Sashe 105
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
hannu ya kunna motar. Ba dan'uwanki ba ne, baki da alaka da shi, Waira baki da alaka da kowa a yanzu sai ni Kai ma ba dan'uwana ba ne! A wani irin dum maganar ta fado masa a kune ta fara rawa a kirjinsa. Ya dan karkato kamar zai kalleta sai kuma ya fasa ya cigaba da tukin motar. Ni ina son Sulem, Sulem ba ya min fada Miye abun fada a cikin magana ta? Gaskiya na fada ai, waye silar zuwanki garin nan ba ni ba? Amman ai a daji ka bar ni, baka taimaka min ba lokacin da maciji ya cije ni That's was my mistakes, amman na taimake ki mana, na dauko ki saka ki a motar Nimra Baka yi ba, Sulem ne yayi? To a ina kika ga Sulem din? Ni ban sani ba, amman shi na gani a gidan Hospital kuma shi ne yake min da sauki ba kamar saura ba Shi fa likita ne kawai, amman ba shi yaje daji ya dauko ki ba, ke dai kawai kin farka kin ganki a asibiti ne, ya taimake ki ne saboda an ba shi kudi ba free yayi miki ba? Ba a bashi kudi ba Waya fada miki? Na gani ai, babu wanda ya bashi kudi, kuma da iyayensa suka masa fada sai ya dauke ni ya kai ji wani gurin muka kwana a can, be bar ni ni kadai ba, kuma da masu bakin kaya police aka ce su kawo ni a nan be min fada ba, ni ina son shi Ya daki sitiyarin motar da karfi Haba Waira ina da fushi sosai, karki saka raina ya bace mana, don't make me angry, kar na fadi wata maganar da zata saka ranki ya bace har Maleek ya yi kwatance da haka Toh ka daina min fada, gashi ka daki mota next ni zaka daka kamar Ya Maleek Ya amsa da sauri. God forbid ni ba zan taba dukanki ba, ba wannan ranar fada kuma na daina, zan siya miki sarka mai tsada sosai ki saka a wuyanki ba zobe ba, ba a saka zobe a wuya Ni Sulem ya saka min ina so Wannan Sulem din dan'iska ne Sai ta ji kamar ta fashe da kuka saboda ya zagi Sulem, ita duk mutanen da take kauna bata son a ta a su. Idan mutum yana kyautata miki shikenan ya zama masoyinki? Zan rufe idonki da kyautata har sai kin manta kowa a rayuwarki Ya saka a ransa sannan ya kalleta yana murmushin ya ce Yi hakuri, Sulem mutumen kirki ne, yanzu idan mun koma saka miki zobenki a wuya shikenan? Ta daga masa kai. Okay Smile Ta yi murmushin kadan, hakan kuma sai ya saukar masa da farinciki duk wani bacin rai da yake ya ji kamar an yaye masa shi Daddy yayi murmushi bayan ya gama sauraren hukuncin da Ameer ya yanke na zama a gidan Ummi for some days. Ka yi tunani mai kyau, kuma a yanzu na yarda ina a mai hankali da sanin ya kamata, Allah ya maka albarka Ameen Ya amsa sannan ya aje jaridar dake hannunsa ya mike tsaye. Idan dai akwai wani taimako da kake bukata zaka iya fada min Ya juyo ya kalli Daddy. Okay thank you Daddy Your Welcome Daddy ya amsa masa da murmushi sannan ya daga masa hannu. Ameer ma murmushin yayi ya juya ya fice daga dakin. Falon Mummy ya shigo ga mamakin Waira ya samu zaune a kasa ta baje gashinta Fiyya na mata kitso kamar ba ita ba, Teema zai dariyarsu take, domin Waira son kitson take a gasken gasken, Fiyya kuma yawan gashin Waira ne ke burgeta yadda ya sha gyara ya sauko har gadon bayanta. Fiyya me kike Kitso nake mata Murmushi yayi domin ya san shirme kawai za a tabka, Fiyya bata iya komai ba kawai dai tana son taba gashin ne. Ya zauna a kujerar dake fuskarta Waira ya kura mata ido ko kyabtawa babu, shi dai kam kallonta yana masa kyau matuka, ba ma kamar a yanzu da take ta far'ah kamar wani kitson arziki za'ayi mata. Is she your new girlfriend Ya dan juyo ya kalli Teema sai kuma ya juya ya kalli Waira da bata ma san ana yi ba, sai murmushi take tana taba gafen gashin da Fiyya take murdawa da sunan kitso, a rayuwarta ba a taba yi mata kitso ba, bata ma san wani abu kitso ba sai a kan su Ummi, abun ya burgeta amman bata taba sha'awar gwadawa a kanta ba, Ummi kuma bata damu da tace ayi mata ba, lura da yawan gashinta ba kowa zai iya mata kitso ba, kuma ba lallai ne ta yarda ba, domin zai iya mata zafi saboda abu ne da ba'a taba yi ba. Hakan ya saka ta maida hankali gurin gyara mata gashin kawai ba tare da kitsawa ba. Me ya saka ki tunanin budurwa ta ce Ya fada bayan ya dauke idonsa daga kallon da baya gundirarshi. Baka taba zuwa da wata mace a gidan nan ba, baka taba gabatar mana da wata ba, amman wannan kana