Sashe 129
Wani Gari Khadeejah Candy Complete Hausa Novel · about 8 min read
min abubuwa da yawa da ban tambaya ba, ka sanar da abubuwan da ban sani ba, na fahimci addinin saboda kai kuma na ji ina kaunarsa duk a ta dalilinka, ina son na musulunta, musulunci kadai abun da zan tafi da shi, da zan zo ban zo da komai ba, dan haka ba zan dauki komai ba, zan tafi daga ni sai abun da na koya... Ya ake shiga musuluncin ina son na shiga, na yi rayuwa mai tsafta kamar ku, ka karu da abun da ka koyar, kuma ka cika burinka kamar yadda ka roko... Ya hade yawu da karfi, farinciki da kishiyarsa suka ziyarce a lokaci daya. Daga kwance da Ummi take ta dago ta kalli Abiey daya shigo dakin sanye da tufafin bachi, abun ka da mace mai kula da miji sai ta yaye zanen da ta rufa da shi ta tashi zaune tana kallonsa har ya iso inda take ya zauna bakin gadon yana kallonta. Madam yau kuma a nan zaki kwana? Ta sauke kai kasa ba tare da tace masa komai ba. Tun da ciwon nan ya bayyana a garemu, sai duk kika canja, abubuwa da yawa wadanda ba halayyarki ba kika ara kika yafa, wadanda suke naki kuma kika zubar, lokacin da ya kamata ace kina cikin farinciki da jindadi, sai kika mayarda da su na bakinciki da damuwa, alhalin ni yanzu ban ga wani abun damuwa a tare da ke ba Haka dai kake gani, amman har yanzu ban gama cika burina ba, balle na zaba zama cikin farinciki, ko kuma damuwa ta zabi rabuwa da ni Toh me ya rage? Ina ce yanzu kina tare da Ameer, iyayen Deen sun san komai, bayan shi akwai wani abun da kika aikata kuma da kike jiran neman yafiyar wani? Ranka ya dade yanzu ba yafiyar wani nake nema ba, hadin kan a nake da bukata, yadda za tafi na bar Ameer yana rashin jituwa da yan'uwansa ne damuwata, yadda kake nuna masa tsana da kiyayya ne matsala ta, ni na rike naka yayan da zuciya daya, na kaunace na nuna musu so, amman kai ka kasa nunawa Ameer nawa kwaya daya tal, har ya gama fahimtar baka sonshi, gashi duk wasu kalamai da zan yi amfani da su na sauya tunaninsa sun kare, kuzarina ya tafi, ina tausayin rayuwar Ameer idan bana raye Abiey ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta. Na taba furta cewar bana son Ameer? Kamin yanzu ban fada miki ki yi iya yadda zaki yi Ameer ya zauna a hannunki ba, ni kuma zan goya miki baya, amman kika zabi abun da kika zaba? Zaman a gidan nan na taba hana shi shiga wani bangare na gidan ko kuma na taba cewa ya fice min daga gida? Zahra ki rika sara kina duba bakin gatari, kar son Ameer ya rufe miki ki kasa ganin gaskiya a inda take marararta Idan har son wani zai rufe min ido na kasa ganin komai, to sonka ne farkon abun da ya fara cutar da ni, kuma ya cutar da Ameer, a duk lokacin da zan yi maganar Ameer ko na nemi ganinsa ina ganin kiyayyar haka a idonka, ka sha canja mu'alama da ni saboda kawai na nuna ina son ganin ana, ka kasa daina kiyayya da wanda ya manta da ya taba wanzuwa a duniya, ka kasa nuna min soyayyar da kake takamar kana yi min tun kurciya har tsufa, saboda ka kasa tirsasa zuciyarka ka fi karfinta ta cusa mata son ana jinina Abiey ya sauke ajiyar zuciya. Laifina a yanzu saboda kawai na ce Maleek yana son Waira? Sai Ummi ta dube shi duba na tsanaki. Ka bata tambayar lafiyarsa? Ka taba cewa Ina Ameer? Me Ameer yake so miye baya so? Me dace mu yi akan Ameer? Yanzu dai ki bar abun da ya wuce ya wuce, tashi muje mu kwanta, kuma likita ya min waya satin nan za ki kwanta asibiti for some months or weeks ya danganta da yadda jikinki ya karbi maganin, idan kin samu lafiya kamin lokacin da ake tsammanin zamu iya dawowa gida ma Lokacin ziyartar asibiti ya wuce kenan, sai dai kwana Hakan kuma ba yana nufin ba zaki warke ba, ko kuma ki dawo gida, kawai mu yi addu'a saukin ya zo a kusa babu cutar da bata da magani ai Ya sauko da kafafuwanta kasa ya rikata sai ta mike tsaye ya kwanta jikinta, shi kuma ya daga kansa sama saboda ya hana hawayensa zubowa, yana matukar tausayin matarsa da kaunarta fiye da tunanin duk wani mai tunanina. Da taimakonsa ta fito dakin ta sauko kasa yana rike da ita har suka isa bangarensa, ya kwantar da abar kaunarsa akan gadonsa ya lullube ta sannan ya shiga bandaki yayi alwala ya gabatar da shafa'i da wutiri yayi ma matarsa da yayansa addu'a sannan ya kwanta bayanta ya rumgume abarsa. Washe gari Abiey be bari Ummi ta fito daga bangarensa ba, shi ya shiga bangarenta ya tasa yaransa a gaba daga Maleek