Sashe 39
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
yana kallonta be san hawaye na sauko masa ba har sai da ta saka hannu ta goge masa, sai ya rumgumeta yana jin kamar ba zai saketa ba, she has to be strong saboda ita uwa ce, ko dan mijinta da yayanta, hakan ya saka ta hana idonta zubar da hawaye ko daya. Baka min alkawari ba, babu wanda zai ji? Ummin na miki alkawari babu wanda zai ji Ta yi murmushi sannan ta nufi kofar fita daga dakin dake kusa da kofar bathroom din, ta bude ta fito a hankali take takawa har ta sauko kasa, yadda ta samu yarta Nimra zaune a saman kujera kanta a kasa ta kasa sake jiki da mahaifinta sai ta bata tausayi, kusa da ita ta zauna ta dafa Nimra ta kasa dagowa saboda idonta na cike da kwalla. Zaman Ummi da kamar minti daya Maleek ya shigo falon ya rike kofar falon Police din dake dauke da Waira ya shigo da ita zai ajeta kasa Ummi ta yi saurin cewa ya dorata akan kujera, bachi take amman tufafinta na rumgume a hannunta da kuma yar takardar da Dr Shuraim ya bata, dayan da baya ciwo dayan kuma an nade shi. Kallo daya Maleek yayi mata ya dauke kai be sake kallon inda aka aje ta ba, ta tsaya jikin kofa domin baya jin shigowa cikin falon ma. A kai su BQ za a kawo musu abinci yanzu sannan mu yi magana Cewar Abiey yana bawa Maleek umarni cewar akai police din da suka mata rakiyar a BQ, sai da yayi musu bayanin da Dr Shuraim yayi musu akan ciwonta da yanayinda ta kuma kalar abincin da take ci ya ba shi takardar magani da file dinta na asibiti sannan ya fice. Ummi ta taso ta karasa inda aka kwantar da ita a dayan set din na kujera tana kallonta kaminnta kai hannu ta taba ba, tausayin yarinyar ya kamata ga ta dai a fuska y matashiyar yarinyar ce ga kyau ga fari tana bachin a tsorace domin ta takure jikinta da yadda mai hankali zai iya fahimtar bata natsu da halin da take ciki ba, ta kai hannu ta taba zoben da yake wuyanta ta fara kokarin zare takardar hannunta sai ta Waira ta kara rikewa hakan ya saka Ummi bata takura ba cewar sai ta ga ko miye a cikin takardar ba. Asibiti za a kaita? Ummi ta juyo ta tambaya tana kallon mijinta. Sai ta farka tukuna, yanzu dai a ina za'a aje ta? Akwai extra daki dake tsakanin Maleek da Namra, a nan ya kamata a ajeta ko kuma dakin su Nimra Aa daga zuwan yarinya ba san wace iri ba ce sai a hade ta da yayana? To zan iya kaita dakina saboda ba zai yiyu a aje ta BQ ba duba da yanayinta da kuma ciwonta, ya kamata ace ta samu kulawa kuma ta haka ne zata sake jiki da mu Ban yarda da kwanta dakin yayana ba zan yarda ta kwanta dakinki? You're more important to me Juyowa ta yi ta kalleshi sai ta yi murmushi. Yau kuma? Kullum ma, ke kika jamyo duk abun da nake furtawa ko yake faruwa ai, kamin na ga yayana wa na fara gani ba ke ba? Da murmushi yayi furucin kamar yadda ita ma murmushin yake shimfide a fuskarta. Duk abun da ake Mahmood na tsaye jikin Stairs ya kasa karasa saukowa kuma shi be hau sama ba, idonsa na kan mahaifinyarsa duk wani motsi nata yana idonsa. Mahmood zo ka shiga da ita dakin dake kusa da na Maleek Sai a lokacin ya sauko ya saka hannu ya dauke ta cak ya haura da ita sama. Abiey ya mike tsaye yana fadin. Ki saka mai aikinki ta kai musu abinci, CP yace su zo nan kai tsaye ba sai sun shiga office dinsa ba, nima kuma yunwa nake ji Yanzu zan saka ta kai musu, daman tun dazun muka gama shirya komai, ni kuma i will serving my King Girgiza kai yayi ya fice yana dariya, sun saba irin wannan wasan amman faruwa abubuwa ya saka sun rufe babin wadandasu abubuwa da dama. Sai da ya fice sannan Nimra ta dago ta kalli Ummi. Har yanzu Abiey fushi yake da ni Zai sauko yata, dole zai daina fushi da yarsa, ki bashi lokaci Abieynku yana daukar zafi akan abubuwa amman yana da kyakkyawar zuciyar mantawa kuma ya yafe, sai dai ba a nan take ba Ummi data karaso kusa da ita ta kai hannu ta taba ta. Yar autar mata, ta so ki fadawa Hanne ta kai baki abinci da abun sha Ta amsa sannan ta tashi tare da wayarta ta fice daga falon, Ummi kuma ta nufi dinning... Khadeeja Candy Copyright 2023 *W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660* After ya nuna musu BQ sai ya samu guri a cikin set din cushion din da aka jera a Balcony ya zauna, yana tsala wayarsa. Har Hanne ta gama ziyar kaiwa bakin abincin da abun sha Maleek ba dago ya kalli gurin ba, Mahmood ne ya fito daga falon