bata sani ba, ta ware kanta daga yan'uwanta saboda ta fi jindadin rayuwarta a inda take rayuwa a yanzu. Saukowa ta yi daga kan itacen ta nufi gabar da ruwa ke gudana ta rika bi tana kallon ruwan har ta isa inda mahadarsu take, sai ta taka wani tsauni ta tsaya akai tana hango wani gari da ba ta taba sanin akwai a gurin ba, domin yawonta be tana kawo ta a nan ba, hangaga ta hangame baki tana dariya domin yanayin iskar gurin ma a dabam take. Wannan ba jindadin rayuwa ba ne, Waira kin tashi babu iyaye kin ware kanki dabam kina rayuwa tare da abubuwan da ake kebewa, a haka kuma jiran ake ki shekara ashirin a baki sarautar da idan kika haihu zaki mutu ki bar abun da kika haifa, to ina jindadin rayuwa a nan? Maganar Eid ta dawo mata, a ciki babu abun da ya fi tsorata kamar cewar zata haihu ta mutu, kamar yadda mahaifiyarta ta mutu bayan haihuwarta, a duniya babu abun da take tsoro kamar mutuwa, ta zauna a gurin ta sako kafafuwanta kasa tana kallon yadda dacin ya wadatu da ni'imar Allah da albarkarsa. AMEER POV. Ya dago yana yi ma sakatarensa wani mugun kallo irin na kaskantaccin mutane. Ga file din Ya aje masa file din akan Table cike da Ladabi. Waya baka inzinin shigo min office? With confused sakataren yake kallonsa. Na yi knocked kamin na shigo Amman ban maka izinin shigowa ba ai, ko kuma rainin wayo ne ya saka ka fara yim yadda kake so a office dina? No ba haka ba ne, wani lokacin ko an yi knocked ba zaka ce komai ba har sai idan na shigo, a yau ma na yi zaton haka din ne, amman ka yi hakuri zan kiyaye next time Wata harara ya watsa masa sannan ya dauke idonsa ya maida gurin wayarsa, a take fuskarsa ta cika da murmushi ganin kiran mahaifinsa. Daddy Ameer kana ina? Ya mike tsaye yana wani irin kamshi kamar wanda kwalbar turare ta fashe a jikinsa dark blue suit din dake jikinaa ya karbe shi sosai ya kara fito da kyaunsa. Daddy a irin wannan lokacin ai kasan ina gurin aiki, ka san ni bana wasa da aiki sai dai ace na yi ba daidai ba Ka zo gida yanzu nan ina son ganinka Ya duba tsadadden agogon hannunsa. Yanzu? Ya sauke wayar yana nazartar muryar da be saba jin fitowarsa a bakin mahaifinsa ba sai idan yana cikin wata damuwar, ko wani abun da ya gagare warwarewa. Fito yayi sai kuma ya daga kadunsa alamar ba damuwa ya nufi gurin da jacket dinsa take ya dauka tare da keys dinsa ya fice daga office din. Yana kokarin sauka second floor ya ji ance. Kai Malam... Da gangan ya ki juyowa duk kuwa da muryar mai kiran ta yi nuna da shi take kira kai tsaye, sai dai yanayin yadda ta yi kiran da yadda yake jin kansa ba zai bar shi ya juyo ba ma balle har ya amsa mata. Malam da kai ba nake magana mai blue suit Ya juyo ya kalleta jacket dinsa na rike a hannunsa, sai dai girman kai ba zai bar shi ya fara yi mata magana ba. Ganin ita ce mai bukata a gurinsa ya saka ta dawo daidai inda yake tsaye ta tsaya cike da a'a ta ce. Sannu, dan Allah office din Manager nake nema? Kallonta kawai yake izzar kudi ta hana shi tambayar dalilinta na son ganin manager, kamar ta san waye shi sai ta gyara zaman jakarta ta yan makaranta ta ce. Ina karantar Information Technology ne a nan jami'ar Abuja, to shi ne aka bawa kowa zabar inda yake son yin IT ni kuma na zabi nan saboda ya fi min kusa da gida, na yi magana da wasu suka ce na je na yi magana da manager ni kuma ban san office din ba. From head to toe ya kalleta, ba laifi shigarta bata nuna cewar ita din yar gidan manyan masu kudi ba ce, shiga ce irin ta matsakaitan masu arzikin Abuja, kuma ta masu arzikin wasu garurun da ba a karyar naira kamar Babban birnin