Sashe 131
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
Waira, kai da ita ina tunanin duk a karkashin ikona kuke, ya kamata ace ka fada min kamin ka aiwatar da komai, ko kuma an fada maka Daddynka ne ya fini son lada ko kuma ni ka raina capacity na ne? Ameer ya gagara cewa komai sai kallon rashin fahimta yake yi ma Abiey. Ka fada masa zan aiwatar da komai, ba sai yayi ba, yanzu ma muna tattaunawa ne akan maganar tafiyarta Umminka ta fada min cewar Waira tana son ta tafi, ni kuma na goyi bayan haka saboda na fara process din sanin danginta saboda hakan abu ne mai kyau ko dan sanin macen da za a gina iyali da ita, amman ina ganin ba zan barta ta tafi ita kadai ba, sai na sanar da police an ba mu police biyu ko uku, kuma a samu amincewar hukuma sannan kuma ku tafi tare da ita zai fi Maleek ya soke kai kasa gabansa sai bugawa yake da karfi. Ummi kuma tana kallon Abiey da wani irin burgewa ganin yana kokarin aiwatar da abun da bata tsammata ba a gurin Ameer. With confused Ameer ya dan ware hannunsa ya ce. Maybe ko zata tafi tare da Maleek saboda ta fi sakewa da shi for now ni ina da abubuwan yi da yawa Amman kai zaka fi sanin hanya ai, kuma kai ka fi cewa ku tafi saboda kai kasan inda ka daukota Cewar Abiey yana nuna shi. Yeah amman Maleek zai fi Abiey ya daga kafadunsa Shikenan ba zan takura ka ba, duk yadda ka so haka za'ayi, shiga ka taso ta sai ku yi breakfast din a tare ita ma bata ci abinci ba No... Zan yi... Ameer ya so ya musa, sai dai ganin Abiey ya girgiza masa kai alamar aa ya saka dole ya fasa furta abun da zai fada ya nufi upstairs mamaki fal a zuciyarsa, Namra ma mamaki take, balle kuma Maleek da Mahmood da suke ganin kamar Abiey dinsu aka dauke aka kawo wani. Ummi kam jindadi ya hana ta cewa komai. A hankali ya tura kofar dakin Waira ya shiga tsoron kar tace ya mata ba daidai ba ya saka shi tsayawa bakin kofar dakin yana kallon yadda take shafa baby rabbit dinta da hannunta. Waira zan iya shigowa? Ta juyo ta kalleshi tare da daga masa kai, sai ya maida kofar a hankali ya rufe ya karasa inda take zaune a kasa, ya zauna ya hade kafafuwansa yana kallonta. Good morning Ya fada yana yafawa fuskarsa murmushi. Tunanin ita ya kamata ta fara gaishe shi ya hana ta amsawa, sai ma mika masa guiwarta da ta yi. Good Morning How are you doing today? Beautiful Angel Ta sauke kanta kasa ganin irin kallon da yake mata kirin yake jira ya fada cikin idonta ya narke kamar ruwa. Abiey ya ce ki fito muje falo mu karya, kuma na yi magana da Daddy na akan musuluntar da zaki yi, yace zai yi magana da Imam dinsu, but then sai kuma Abiey a yanzu yake min maganar cewar zai yi komai ba sai Daddy ya shigo ba, i don't know ko haka din yayi miki? Bata ce komai ba, kanta na kasa har lokacin, shi kam a yanzu dai baya gajiya da kallon duk wani abu da ya shafe ta balle kuma ita din kanta. Ko kin fi son ki karya a nan? Bari na wanke baki Ta tashi ta shiga bandaki, sai ya bita da kallo kamin ya dauki rabbit din ya fara shafawa yana laka shi da jikinsa jin yake kamar Waira yake tabawa saboda ta saka hannunta ta taba gurin. Tana fitowa daga bandakin ya maida idonsa a inda suka fi yi masa dadin kallo wato fuskar Waira, shigar da ta yi bandakin ta wanke baki da fuska sai ya ga kamar ta kara kyau da kwarji, sanyin ruwan dake fuskarta sai ya ji kamar ta tafi ya lashe su. Gaban madubi ta nufa ta dauki ribbon ta daure gashin kanta sannan ta nufi kofa kamin ta isa har ya riga ta bude mata kofar kamar wata sarauniya. Tana fara saukowa stairs din sai ta tsaya ta juyo ta kalleshi. Ba zan iya cin abinci a can ba kowa yana nan Wani iri take ji a yanzu, daman can tana ganin kanwarta da ta Abiey bata jika ba, a yanzu kuma tana ganin Ummi kamar tana tsoronta ne ko kuma ta tsaneta saboda abubuwan da suke faruwa. Na kawo miki daki? Kamin ta bawa Ameer amsawa suka hango Abiey na magana ba dan ya ji abun da suke fada ba sai dan ya fahimci damuwar Waira. Sauko mu tashi zamu yi mun gama ai, idan ganinmu ne zai hana ku ci a nan Ta kalli Ameer sai da ya karfafa mata guiwa ta hanyar daga mata kai, sannan ta sauka a hankali yana gefenta har suka isa dinning, kujera ce first abun da ya fara ja mata a zatonsa zata zauna a inda yaja, sai ya ga ta nufi kujerar da babu kowa kuma bata kusa da kowa ta zauna, tana sanda kai kasa