har Namra da Mahmood Waira ce kawai aka bari a daki, su kuma suka dunguma zuwa kitchen ko Hanne be yarda ta saka masa hannu a cikin a breakfast din da suke shiryawa ba, kawai so yake yau ya burge matarsa, rabon da ya shiga kitchen irin haka tare da yaransa ko Ummi tun yana da sauran kurciya, kamin ayukan da iyali su fara girma su sauya masa rayuwa. Hadin girkin ya saka kowanensu nishadi, Namra ta saka wayarta tana musu hotuna da video, kamin ta saka su hawaye tunawa da ta yi da yar'uwarta, tana fadar ina ma ace Nimra tana raye, kusan kowa sai da yayi hawaye har Abiey. Suna fara jera abinci a dinning Ummi ta iso bangaren, bata a cikin yanayi mai dadi amman hakan ba hana ta murmushi da farinciki ganin iyalanta a haka ba. Abiey da kansa ya ja mata kujera ta zauna. Yana zolayarta wai idan bata bashi rate na 100 ba za su samu matsala. Abiey to ai bakai kadai ka yi girkin ba Then n OK da yayana na yi Ya amsa yana cire gilashin idonsa. Nimra ta koma gefen Ummi taja kujera ta zauna. Toh ni ina bangaren Ummi, saboda na saka hannu girkin yayi dadi Ummi ta kalleta tana murmushi. Aa daman ni mijina ya iya abinci, tun kamin a haife ku yake min girki Sai duk suka sa dariya jin Ummi ta shigarwa mijinta kai tsaye. AMEER POV. Hakan ma abun farinciki ne a gurina, zan gabatar da maganar nan a gurin Daddy sai mu yi abun da ya kamata Ya juya ya bude motarsa ya shiga ya barta a gurin tsaye tana bin motarsa da kallo har ya fice. Har ya isa gida da hannu daya yake driving dayan hannunsa na dafe a kirjinsa, gaba daya ya rasa abun da ke masa dadi ga zuciyarsa sai zafi take. Ya faka a daidai lokacin da motar Daddy ta faka harabar gidan, shi ya bude ya fito Daddy kuma direba ya bude masa ya fito, tsabar hankalinsa da tunaninaa ba a jikinsa suke ba sam be lura da Daddy ba sai kokarin shigewa ciki yake har sai Daddy ya kira sunansa. Ameer Sai ya juyo kamar a rude ya kalli saitin inda ake kiran sunan nasa. Ganin Daddy ya saka shi hanzarin isa gurin motar, wani abun da be saba ba sai ya bawa Daddy hannu su gaisa, kamar wanda ya tarardar wani abun kunyarsa ba Daddy ba. Kallon tsanaki Daddy yayi masa yana karantar damuwar dake tare da shi, hakan kuma be hana shi mika masa hannu su gaisa ba. Ameer me yake damunka? Yau kuma ni kake bawa hannu mu gaisa? Ameer ya kalli Daddy sai kuma ya sauke kansa kasa, be san ta inda zai fara fadawa Daddy damuwarsa ba bayan ya gujewa bukatarsa kuma ya kara masa da yin karya. Daddy ya kai hannu ya dafa shi. Ameer ana ban taba ganinka a irin wannan yanayin ba, fada min mw ya faru? Wani abu ya same ka ne ko Ummi? Ko wani ya fada maka wata magana marar dadi ne? Waya jefaka a wannan yanayin? Tell ko miye zan magance maka shi Ameer ya hade yawu ya girgiza kai ya soma magana kamar zai yi kuka. Ba zaka iya ba Daddy, wani abu ne da kudi baya siya, kyau ilmin martaba ko isa basa siya, kima mutumci da daraja basa siya Daga saman kafardarsa Daddy ya gangaro zuwa kasa ya rika hannunsa. Zo mu shiga ciki Ameer ya jera tare da Daddy suka shiga cikin gidan, sai da suka isa a inda za su zauna sannan Daddy ya sake hannun Ameer ya zauna a kujerar da ya saba zama. Ina iya fahimtar halin da kake ciki Ameer, na san damuwarka n a san farincikinka, sai dai wannan karon ka shiga a wata kalar damuwa da ta wuce misali, a yanayin yadda ka jera min abubuwan da na za su iya siyen damuwarka su kawo maka farinciki ba sai na fahimci so ne am I right? Ya daga kai ba tare da ya kalli Daddy ba. Ya sani yi maka karya Daddy, ya maida ni mahaukaci, ya jefa ni a halin da ban taba mafarkin shiga ba, sanin cewar kai ba mahaifina ba ne, sanin abun da Ummi ta yi, gorin da za ayi min da duk wani abun da zan rasa ko na ji, ba kai yadda nake ji a yanzu da na rasa Waira ba How comes ka rasata? Wane irin sake ka yi har ka rasata? Garin ya? Bata sona Daddy, ta fada min kuma na ga haka a idonta, na karanta a kalamanta wani take so dabam ba ni ba Daddy ya tashi daga inda yake zaune ya dawo kusa da Ameer ya zauna ya dafa kafadarsa. Ameer kana da kyau da asali da kudi da muruba da kwarjini da farin jini da haiba da cikar zati da siffar da ko wace mace zata so ka, ko da kuwa kai baka furta mata ba ita zata so haka, balle kuma ace har ka furta mata ko da kuwa yar zinarice, kasan abun da na dade ina jira arayuwata? Ganin Ranar da zaka zama mai hankali da sanin ya kamata, ranar aurenka Daddy Yarinyar