taraiyya, sai dai wani abun da zai iya yaba a tare da ita shi ne kamshin turaren da take. Ba tare da ya ce da ita komai ba ya juya ya cigaba da tafiya. Karya fa na yi na ce yayana ya aiko ni gurin Manager shiyasa aka bar ni na shigo, dan Allah ka taimaka ka fada min Ya tsaya sai kuma ya sake juyowa ya kalleta. Ba ma bukatar irinku Ta kalli tufafinta zuwa kasanta. To na gode Ta sauko ta wuce ta fice daga gurin cikin yanayi na rashin jindadin, bata san waye shi ba, sai dai da alama yana da babban mukami shiyasa har yake korarta, samun kansa yayi tsaye yana kallonta har ta sauka daga gurin gaba daya sannan ya fito, a gurin da ya saba aje motarsa ya nufa ya bude motar ya shiga ya dora rigarsa a kan kujerar sannan yayi reverse ya fice daga kamfanin da irin tukin da ya fi kwarewa akai. A harabar entrance din falon ya faka motarsa sannan ya fito ya doshi kofar, a ka'idarsa baya taba door Bell din wai be san iya mutanen da suka tsaba ba zai iya tabawa ya kwashi cuta, wannan ya saka yafi jindadin yayi knocked ko ba komai knocked kan banbanta shi da sauran mutane a san da cewar shi ne zai shigo so that ayi saurin bude masa. Sai da ya tsaya ya cire talkaminsa ya saka na shiga falon sannan ya shiga, as usual ko'ina na falon kamshin turaren wuta yake bayan air freshener da aka saka da kuma turaren goge tile. Karamar kofar da suka saba budewa su shiga ta sada su da bangaren Mahaifinsa ya bude ya shiga dan karamin corridor dake cike da kayan kawa, karamin falon ya shiga sai ya samu Daddy a tsaye Momy na daura masa a gogo a hannu. Lafiya Daddy? Da hannu Daddy yayi masa alama da ya zauna, sannan shi ma ya zauna Momy ma ta zauna cikin yanayin damuwa. Ameer ka yi fada da wani? Ameer ya kalli mahaifinsa kamin ya kalli Momy dake maganar. Kamar ya? Police aka turo su tafi da kai Dariya yayi ya dan yamutsa fuska. Ni kuma? Ni police za su tafi da ni? Sai a wannan karon Daddy yayi magana. Calm down na yi magana da CP bana son ka je gurin nan but it seems like dole sai ka je da alama yaron da ka taba shi ma dan masu gari ne Me suke zargina da shi? Wai cin mutumci da barazana akan rasa rayuwar wani, da wa ka yi fada Ameer? Na sha gargadinka akan abun da kake tun kana yi abu yana wucewa yanzu ya kai har a turo police a gidana da sunan ana son a tafi da ana? Na so na kashe case din ba tare da kaje ba amman CP ya nuna min abun ba zai yiyu ba Ameer ina tsoron ka dauko rigimar da zata fi karfina na kasa cireka daga wata matsalar Waye yayi karata ne Daddy? Shi nake son sani Akwai yaron da ka saka yayi wani aiki a gurin da kuke shakatawa? Ameer na jin haka sai yayi murmushi abun da ya bawa mahaifinsa mamaki. Yeah akwai wanda na saka ya bawa wani abokin mu abu Kamar ya? Ka yi min bayanin komai so that na san yadda zan bullowa lamarin Daddy ya bukata. Ya taba ni ne Daddy, kuma zan koya masa hankali nan gaba kadan Me ka yi masa a yanzu? Ameer ya kalli mahaifinsa. Ba su fada maka ba? Wata kila laifin yana da girma shiyasa CP be fada min ba yace min sai na zo Babu kunya babu tsoron Allah Ameer ya fadawa mahaifinsa abun da ya aikata da kuma wanda yake da kudirin aikatawa a gaba. Daddy ya mike tsaye yana kallon ansa cike da tsoro. Ameer yaushe ka lalace har haka? Ka kullawa abokinka Sherri saboda kawai ya watsa maka yawu a fuska? Bayan kai ka fara takalarsa? Ameer ya daga kai yana kallon mahaifinsa. Daddy sai ka rika daga hankalinka akan abun da be kai ya kawo ba Ameer kana da hankali kuwa?Miye be kai ya kawo ba? Kokarin bata sunan abokinka ko kuma kallon tsabar idona ka fada min saboda ka tambayi friends dinka yarinyar ka