yana kallon harabar gidan zuciyarsa cike da tunani kala kala kamin ya kalli gurin da dan'uwansa yake zaune ya nufi gurin. Ajiyar zuciya ya sauke hakannya sakan Maleek dubansa domin ba kasafai Mahmood yake barin wani abun ya dame shi, kusan shi da Namra a gidan babu wanda zai ce ga damuwarsu, Namra saboda bata sake jiki da kowa ciki har da Ummi da yar'uwarta Nimra, komai yake cinta sai dai ta barshi a cikinta, shi kuma baya barin damuwa ta kusance shi ma balle har ya damu da ita, idan ma akwai damuwar kenan, babu abun da suka nema suka rasa a duniyar nan hakan ya saka damuwa nesanta inda suke. Are you okay? I hope so Ya amsa yana kallon harabar gidan, Maleek ya cigaba da danna wayarsa. Tunani nake yadda rayuwa zata zama idan babu Ummi Mahmood ya fada ba tare da ya kalli inda Maleek yake zaune ba. Cak Maleek ya tsayar da taba wayar ya dago kalli Mahmood. Baka da hankali? How could you say that? Kasan abun da ake nufi da babu Mahmood? Rasa ta fa kenan mutuwa, ta ya zaka fadin irin wannan maganar? Mahmoud yayi murmushi yana kallon Maleek, da ya mike tsaye rai a bace. Wannan ranar ba zata zo ba Mahmood idan kuma ta zo to ba zata same ni da rayuwa ba, ban taba mafarkin rana zata zo da zan saka kafata a cikin gidan nan ace Ummi bata nan ba, ban san me ya zo kanka ba ya kamata ka yake shi ka nemi tsarin shaidan daga wannan mummunan tunani naka i hate nonsense Ta zazzaga masa magana sannan ya saka kafarsa sai fice daga gurin sai kuma ya juyo ya kalleshi. Ko wani abu kanji Mahmood? No ban ji wani abu ba, kawai zuwan yarinyar nan ne ya ba ni tausayi ta rabu da iyayenta, ya saka ni tunanin mu idan muka rasa Ummi ya zamu ji irin yadda muka saba da ita? Ku da kuka saba da ita kenan, ya kake tunanin ni da ka kasa kebewa da ita ko da tsawon awa daya ne? Balle har na raba jikinta na rumgume ta a matsayin uwata? Baka tunanin ina jin zafin haka Mahmood? Mi yasa zaka min irin wannan maganar? Why? Ya karshe maganar muryarsa na karkarwa irin na wanda rauni da bakinciki ya dade a zuciyarsa. Bana nufin bata maka rai... Fuuu ya fice daga gurin be tsaya sauraren abun da Mahmood zai fada ba, baya jin komawa ya cikin gidan hakan ya saka shi nufar Katon Garden din dake gidan, Garden da aka kawata da itatuwa da fulawoyi ta ko'ina ta bangare daya kuma an yi Swimming Pool, an jera kujeru a kusa da gurin, ta dayan gefen dama kuma kebantattun tsuntsaye ne da aka yi musu muhalli na dabam, sai barewar dake ta kiwonta a gurin wani decoration na busashen itace. A hankali yake takawa har ya isa gurin da tsuntsayen suke ya bude yar wayar da aka kewasu da ita ya shiga cikin garden din, guri ya samu a gurin kujerun nan da ake na siminti ya zauna yana kallon yadda wasu suke tashi wasu na sauka. Wayarsa dake hannunsa ya bude Gallary ya shiga can wani gurin ajiyar sirrin ya kamo hoton mahaifiyarsa inda take zaune tare da Abiey aka yi musu hoto Tan murmushi har koranta sun bayyana. Yatsansa yakai ya shafa saitin inda take a jikin hoto yana jin wani launi marar dadi na masa yawo a zuciya. Shi ne kadai abun da yake iya, ya kalli hotonta ko ya shafa amman a fili ba zai iya zama yayi shawara ko hira da ita ba, ba zai iya kai hannu ya taba taba jikinta a matsayinta na mahaifinyarsa ba, ba zai iya kebewa daga ita sai shi na tsawon awa daya ba, tun da yayi wayo ya mallaki hankalin kansa be san wata rana da haka ta taba faruwa a tsakaninsu ba, sai dai duk da haka Ummi bata taba juya masa baya ba, bata taba jin ta tsana shi ba, tana kokarin ganin ta ja shi a jikin sai ta ga hakan ya gagara sannan ya saka masa ido ta daina kokarin kebewa da shi a cilas ko taba shi, sai ma taimaka masa da take na yadda zai rayu ba tare da yan'uwansa sun shiga rayuwarsa sun bata masa rai kamar yadda baya bukata ba. Shi dai ya san ba tsanar mahaifiyarsa yayi ba, domin bata yi masa abun da zai saka ya tsane ta ba, idan ma ta yi masa dole ya so ta saboda ita din uwa ce, balle kuma bata yi ba, sai dai ya tsabarsa da mata ne ya saka ita din yake kaurace mata saboda ita ma tana daya daga cikin jinsin matan. To miyasa ya tsani matan? Why? Shi kasan ba zai iya fada ba, be yi soyayya ba balle yace yaudararsa akai yi, be zauna da matar uba ba balle yace ta cucheshi. Sai da aka kira Sallah magariba sannan fito daga gurin, a harabar gidan ya hadu da Ummi ta nufo Garden tana kallonsa. Mahmood yace min