alamar bata son kallon mutane. Ameer ya zauna a kujerar da ya ja, Namra ce ta fara mikewa tsaye sai Abiey ya kalleta ya ce. Baki gaishe da Yayanki ba? Ta kalli Abiey with shock, sai dai ba zata iya musawa mahaifinta ba, ko kuwa daga ita sai shi ne balle kuma a gaban yan'uwanta, saboda haka ta kalli Ameer ta ce. Good Morning Ya amsa mata kai, mamakin na gaf da kashe shi ganin Abiey ya dauko wata hanya da be san me yake nufi da haka ba. Kuma duk sai na fada za ku yi magana da shi? Wannan ya zama na karshe da zai shigo ba ku masa magana ba, musamman da safe irin nan, kai ma kuma karka jira sai sun maka zaka iya fara musu magana Ameer ya amsa da kai yana kallon Ummi dake kallonaa with so much joy. Good Morning Maleek da Mahmood suka gada baki gurin furtawa bayan sun gama kallon junansu da mamaki, su ma dai da kai ya amsa musu. Abiey ya mike tsaye da murmushi a fuskarsa ya ce. Good, idan ka gama ina son magana da kai Son Maleek ya mike tsaye daman tun shigowar Ameer da Waira a dinning din yake jin kamar yana kan aya. Abiey ya juyo ya kalleshi I guess you're not the only Son here, i'm taking to Ameer, shi nake nufin idan ya gama ya same ni a ciki akwai maganar da zan yi da shi not you O.... O.... Okay... Maleek ya fada har sau biyu a ukun ne ya samu hada kalmomin, hakan kuma be saka shi fasa barin dinning din ba, suka fice tare da Mahmood suna kuskus, Namra kuma ta nufi stairs. Sai da Abiey ya fice daga sashen sannan Ameer ya kalli Ummi da mamaki ya ce. Me yasa Abiey yake min haka this time? Is he up to something? Ummi yaja kujerarta baya ta mike tsaye ta nufi inda yake zaune ta shafa kansa ta sumbanci saman kanta ta kwanto da shi jikinta. No ko kadan, addu'ar da na dade ina yi ce Allah ya karba min a yanzu, farinciki da na dade ina son samu a tare da duka yayana ne Allah ya kawo min cikin sauki Sannan ta kalli Waira ta ce. Waira ni ban tsane ki ba, karki kalleni a baibai, kawai ina kokarin ganin na shirya tsakanin yayana ne Anjima nake son na tafi Waira ta fada, Ummi bata ce mata komai ba ta saki Ameer ta nufi hanyar dakinta. Ameer ya mike tsaye yayi serving dinta sannan ya zuba na kasa. Abiey yace be yarda ki tafi ke kadai ba, sai dai a rakaki kuma sai an sanar da jami'an tsaro ina ganin ya kamata ki hakuri har zuwa gobe saboda ayi komai cikin kwanciyar hankali, kuma Maleek da zai raka ki zai samu lokaci ya shirya kamin time din Bana son kowa ya raka ni, a garin ba a karba baki, kuma za a iya cutar da wasu saboda ni, ko kuma ma laifina ya yafe su No ba zan iya bari ki tafi ke kadai ba Waira, ko da kuwa kashe wanda zaku tafi tare za'ayi, i know baki sona a kusa da ke, shiyasa da Abiey ya ce na rakaki na zabi Maleek ya rakaki, saboda kin fi sonsa kuma hankalinki zai fi kwanciya idan yana tare da ke sama da ni Kamar tace masa kai ma ba tsanarka na yi ba, kawai da zancen aurena da kai ne bane so, sai kuma ta samu kanta da jin nauyin kasa furta haka. After sun gama breakfast din Ameer ya nufi dakin mahaifiyarsa wato Ummi, first tambayar da yayi mata is. Kin san abun da yasa Abiey yake son magana da ni? Sai ta girgiza masa kai. Ban sani ba, be fada min zai yi wata magana da kai ba ban san komai akan abun da zai tambayeka ba Ya juya ya fice daga dakin yana tunanin kondai Abiey zai roki wata alfarma a gurinsa ne akan Waira shiyasa yake masa magana kamar daman can babu wata kiyaya ko tsanar juna a tsakaninsu. Be san bangaren Abiey ba, dan haka yayi ta bude dakunan da suke corridor kamin ya isa babban falon dake cike da sanyin ac. Abiey yana hakimce saman kujera sanye da jallabiyar da ya saka tun safe sai wayar dake hannunsa yana duba yanar gizo. Bismillah Ameer shigo ciki Ameer ya cire talkamin kafarsa for the first time saboda zai shiga gurin wani. Ya isa cikin falon sai ya zauna a kujerar dake nesa da wanda Abiey yake zaune, zuciyarsa na raya masa abubuwa kala kala akan kiran da Abiey yayi masa, ko da yake hausawa sun ce karka ji tsoron kira ka ji tsoron laifin da ka aikata. Shiru ne yayi ta wanzuwa a cikin falon na tsawon lokaci kamin Abiey ya dago ya kalleshi ya ce. Da gaske baka ra'ayin raka Waira garinsu? Yayi jimmmm kamar mai nazari sannan ya daga kai. Yeah akwai abubuwa da zan yi masu muhimmanci a nan, kuma zata fi jindadin tafiya da Maleek din dai Okay, na yi magana da Imam na sanar