shigowa sai ka cewa Mummy ga Waira suka gaisa, baka jira wani ya bata abinci ko abin sha ba, da kanka ka dauko mata lemu, ka nuna mata gurin da zata zauna, har kana fadar ta saki jikinta nan din ma gidansu ne Ya yi murmushi, sam be taba tunanin Teema ta lura da abun da be san ma yana yi ba. Kuma tana da kyau, da irin wayewar da nake tunanin idan mace bata yi ba, kamar ba zaka yarda ka kulata, kalli yadda ta shigo rigarta kadan ta wuce knees, bata rufe kai wata kila saboda yawan gashin kanta, ga ta fara har farinta ya fi naka kyau, idonta irin mai kyaun nan ne, bakinta da hancinta iya ita A karo na yi yayi murmushi yana kara bawa kansa abun da ya kusa zame masa dole, wato kallon Waira. Komai kin canka daidai, amman ba girlfriend dita ba ce, rashin saja mayafi kuma ya samo asali ne saboda addinita da al'adarta, ita din ba musulma ba ce Teema ta sauke wayar hannunta ya kara kallon Waira da mamaki. Ikon Allah kiristace? Ban san wane kalar addini take ba tukuna, amman dai zan sani soon Gaskiya da zan baka shawara ka dauka, zan ce karka bari wannan ta wuce ka, domin ta hada komai da duk wani namiji zai gani ya ji yana sonta, sai idan namijin nan wani kala ne mai neman wani abun dabam a jikin mace ba wannan ba, kuma zaku yi matukar dacewa da juna, yayanku za su yi kyau Yayi murmushi ya mike tsaye still yana kallon Waira kamar zai cinyeta. Waira na barki a nan naje na dawo? Ta fisge kanta ta mike tsaye da sauri tana girgiza masa kai alamar aa. Okay saka ribbon dinki mu tafi yanzu Ta dauki ribbon din ta saka sai gashin ya hade guri. Ba zaka barta har ka dawo anjima ba? Ba nan zan kwana ba yau Amman ai dare yayi already Yeah gida zamu tafi Idan kun ci abinci ko? Mummy ta tari numfashinsa tana aje kulolin abinci dinning. Bata cin irin abun da muke ci, tea kawai take sha sai cake ko biscuits Waira ta daga masa kai tana murnushin jindadin be manta abun da ta fada masa tana ci ba. Akwai cake ai, zan dumama mata Mummy ta fada ita ma tana yi ma Waira kallon budurwar Ameer ne dan haka so take ta kyautata mata saboda shi. Fiyya ta ware hannayenta tana fadin. Mummy ina da cake dazun da Ya Ya aje ni gurin birthday Ikram ta raba mana cake da zamu dawo gida Toh dauko mata ta ci bari na hada mata tea, zo nan ki zauna yata Mummy ta mika mata hannu, sai ta kalli Ameer har sai da yayi mata umarni da ta tafi sannan ta isa gurin Mummy, Mummy taja mata kujera ta zauna ta zauna. To kai Malam ka zo ka zauna, zata fi sakewa da jindadi Ba musu Ameer ya iso gurin ya ja kujera ya zauna. Mummy ba abun da kike tunani ba ne, not yet Ni ka ji na ce wani abu? Ko kuma ka shiga zuciyata ka ga ina wani tunanin ne? Mummy ta fada da murmushi a fuskarta sannan ta juya ta shiga Kitchen. Ameer ya dauki plate ya zuba abinci ya saka spoon, ya dauki cup ta zuba lemu ya zuba ruwa. Ya fara cin abinci kenan Mummy ta fito da ruwan zafi a cup ta aje a gaban Waira. Teema tashi ki dauko mata kayan tea ta hada da kanta ban san wane kalar tea take so ba kar na mata ba daidai ba Fiyyata nufo gurin da zimmar zama Mummy ta yi mata alama da aa da ido, sai kawai ta zarce kitchen ta dauko plate ta zo dinning din ta zuba abincinta ta nufi hanyar dakin baki dake kasan benen, Teema ma tana gama jera mata kayan tea ta shige ita da Mummy aka bar Ameer daga shi sai Waira. Da kansa ya mike tsaye ya fara hada mata tea yana tambayarta me da me zai zuba, sai ta nuna masa idan ta shimshina ta ji kamshi be yi ba sai ta ce ya kara. Ba a shinshina abinci ba kyau Saboda me? Saboda zaki sakawa kanki cuta ne kawai, abun da za'a ci ba a shinshinawa, kuma ba a hurawa musulumci ya hana Me yasa ake hana ku abubuwa da yawa? Haka Ummi take cewa ba a cin abinci da hagu Yes duk wani abun da zai cutar da mutum addinin mu yana hana mu aikata shi, idan kuma kika ji ance ka aikata to a cikin aikatawar akwai lada da karin kariya ko lafiya da kuma natsuwa Minene lada kuma Yayi murmushi ya koma mazauninsa ya zauna ya fara cin abincin. Lada wani abu ne da ba a gani a ido, amman ana iya fadarsa kuma wani abun kana ganin ribarsa tun a duniya, bari na baki misali da karatun da kike yi, idan kuka yi assignment ko test ba ana baku maki ba? Ta daga kai. Kina ganin makin? Ta girgiza kai. Amman da makin ake auna abun